AREWA TV
News from 36 States of Nigeria �
16/08/2026
An k**a wata ƴar ƙasar Chadi da ake nema kan zargin kisan kai a Kano
Rundunar ’yansandan Najeriya, ta hannun jami’an ƴansandan duniya INTERPOL na National Central Bureau (NCB), Abuja, ta k**a wata ’yar ƙasar Chadi, Mahadijiria Abdoulaye, da hukumomin ƙasarta ke nema bisa zargin hannu a kisan Nazik Mahamat Saleh.
An ce an azabtar da Saleh tare da kashe shi a ranar 3 ga Mayu, 2026, lamarin da ya sa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta N’Djamena ta bayar da sammacin k**a Abdoulaye da abokiyar aikinta, Fatime Senoussi Mouktar, a ranar 22 ga Yuni, 2026.
Kakakin Rundunar ’yansandan Najeriya, CSP Ani Iniedu, ya tabbatar da k**a Abdoulaye, inda ya ce an kuma alakanta ta da safarar miyagun ƙwayoyi a Chadi.
A cewarsa, Abdoulaye ta tsere zuwa Najeriya bayan faruwar lamarin, kafin jami’an INTERPOL NCB Abuja su gano inda take tare da k**a ta a ranar 5 ga Agusta, 2026, a Railway Quarters da ke ƙaramar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano, bayan wani samame da aka gudanar bisa bayanan sirri.
Kakakin ya ce a ranar 14 ga Agusta, 2026, an mayar da wadda ake zargin zuwa N’Djamena ta Chadi, ta hanyar Lomé, babban birnin Togo, ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwar ’yansanda tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce aikin ya gudana ne tare da haɗin gwiwar INTERPOL NCB Abuja da takwarorinsu na N’Djamena domin tabbatar da cewa Abdoulaye ta koma Chadi don fuskantar shari’a.
A nasa bangaren, Sufeto-Janar na ’yansandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya yaba wa jami’an INTERPOL NCB Abuja bisa ƙwarewa, jajircewa da kyakkyawar haɗin gwiwa da takwarorinsu na Chadi.
Disu ya ce nasarar k**a tare da mayar da wadda ake nema Chadi na nuna ƙudirin rundunar na tabbatar da cewa masu gudun hijira daga shari’a ba za su yi amfani da iyakokin ƙasashe wajen tsere wa hukunci ba.
2027 Election 🗳️ Part 27
2027 Election 🗳️ Part 26
2027 Election 🗳️ Part 25
2027 Election 🗳️ Part 24
2027 Election 🗳️ Part 23
2027 Election 🗳️ Part 22
2027 Election 🗳️ Part 21
2027 Election 🗳️ Part 20
2027 Election 🗳️ Part 19
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Abuja
900104