SANI S.K
Labaran soyayya kuzo mu hada karfi da karfe
mugina soyayya ta gaskiya
dan nishadi
mu dage dan kawar da soyayyar karya
da yaudara
Na lashe kyautar $ 3.00 daga ClipClaps, bude ClipClaps don raba kyaututtuka tare da ni. = # https://www.clipclaps.com/?activity_spin=77518391
19/05/2022
https://www.facebook.com/105610588569892/posts/168388415625442/?app=fbl
Yadda zaka iya gane cewa mutum yana sonka
Kamar yadda zamu iya shadawa a kusan dukkanin halittun da suke faɗin duniyar nan, zamu ga cewa mazaje sune suke fara ko yunƙurin neman mata domin kuwa ba kasafai ake samun mata suna neman maza ba. Idan mace tana son ka baza ta gaya maka da maki ba, amma zata gaya maka da yanayin motsin jikin ta. Jikin mutum ya kasance yana fayyace abun dake cikin ran shi ta yanayin yadda mutum yake matsawa, tsayuwa da kuma yanayin fuskar mutum koda kuwa mutum bai yi magana ba. Galibi mata suna nuna wasu alamu ne dake nuna cewa suna son namiji. Waɗannan alamun suna bayyana sune ba tare da sun ankara ba, idan mace tana son ka bazai yuwu ta iya ɓoyewa ba. Hakan kenan yana nufin dole namiji ya zamo mai ƙwarin gwiwar neman mace da soyayya, to kenan mazaje masu kunya baza su iya samun budurwa ba kenan? Zamu bada amsar wannan tambayar a wasu shafuka na gaba.
Alamomin da suke nuna cewa mace tana son namiji
Zata riƙa neman taga cewa tayi maka magana, misali ta hanyar yi maka wasu tambayoyi akan abubuwan data sani.
Zata riƙa yawan yi maka murmushi akan abubuwan da yin murmushi akan su bai da wani muhinmanci.
Zata riƙa yawan taɓa gashin kai a sa'ilin da take yin magana dakai.
Zata riƙa yawan gyaran jikin ta a lokacin da take tare da kai.
Zaka riƙa yawan haɗuwa da ita a gurare mabanbanta.
Zaka fahimci cewa bata ruɗewa idan tana magana a gaban wasu mazajen amma kai kuma tana ruɗewa idan tana yin magana da kai. Abun da nake nufi da ruɗewa anan shi ne irin ruɗewa da mutum zai yi misali idan ya shiga ofishin wani babban jami'i k**ar dai manajan wani kamfani idan yaje neman aiki, dalilin da yasa mutum yake wannan ruɗewar shine saboda yana ganin wannan mutumin da martaba. To k**ar haka ne itama martabar ka da take gani shine zai sata ruɗewa idan tana gaban ka.
Ƙwayoyin idanuwan ta zasu wage a lokacin data haɗu da kai (amma ka sani wagewan ƙwayoyin idanuwa alama ce kuma na jin tsoro ko fusata).
Kuma zaka samu tana juyawa ta fuskance ka. Yanayin yadda mace take fuskantar mutum yana nuna irin yadda take son mutum. Macen da take son namiji a koda yaushe zata riƙa fuskantar shi idan suna guri.
Sannan idan mace tana son ka zata riƙa kwaikwayon abubuwan da kake aikatawa ba tare da ta ankara ba.
Reaction Formation
A Psychology Reaction formation wani yunƙuri ne da zuciyar mutane take yi domin gujewa gasgata magana ta inda mutum ba tare daya ankare ba zai yi yunƙurin kawar da lamurran da suke tsorata shi ko waɗanda baya so tare da maye gurbin su da wasu lamurran da suke yin inkari dasu. Don haka namijin da kwatsam ya fara wulaƙanta wata mace ko macen da kwatsam ta fara yiwa wani namiji rashin kunya mai yuwuwa son shi ne yake neman shiga zuciyar ta amma kuma bata son hakan ya faru a zahiri bisa tunanin cewa shi ba sa'ar soyayyar ta bane, don haka sai ta ɓuge da yi mashi rashin ɗa'a domin ganin ta tabbatar da bata son shi a ran ta.
Waɗannan sune alamomin dake nuna cewa mace tana son namiji, duk da cewa dai akwai wasu alamomin.
14/03/2022
https://www.facebook.com/105610588569892/posts/153626460434971/?app=fbl
NA MAZA
Ke ce hasken ranar da ke haska min dare na san safiya ta yi a duniyata, ke ce iskar da nake shaka domin na rayu, ke tamkar igiyar ruwa ce a cikin kogin da nake ninkaya, ke ce bugun zuciyata da yake bambance rayuwa da mutuwata. Ina Son Ki.
Son da nake yi miki tamkar madubi ne a cikin zuciyata. Ko da a ce ya fashe, idan kika sanya idanuwanki a kansa za ki tarar da ke a cikinsa. Son ki ya zamo jini a jikina ya bi ta jijiyoyin jikina ya narke a cikin zuciyata. Ina Son Ki Sarauniyata.
Ranar da za a ce ga ki a kusa da ni, a wannan ranar zan ji ni a matsayin cikakken mutum mai sa’ar da babu irin sa, a wannan rana zan yi takun kasaita tamkar na sarkin da ke da daular da babu irin ta a duniya, saboda na mallaki mai kyawun da babu k**ar ta, wadda nake fatan mu rayu tare rayuwa ta har abada. Ina hango mana rayuwa mai tsawo cikin shekaru masu ɗauke da ranaku masu ban mamaki a nan gaba. Ina Son Ki Gimbiyata.
A dukkan lokacin da tinanin kyakkyawar fuskarki ya bujuro a cikin zuciyata, sai na ji zuciyata ta kara narkewa a cikin soyayyarki, na ji na kamu da matsanancin begenki, kewarki mara misaltuwa ta dabaibaye ni ta yadda nake kasa tsaida zuciyata daga tinaninki. Ina Son Ki.
A lokacin da taurari s**a kasance suna haska saman duniya da haskensu, mu kuma mu kasance tare a kasanta muna masu haska cikinta, wannan abu ne da zuciyata tini ta aminta da shi tare da kaguwa wajen ganin mun kasance tare tamkar jini da tsoka, zan so a kullum ke ma k**ar ni burin son ganin faruwar hakan ya kasance a cikin zuciyarki. Ina Son Ki. Fatan Kina Nan Lafiya?
Macen da murmushinta ke haska duhun dare, macen da sautin muryarta ke sanya nutsuwa a zuciyar mai sauraro. Kin samar da farin-ciki a cikin zuciyata, kin zamo mace ɗaya tilo da babu k**ar ta a cikin idanuwana. Ina Son Ki.
Amincin Allah ya tabbata a gare ki, mace ta farko da ganin kyawunta a karon farko ya hana ni bacci a tsawon dare, ya hana ni sukuni a tsawon yini, macen da ta tsaida zuciyata daga tinanin komai sai nata, macen da nake so kuma zan cigaba da so har karshen rayuwata. Ina Son Ki.
Ke ce babbar kyautar da a tarihin rayuwata na taɓa samu wadda ba zan taɓa mantawa da ita ba. Ina son ki. Ina fatan tabbatuwar murmushi a saman fuskarki tare da kasancewarki cikin walwala da farin-ciki a ko da yaushe.
♡
A lokacin da na ga hoton kyakkyawar surarki na kan yi murmushi ko da ina cikin damuwa, na kan faɗa cikin tinanin kyawawan idanuwanki da tattausan murmushinki. Ya kan gusar da hankalina daga sauraren komai da tinanin komai sai naki, ya kuma iza wutar begenki a cikin zuciyata. Ina son ki masoyiyata, abar tinanina.
♡
Ke ce mai kawata baccina a duk cikin dare, a lokacin da k**e bayyana a cikin mafarkina kina mai haske ni da hasken murmushinki mai taushi. Zan so ki kasance a tare da ni a rayuwarmu ta zahiri k**ar haka, na tabbata jama’a zasu koma kirana da Yarima ko Dangata, saboda na mallake ki. Ina son ki.
♡
Son da k**e yi min, shi ne abu mafi girman dukkan wata kyauta da na taɓa samu a rayuwata. Kamar yadda na sha sanar da ke a baya ina son ki ni ma so mara iyaka da lokacin yankewa. Ki kula min da kanki.
Ba na yin nadama ko da na sani da zaɓenki a matsayin masoyiyata, saboda ke ce zaɓin raina kuma ke ce mahaɗin rayuwata, ke ce wadda na jima ina nema. Fatana na rayu tare da ke a matsayin uwar ‘ya’yana, na kuma mutu ina mai fatan sake haɗuwa da ke a gida mafi soyuwa ga kowane mutum wato Aljanna. Ina Son Ki.
Barka da safiya masoyiyata, kyakkyawar macen da babu k**ar ta, mai sanyin muryar da ta zarce sarewa, mai kyawun ido da kyawun kallo, ina fatan kin tashi lafiya kyakkyawar zinariyata.
Son ki ya shiga zuciyata ta yadda ba zan iya wuni ba tare da tinaninki ba. Yadda nake ji a cikin zuciyata a kanki ya sanya ni jin cewa ina son ki ne fiye da yadda kowa yake nuna hakan a kanki. Idan har kika tambaye ni me ya sa, ba zan iya sanar da ke dalili ba. Zan ci gaba da son ki har na tsawan rayuwata, zan kasance a tare da ke ba zan bari ki kuɓuce min ba. Ke tawa ce ni naki ne, fatan zaki amince mu rayu tare rayuwa ta har abada? Ina Son Ki.
Son ki na bayyana kullum a cikin zuciyata, tamkar yadda rana ke futowa a sararin samaniya, ya yaɗu a cikinta ya kawata ta, fiye da yadda taurari ke kawata sararin samaniya a cikin dare. Ina son ki kuma zan cigaba da son ki har zuwa fitar numfashina
13/03/2022
https://www.facebook.com/105610588569892/posts/153501413780809/
Sinadaran Kalaman Soyayya
Assalamu Alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili. A wannan karon in sha Allah za mu tattauna kan sinadaran da suke kara dandano da zakin kalaman soyayya tsakananin masoya. Da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
1.Sarrafa Murya
Wata babbar ka’ida da take kara inganci da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin masoya ita ce, yanayi da sigar da kalaman ke fita su isa kunnen mai sauraren su. Dole sai masoya sun rika sarrafa murya wajen bayyana shaukin kaunarsu ga juna; kowane kalami da irin sigar muryar da tafi dacewa da shi:
• Kalaman nuna so da kauna ana furta su garwaye da shaukin bege, cikin bayyanannun kalmomi, wata sa’in ana iya furta su cikin yanayin wake, ko a siririntar da murya ko a nauyaya ta don ta yi daidai da lokaci da kuma yanayi.
• Kalaman tausayawa, suna bukatar a tausasa murya wajen furta su, a cakuda murya kafin a bayyana jimamin abin da ake tausayawa dominsa.
• Kalaman ban hakuri na bukatar a nauyaya su da muryar da-na-sani, nadama da marairaicewa.
• Kalamana godiya na bukatar a kawata furucinsu da farin ciki da jin dadin abin da ake godewar.
• Kalaman wasa da zaurance kuwa sai a surka muryarsu da jin dadi da nishadi.
• Kalaman sha’awa, ko dai a sa murya ta yi taushi yayin furucinsu, ko a sanyaya ta, ko a siririnta murya, ko a sa murya ta yi kasa-kasa, ko a rika fitar da kalaman cikin rada, ko a rika fitar da su dai-dai cikin yanayi na jan hankali; abin nufi dai, ma’aurata su yi kokari su rika karya murya cikin siga mafi dacewa da lokaci da kuma yanayi. Kalaman sha’awa ba lallai sai sun yi ma’ana ba wata sa’in, ana iya caccakuda wasu kalmomi a fitar da su da wani irin karin muryar sha’awa wadanda zai sa su yi tasiri sosai.
• Kalaman neman alfarma sai a gauraya su da muryar kwantar da kai da marairaicewa.
2. Sarrafa Jiki
Sarrafa yanayin jiki ya dace da kalaman kaunar da ake bayyanarwa, shi ma yana matukar kara fa’ida da tasirin kalaman bayyana soyayya tsakanin masoya. Kowane kalami; kowane karin murya, akwai irin yanayin lauya jikin da ya fi dacewa da shi. Fuska ita ce madubin zuciya, duk abin da mutum ke ciki, za ka iya fahimtar hakan daga yanayin da fuskarsa ta alamtar; don haka sai masoya su rika kiyaye irin sakon da fuskarsu ke bayyanawa lokacin da suke kalaman soyayya.
• Lokacin furta kalaman nuna so da kauna, sai masoya su zanance fuskarsu da launikan kauna, ta hanyar marairaicewa da kallon juna cikin kwayar ido, da sa kwayar idon ta yi narai-narai da shaukin so.
• Wajen bayyanar da sha’awa shi ma sai a marairaitar da fuska cikin hayakin sha’awa, tare da lallauya wasu bangarorin jiki yadda za su fito da ma’anar cikin kalaman da ake furtawa; misali narairaitar da ido cikin ruwan sha’awa, da jujjuya kwayar idon, da sarrafa girar idon, da yin gatsine cikin yanayin shagwaba ko cikin yanayin tsiwa (amma tsiwar wasa), murguda baki, daga gira, yanayin tafiya, yatsina na yatsun hannu ko na jiki duka, yanga, kissa da kisisina da sauran abubuwa mak**antan haka.
• Wajen nuna godiya da jin dadi, dole ma’aurata su barbada garin farin ciki da jin dadi a fuskokinsu.
• Wajen nuna tausayawa, sai ma’aurata su jike fuskarsu da jimami da shaukin tausayi.
Da sauran ire-iren yanayin sarrafa jiki don ya dace da kalami, yanayi da kuma bukata.
3. Hirar Kyautata Soyayya:
Yana da matukar alfanu ga masoya da su sanya wani lokaci a kullum, komai kankantarsa, wanda za su rika yin hirar jin dadi da debe kewa a tsakaninsu, yin haka zai yi matukar kyautata so da kaunar da suke yi wa juna, kuma zai matukar inganta dangantakar da ke tsakaninsu. Duk lokacin da suke irin wannan hira, ya k**ata masoya su kiyaye wadannan muhimman abubuwan:
• Ya kasance ma’aurata sun mayar da hankalinsu ga dari bisa dari ga junansu, watau su saurari junansu da gaba dayan kafofin hankalinsu.
• Kallon ido cikin ido ya zama wajibi gare su lokacin da suke hirar, da kallon fuskar juna da fahimtar sakon da ke zayyane a fuskar wanda zai kara fito da ma’anar hirar da suke yi.
• Sauraran yanayin shaukin da ke cakude cikin kowane kalami a lokacin hirar, na miji ya k**ata ya kiyaye da wannan, domin mata na da wani irin halin yin magana a murgude, watau su fadi magana alhali a cikin zuciyarsu ba hakan suke nufi ba, ta hanyar sauraren shaukin da ya cakudu da kalamin, ko yanayin zane da launin fuska, ko yanayin sarrafa jiki ne kadai zai sa a fahimci maganarsu ba iyakar maganarta ke nan ba.
• Ma’aurata su kasance masu lura da yanayin yaren jikin sunansu lokacin hirar, wannan zai kara kusanci da jin dadin hirar gare su.
• Sannan ma’aurata su lura kada su rika katse junansu yayin irin wannan hirar, duk wanda yake wata magana, komai rashin muhimmancinta a wajen mai sauraren, to ya yi hakuri ya bar shi har sai ya kai aya tukun, domin katse mutum lokacin da yake tsakiyar zance na haifar da jin haushi cikin zuciyar wanda aka katse din. Yana da matukar alfanu kowane daga cikin ma’aurata a ba shi cikakkiyar dama ya fadi dukkan abin da ke ransa, kuma a saurare shi cikakken sauraro.
4. Muhimman Abubuwa
• Yana da matukar muhimmanci sosai masoya su rika yaba wa juna ko da sau daya ne a kullum, kuma yabo na gaskiya ba na riya ba. Sai a lura da wani abu na musamman a yabi wanda ake aure da shi; kuma ya kasance ana dan caccanza abun yabon ba kullum a k**a abu daya a yi ta maimaita yabo a kansa ba.
• Sannan a rika yabon wanda ake aure a gaban wasu daban wadanda za su iya sanar da shi wannan yabon, k**ar a wajen ‘yan uwa.
• Sannan masoya su yi kokari wajen fahimtar ra’ayin junansu, kuma su rika yi wa juna uzuri game da ra’ayoyinsu da kalamansu.
• Haka kuma masoya rika kokarin tauna duk kalamin da zai fito bakinsu, don kauce wa fadar kalamin da zai iya haifar da husuma ko jin zafi a tsakaninsu.
• Sannan ma’aurata su rika zabar kalmomi mafiya dadi; mafiya dacewa da kowane zancen da suke yi.
5. Abubuwan Kiyayewa
• masoya su kiyaye fadar kalmomin kushe ko kasawa ga junansu; domin irin wadannan kalmomi suna saurin gusar da soyayya da haifar jin haushin juna tsakanin ma’aurata.
• Sannan masoya su kiyaye takaita surutu lokacin hira, sannan kada daya ya mamaye hirar ya kasance shi kadai ke zuba, ya ki bayar da dama ga dan uwansa shi ma ya fadi albarkacin bakinsa.
11/03/2022
KALMA
Ko da a ce ba ki furta min kowace irin kalma ba, a dukkan lokacin da na kalli fuskarki mai cike da annuri, na kan iya bayyana abun da ke a cikin zuciyarki. Wannan misali ne na yadda na damu da ke, fiye da yadda na damu da kaina. Ina Son Ki.
NAZARI
Na jima ina nazarin hanyoyin da zan bi wajen bayyana miki adadin yadda soyayyarki take a raina, amma yanzu na samo wata hanya guda, kin kuwa san wacce ce? Ta hanyar ƙara jaddada miki cewa INA SON KI! Ki Kula Min Da Kanki.
DAƊI
Soyayya na da matukar daɗi, ban tashi gane hakan ba sai da na same ki. Ko da a ce babu kowa a duniya, da iya ke kaɗai zan iya ƙare rayuwata. Fatana a ko da yaushe, ki kasance cikin jin yadda nake ji a kan ki. Ki Huta Lafiya.
KULAWA
Ba zan taɓa bari ki kuɓuce min ba, zan kasance cikin son ki tare da baki kulawa a cikin kowane irin yanayi. Ina Son Ki.
TAMBAYA
Ina da wasu tambayoyi a gare ki. Shin me ya sa a dukkan lokacin da idanuwana s**a yi tozali da ke, sai na ji zuciyata na kerma, ƙafafuwana na girgiza? Me ya sa nake jin k**ar na mallaki komai na duniya, kuma na zama mutum mai sa'a? Tabbas, ina ganin matsanancin son ki da na kamu da shi, shi ne amsar. Ina Son Ki.
NASARA
Dukkan wata nasara, ko wani ƙoƙarina na cimma wa ƙaddarata, da dukkan wani tinanina, ina yin su ne domin ke, domin yalwata farin ciki da jin daɗi a rayuwarki. Kina Raina, Domin Ina Son Ki.
HASASHE
A dukkan lokacin da nake tinani a kan soyayya, ina hasaso ki a cikin zuciyata. A dukkan lokacin da na ga wani abu mai tsananin kyau, kina bayyana a cikin tinanina. A dukkan lokacin da na shiga damuwa, na kan yi kewar rashin ki a kusa da ni. Amma a dukkan lokacin da nake cikin farin ciki, na kan rintse idanuwana, wanda a haka nake iya hango mu tare, mun zamo ango da amarya. Hm! Ina Son Ki.
RAYUWA
So abu ne da ke shammatar zuciya, ya sa idaniya kuka ko a wani lokaci ya sa mutum ya yi dariya. Ni dai na zamo mutum mai nasara, saboda samun ki a rayuwata ya nesanta ni da damuwa.
YANAYI
Ba wai kawai ina buƙatar martani ko kulawarki ba ne a soyayya, ina son ne, ki kasance cikin jin yadda nake ji a kan ki. Ki kasance cikin jin, zaki iya rayuwa da ni a kowane irin yanayi, k**ar yadda nake ji a cikin zuciyata. Ina Son Ki.
TAFKI
Furta kalmar SO a gare ni ba shi ne iya abun da nake tsammanin samu daga gare ki ba, saboda shi SO bai yi k**a da gadon furanni ba, haka kuma bai yi k**a da kofin ruwan sanyi ba, wani fage ne mai tarin ƙayoyi, kuma shi tamkar wani tafki ne mai cike da muggan halittun ruwa. Fatana karda ki bar ni na sha wuya a cikin sa.
SO
Babu wani da zai iya bayyanar da halin da zuciya ke shiga a dukkan lokacin da ta kamu da so, har da ni ma nan, duk da na kamu da shi. Hakan ce ta sa na mallaka miki zuciyata, domin ki leƙa cikinta, ki ga irin yadda na kamu da son ki. Ba ni da k**ar ya ke a wannan duniya. Ina Son Ki.
DALILI
Har yanzujama'a sun gaza samo dalili, b***e su samu amsar bayarwa ga tambayar, me ya sa nake son ki? Amma ke yanzu zan sanar da ke dalilin, ina son ki ne domin Allah, kuma ina fatan ki zamo uwar 'ya'yana. Ina nan cike da kewar rashin ganin Ki.
LAMBU
Tun bayan da na ɗanɗani yadda zaƙin soyayya yake, sai fuskata ta cika da murmushi, idanuwana s**a daina ganin munin komai, ya zamana komai na burge ni. Dalilin samun wannan sauyin nawa, na ga yadda na samu sa'ar tsintar kyakkyawan fure a cikin lambun furanni. Ina fatan mu kasance tare, ni da ke har abada. Ina Son Ki.
IDANUWA
Ina fatan bayyana miki yanayin da nake shiga a kullum, a tsakiyar dare ko safiya, a lokutan cin abinci da na bacci, ina kasancewa cikin kewar rashin ganin ki a gefena, tare da jin, da ma na rufe idanuwana na buɗe na gan ki zaune a kusa da ni, da a wannan lokacin zan ƙara tabbatar miki da cewa INA SON KI!
KALMOMI
Jin wasu 'yan kalmomi daga bakinki, ka iya canja rayuwata, zan iya yin komai da k**e so, matuƙar ina da dama, domin jin waɗannan kalmomi daga bakinki. Don Allah, ki daure ki furta min cewa, KINA SO NA.
MASOYINA
A dukkan lokacin da na kalli sararin samaniya, mai cike da tarin taurari, babu wani abu da nake fara tinawa face kai, saboda ka zamo tauraro mai haske fuska da zuciyata. Ina Son Ka.
CIWO
Tayaya zan iya bayyana maka yadda nake ji? Wani zugi ne na ciwo mai tsananin zafi, wani abu ne mai kawar da ido daga ganin komai, ya kore yunwa daga jikina, ya koren jin sautin komai sai nasa, bana ganin komai sai shi. Wai shin mene ne wannan? To ba komai bane face KAI MASOYINA. Hmm! Ina Son Ka.
MAFARKI
Babu sama da SO daga cikin abubuwan da ke saka ni farin ciki da walwala a rayuwata. Soyayyarka ita ce abun da nake matsanancin so. Rayuwa tare da kai, shi ne mafarkina. Ka amince mu rayu tare, hakan shi ne cikar burina. Ina Son Ka.
LOKACI
Zan kasance cikin kewarka, ina mai tinanin irin tsawon lokacin da muka kasance tare, cikin so da ƙaunar juna. Fatana a duk inda kake, zaka kasance cikin tina cewa INA SON KA.
GIDA
Kai ne wanda nake tinani a tsakiyar dare, kuma kai nake fara tinawa da sanyin safiya. Kai ne abun so na a tsawon rayuwa, kuma kai ne wanda nake fatan na rayu tare da shi a gidan Aljanna. Ina matuƙar So da ƙaunarka.
ZUCIYA TA
Son da nake yi maka, ba zai taɓa gushewa ko canjawa a cikin zuciyata ba, ko da a ce ka juyan baya, ni kuma zan zagayo na fuskance ka. Ina Son Ka.
SAKO MAI MUHIMMANCI
Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.
09/03/2022
https://www.facebook.com/105610588569892/posts/152556093875341/
🄽🄸.🄳🄰.🄺🄰🄽🅆🄰🅃🄰
ⓚⓐⓢⓗⓘ ④
ᴢᴀɪᴢᴏᴍᴜᴋᴜ ᴅᴀɢᴀ
🅛🅘🅚🅘🅣🅐🅝 🅜🅐🅢🅞🅨🅐
𝚊𝚢𝚒 𝚔𝚊𝚛𝚊𝚝𝚞 𝚕𝚊𝚏𝚒𝚢𝚊
Idan baku manta ba mun tsayane inda mm s azima tayimun tambaya
Ayazukuma zamu zamu cigaba
Tambayar ce ke sake mai maituwa akunaina da ma kwakwalwata
Ina jin kunyar bazan iya cewa ina suntaba sabida kunyar mm
Duke kainayi tareda wasa da abin rubutu dake hanuna yayin da acan tsakiyar fadar zuciyata tuni antaru anna mahawara dan ganin ansarda ta dace sai bayan wani dan lokaci sai axima ta zare tarkar darda ke karkashin hanuna tace bakabada ansaba ayau kuma kazama kurma
Ganin banadawata dabara bace nace eh ina sunta
Amma sainaga idan kai tsaye nafadi han mm zataga tamkar dan tayimun doline
Sainafara jawabi k**ar ha acikin toshashiyar murya
Amma aganinna azima ayanxu ai karatutake kuma kawu yanasun tayi karatu sosai gashi kuma Soyyaya itada karatu abune mai wahalar haduwa banasun nazama sanadiyar lalacewa karatun azima dan ni banyiba mm batace ko uffun ba bale takarayimun tanbaya hsk**a azima ganin hakayasa naci gabada cewa idan kawuyasamu labari zai kabadokar namadena zuwa gidan sa dan nasan bayasun azima nayin ma amala da duk samarin garin nan
Mm ta ce dakata kansamun tanbayatade
Nacigabadacewa
Banasun azima ta shiga fushin kawu hakafadaga ya sameta awajena kwanaki yiyimata duka to ayanxu idan yaji muna soyayya ai zata shiga matsala bawai banasun tabane amma ina tunani. Halin kawu
Anan mm tayima na bayani yadda Kasan wasiya take bamu harda zancinda yasamu farin ciki bakidaya takaredacewa ku kulada da kanku karkubi irin soyayyar zamani ta yaudara
Tambaya nasakowa mm da saida nakomajin kunya danayita
Wace kalar soyayya kenan mm murmushi ne mm tayi takaradacewa
Bawatabace face soyayyar yaudara da karya
Anan tafara antayomana bayani k**ar haka
Bawai mu kadai tayimaba harku samarida yan mata kuna ciki
Tafara k**ar ha
Abaya zakaga budurwa babu ruwanta dawani tara samari dan zaka samu budurwa ta issa aure amma babu saurayi gare ta saide zabin iyayenta kodayaya yake doli zata zauna da kunci ko da farin ciki
Amma nayanxu kuwa sakasamu budurwa batafi shekara 12 ba amma hartayi digiri Soyyaya abin damu soyayya kawai ta iyafadi amma tunanin ta kuwadabanne idande zaka sayamata waya kayimata anko batadamuba komizai faru tsakanin ku
Kodayake matsalar daga iyayene dan sune sukewa yayan su dama suyi abinda bai dace ba sabi da sun duniya
Zakaga yar ka ko yar ki tasaka kayanda basu dace dayayan mussulmiba sun fita kasuwa ko t**i dan sudauki hankalin samari
A ido burgewace amma kusani babu wani mai mutunci dazaiga kinyi shiga acikin haka kinatafiya akan t**i zai nemi aurin ki hak**a daga cikin dangi babu wanda zaiyi shayin yazo neman aurinki koda kin fito daga cikin matan da s**afi nagarin kyau
Takaradacewa gashi kuma ayanxu samari sun gurface sanadiyar wayoyin zamani tahanyar kalekale sunkaranci hanyoyin yaudara da iya shawo kan budurwa cikin sauki mafiyawancin su ba aure bane agabansu kawai zasuyitayimiki Soyyaya daga sunsamu kanki ko kin amintadasu harkikasake zasu lalata kimar gidan ku sannan sugudu
Wasu kuma samarin zakasamu duk bawannan ne agabansuba su abinda yake gabansu yin aure saide kuma kodayaushe Soyyaya kawai sukeyi babu sana a
Tokasani babu wanda zai dauki diyar sa yabakawai dan kanasun ta dan haka katashi kadage kanema idan danaka kazarce karamar magana bale akoraka
Idan nace zan kawo muku lasihar da mm tayi garemu ko to
Dan saida mukayi awa 1 da wasun yan mintuna muna sauraro abokina kanwata kaje k**anya kasamu bayani yafi kayita kashe lokacinka dan karanta kalaman Soyyaya wai zakaburge budurwa da su in da kake karantawa ita tana karan ta taya zakaburgetada abindayazamemata jiki amma idan ka kasance mai hada abubuwadayawa kuwa cikin sauki zakazama mai farin jini bawai sai anje gun boka ko malamin duba ne ake malakar tunanin yarin ya Amma kabiyoni zaka san tayaya zakasan yadda zak**alaki tunanin duk wata budurwa damayadda zaki malaki wani saurayi da yatsayamiki arai
Kirana agareku kuwa kar kuyi anfanida dubarata dan ganin kunyi yaudara dan kaima kanada kanwa kuma zaka iya haifar ya bawai kan samari ba kawai har yan mata dan sune sanadiyar saka samari yaudara bawai nace duk ba amma bafiyawancin su dan zaka samu budurwa ita damuwar ta tasamu mai kudi kuma gas to ki sani samun hakan sai mai rabo domin mai kudi kodayaushe damuwar sa yaga yatafi kasuwa ina yaga lokacin gyaran gashi gyaran kafa koyon kalamam Soyyaya da iya saka kaya
Haka dan boko shima kodayaushe aikonsa karatu kodayake anfi samun gayu acikin su Amma kuma mawuyacin abune asamu masu kudi to haka matasa masu jini ajika damuwarsu buge irinku gashi basada kudi 1.. 1 das**a taso daga gida masu kudi dan haka kinemi wandayadace da irin rayuwarki zakofi samun kwanciyar hankali
Waje nadawo azima tabiyoni tuno munsamu karfin kafa Soyyaya dan bamada wata fargaba munacikin nishadi saida dare yafa banyan isha.i ne kawu yazo mukatar beshi da murna haka nakasance cikin tunane da kewar azima ina ma axe kawu zai koma muci gabadasoya gashi ayanxune Soyyaya tafara gina babar burni hakade atsawun kwanakin nan tuni Facebook hadi da WhatsApp duk sun fita araina dan koshiga ma banayi dan wasu daga abokainama saide sukirani alokacin nafara dubawa naga sakoni dadama bazaiyima na iya lisafosuba namaida wasu wasu kuwa na wuce da su safiya tayi naso tafiya tadan kar Soyyaya tarufemuna ido muyi abinda baik**ata ba agaban kawu ya haumuda fada dan shikawu babu ruwansadawata nasiha
Tap ankauyi kuskure bayan safiya tayi sai muka fara fira k**ar haka ayanzu gida ani aiki kukeyi nayi dan shiru daga baya yakara tambaya
Banaceba dan banyi firadasuba to tunda
kadade anna kaje kagansu
Haka da rana tayi sai kawu ya kira azima yasamu agabadatan baya uhun komai da lokacin sa lale ko gabadagabata duk kunyarda najiya agaban mm tayau talinka
Saide nace kubiyomu musha dariya da al.amarin yarinta
Alabari nagaba
Kuyimun share da like gami da
Pollows
Gamai tanbaya kuma kokarin bayani kowani zancin yaduba kasan hotun nan zaiga wajan sako kai tsaye zai fadi abindayake ransa niko Zan mayar masa da martani daidai zan cin sa
Dawannan nake cewa kubuta lafiya
Naku likitan masoya ke gaida ku
09/03/2022
Ummi rahab zaku,iya
Yarda nijin hilani CE💕💕
09/03/2022
SHAWARWARI GA MASOYA
1- Ki kasance me matuqar nuna damuwa ga masoyinki Wanda Shima ya damu dake, hakan zai qara Masa qaunarki a Cikin Zuciyarsa!
2- Kada ki kasance me fadin "Ya Akayi?" Yayin amsa Kiran wayar masoyinki, domin hakan zaisa yaji Babu Dadi a Zuciyarsa!
3- Ki kasance a Cikin walwala da jindadi a lokacin da Abin farin Ciki ya samu masoyinki wannan ma yakan qara Masa qaunarki fiye da wadda yakeyi a yanzu!
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Tripoli