Djamilou hadimin mazan allah
Informations de contact, plan et itinéraire, formulaire de contact, heures d'ouverture, services, évaluations, photos, vidéos et annonces de Djamilou hadimin mazan allah, Niamey.
AKWAI MATA KALA 6 KO DA KUDINKA SAI KA HADA DA SALLAR DARE KAFIN KA SAMU AUREN SU.
Na san abin da ya fara fado muku a rai shine kyau, to ba haka bane! A nan ba lissafin kyau ake yi ba, ina magana ne a kan abin da yafi kyau amfani wanda muke wasa da shi. Kyau yana kodewa, amma wadannan halayen sune suke rike gida.
Koda kana da Miliyoyi, idan har kana son samun daya daga cikin wadannan matan guda 6, wallahi sai ka tashi tsakar dare ka roki Allah:
1. Mace Mai Qana'a:
Matar da idan ka kawo N1,000 zata karba ta yi maka addu'a tamkar ka bata N100,000. Ba ta gasa da kawayenta, kuma bata matsa maka a kan abin da baka da shi. Kudinka ba zai sayi wannan zuciyar ba.
2. Mace Mai Kare Sirrin Ogan Gida:
Matar da koda za ku yi fada har ku dambace, muddin kuka fita waje, zata nuna wa duniya kai ne sarki. Bata kai gulmarka wajen iyayenta ko kawayenta. Wannan asibitin sirrin, sai da addu'a ake samunta.
3. Mace Mai Ilimin Tarbiyya, Uwar 'Ya'ya: Kudi suna sayen 'yar shila, amma ba sa sayen wacce zata koya wa 'ya'yanka Alkur'ani da tsoron Allah a lokacin da baka nan.
4. Mace Mai Hangen Nesa, Mai Bada Shawara: Matar da idan ka bata jari, maimakon ta sayi atamfa, tunanin yadda zata juya kudin ta tallafa maka take yi. Wannan ba mace bace kawai, abokiyar cin nasara ce.
5. Mace Mai Hakuri A Lokacin Tsanani: Matar da idan ka fadi a kasuwa ka rasa komai, ba zata hada kayanta ta koma gidan su ba. Zata dafa kafadarka tace "Oga zamu sake farawa, Allah Yana tare da mu."
6. Mace Mai Tsoron Allah A Boye: Matar da baka bukatar ka duba wayarta ko ka sa mata 'yan leken asiri idan ta fita. Tsoron Allah da ke zuciyarta shine asalin garkuwar da take kare maka mutuncinka.
Maza ku farka, Kudi suna kawo mace a gida, amma kyakkyawan hali da rokon Allah suke kawo natsuwa
DOKOKIN RAYUWA GUDA 7 WADANDA ZASU TSERATAR DA MAKOMARKA A YAU.
Daina tunanin rayuwa zata baka abin da kake so a kan faranti na zinare. Idan har kana son tsira da mutuncinka da lafiyar zuciyarka, ina son ka hadiye wadannan dokokin guda 7:
1. Yi Sulhu Da Jiya:
Kada ka bari kura-kuran baya su ci gaba da sarrafa yau dinka. Abin da ya faru ya riga ya faru, ka yafe wa kanka ka saki zaren!
2. Kawar Da Kai Daga Surutun Mutane:
Abin da mutane suke tunani a kanka ko suke fada a bayanka ba shi da amfani a rayuwarka. Suna fada ne, kai kuma kana ci gaba da tafiya. Share su.
3. Lokaci Yana Warkar Da Komai:
Duk irin zafin da kake ji a yau, wataran zai zama labari. Ka yi hakuri ka bawa abin lokaci, wutar zata mutu.
4. Daina Kwatance:
Kada ka taba hada lissafin rayuwarka da ta wani, Kowane mutum da irin jarrabawar da aka tsara masa da kuma lokacin nasararsa. Ka tsaya a kan layinka.
5. Natsu A Cikin Duhu:
Babu laifi idan har a yanzu baka da dukkan amsoshin matsalolinka. Ka yarda da tsarin yadda abubuwa suke tafiya. Ka kwantar da hankalinka.
6. Farin Cikinka Alhakinka Ne:
Babu wani dan adam ko wata Gwamnati da take da alhakin faranta maka rai in ba kai kanka ba. Tashi ka kera natsuwarka.
7. Yi Murmushi A Cikin Guguwa:
Ko duniya tana yi maka zafi, ka koyi yin murmushi. Ba kai kake dauke da nauyin duniyar nan ba, Allah Ne Yake sarrafa ta. Yi murmushi.
Idan zaka iya Hadiye wannan kwayar gaskiyar, ka gama cin duniya da yaki da izinin Allah.
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.