Elaaj Sirrin Tarbiyya
Tarbiyyar yara • Hikimar aure • Gina iyali nagari. Shawarwari masu amfani domin kawo waraka da natsuwa a cikin gida.
16/05/2026
🚨 Kamar yadda muka sanar a rubutun jiya, In sha Allah za mu fara sabon program na musamman akan hanyoyin warware matsalolin tarbiyya.
Daya bayan daya, za mu dinga daukar kowace matsala domin:
✔️ mu bayyana musabbabin ta
✔️ illolin ta
✔️ sannan mu kawo hanyoyin gyara matsalar ta fuskar addini da kuma zamani (Physiology).
A cikin program ɗin, za mu tattauna matsaloli k**ar haka:
1. Rashin addini
Idan zuciya babu tsoron Allah, gyaran ɗabi’a zai yi wahala.
2. Rashin girmama iyaye
Alamar rushewar tarbiyya da biyayya tun daga gida.
3. Yawan amfani da TV ko waya
Babbar ƙofa zuwa lalacewar tunani da kwaikwayon ɗabi’u marasa kyau.
4. Rashin jin magana / rashin zama kurum
Idan ba a gyara tun ƙuruciya ba, yakan rikide zuwa tawaye.
5. Rashin kunya
Idan kunya ta fita, yaro zai iya aikata komai ba tare da nadama ba.
6. Kwaikwayon mutanen banza
Musamman ta hanyar social media, films, celebrities, da abokan banza.
7. Kungiyar banza
Peer pressure na iya rushe tarbiyyar gida cikin sauƙi.
8. Rashin son karatu
Matsalar da ke lalata makomar yara a hankali.
9. Rashin haƙuri
Yana haddasa fushi, gaggawa, da yanke shawara mara kyau.
10. Yawan faɗa
Yawanci yana fitowa daga rashin kulawa da rashin tarbiyyar magana.
11. Rashin tausayi
Yana sa zuciya ta taurare har mutum baya jin ciwon wasu.
12. Ƙarya
Yawanci tana farawa ne saboda tsoro, son kubuta daga hukunci, ko kwaikwayon manya.
13. Sata
Sak**akon rashin tsoron Allah da son abin duniya.
14. Rashin tsafta
Muhimmin bangare na tarbiyya da addini da ake sakaci da shi.
15. Son duniya
Yana haifar da hassada, girman kai, da rashin godiya.
16. Shaye-shaye
Yawanci yana farawa daga abokan banza da kallon abubuwa marasa kyau.
17. Zina da dangoginta
Babban sak**akon haɗuwar sha’awa da rashin tarbiyya.
18. Matsalolin shirka
Sak**akon raunin fahimtar tauhidi da addini.
📌 Ku kasance tare da mu domin kowace matsala za mu tattauna ta dalla-dalla tare da hanyoyin magance ta cikin yardar Allah.
Kuyi sharing domin bada naku taimako.
✍️ Elaaj Sirrin Tarbiyya
14/05/2026
Idan kana da yaro mara jin magana, kuskure mafi girma da zakayi shi ne ya kasance baka karanta wannan post din ba.
Idan kuna son ilimin dabarun tarbiyya yara da mafita ga matsalolin ma'aurata kuyi following wannan page din na Elaaj Sirrin Tarbiyya domin kada ku rasa darussa masu amfani.
Zamu fara asalin program akan dabarun da zakayi idan kana da yaron ko wani dake baka ciwon kai game da matsaloli k**ar haka
1. Rashin kunya
2. Rashin girmama iyaye
3. Rashin son karatu
4. Yawan amfani da TV ko waya
5. Rashin hakuri
6. Rashin tausayi
7. Rarya
8. Sata
9. Shaye-shaye
10. Zina da dangogin ta
11. Kungiyar banza
12. Rashin addini
13. Yawan faɗa
14. Rashin tsafta
15. Son duniya
16. Kwaikwayon mutanen banza
17. Rashin jin magana ko rashin zama kurum
18. Matsalolin shirka
Idan akwai wata matsala da kuke fama da ita wacce ban kawo ba sai ku sanya ta a comment section.
Please kuyi sharing domin ceton sauran al'umma.
13/05/2026
Maganar Uwa mai hikima zuwa ga yaron ta daya faɗi jarabawa a makaranta!
Wata rana, wani yaro ya dawo gida daga makaranta, takun sa a hankali, zuciyar sa cike da fargaba kuma fuskarsa ta nuna zallar damuwa.
A hannun sa akwai takardar sak**akon jarrabawar makaranta wanda sam bai yi kyau ba.
Da mahaifin sa ya duba sak**akon, ai kuwa sai ya fusata yayi ta yiwa yaron fada, yaron yayi ta kuka. Haka yaron nan yaji k**ar rayuwar sa bata da wani sauran amfani.
Mahaifiyar yaron na daga gefe tana kallon abinda ke faruwa tsakanin yaron da baban sa.
Bayan mahaifin yaron ya wuce, sai mahaifiyar ta matso ta zauna kusa da yaron, cikin magana mai sanyaya zuciya ta ce masa:
"Karka damu da abinda ya faru. Ni ban damu da sak**akon da ka samu a yanzu ba… abin da nake so shine kada ka karaya kuma kada ka daina ƙoƙarin da kake yi a yanzu, kawai kadan ƙara maida hankali. Allah yayi maka albarka”
Sanadiyar wannan maganar, yaron nan hankalin shi ya kwanta kuma ya sawa ran sa cewa lallai zai yi duk mai yiwuwa domin ganin yayi abinda zai sa mamar shi alfahari da shi a gaba.
Sai yaron ya bude baki ya cewa mamar sa:
"Gaskiya mama na gode da yadda kika sa na fahimci ina da sauran amfani a rayuwa. Lokacin da baba yake mini fada wallahi har na cire rai zan yi abin kirki a rayuwa. Amma yadda ki kayi mini magana yanzu yasa na fahimci ina da sauran dama"
Haka wannan magana ta tsaya a zuciyar yaron nan na tsawon shekaru masu yawa kuma maganar tayi sanadiyar cigaban yaron har ya zama abun alfahari cikin al'umma.
⚠️ GARGADI:
Yara basa manta irin maganar da muke musu da kuma yadda muka mu'amulan ce su.
Wasu kalmomi suna gina yaro, wasu kuma suna karya ƙwarin gwuiwar su a hankali.
Wace magana ce aka taba muku tun kana yara har yanzu baku manta ba?
10/05/2026
😭 Hmmmm, Gaskiya akwai damuwa... 🤔
Wai wasu bayin Allah su biyu a wasu lokuta, sun ga yanayin posts dina akan tarbiyya.
Saboda rashin sanin me ake nufi da tarbiyya da kuma mahimmancin ta, sai daya daga cikin mutanen yake ce mini wai "kai a wa da zaka shiryar da mutum" 🤔
Abun sai ya bani mamaki saboda ni ban ce ina shiryar da mutane ba ne, kawai ina karantar da hanyoyin tarbiyya ne. Shi a tunanin shi idan ance tarbiyya kawai zallar shiriya ake magana 😭
Dayan mutumin kuma a wani lokacin daban yake ce min wai "ka je ka fara yiwa naka yaran tarbiyya" alhali bai taɓa sani na ba kuma bai san yadda nake gudanar da mu'amala tsakanin nawa family ba.
Duk irin abubuwan nan suna faruwa ne saboda mun jahili al'amarin tarbiyyar da kuma zamantakewa.
Mun dauka babu wani abu da ake yiwa yara, haka kawai suke ta shi cikin tarbiyya mai kyau.
Wallahi a wannan lokacin bawai yara kadai ke bukatar ayi training din su akan tarbiyya ba, harda mafi yawan iyaye 😭
Wallahi iyaye kada mu dauki wannan al'amari da wasa domin lafiya ƙalau sai mutum ya gan shi a wuta sanadiyar hakan.
Allah yana cewa "Ya ku wadanda ku kayi imani, ku kiyaye kan ku da kuma iyalan ku daga shiga wuta"
Wannan ayar kadai ta isa ta nuna mana cewa tarbiyya dole ce.
Allah yayi muna mafita. Soon asalin program din mu akan hanyoyin daura yara akan Tarbiyya zai fara in sha Allah.
Ku shirya… domin akwai abubuwa masu anfani sosai da zasu taimaki iyaye da ma’aurata. 🤎
09/05/2026
🤔 Ko kun san cewa gina kyawawan ɗabi'u ga yara (tarbiyya) da kuma zamantakewar aure akeyi?
Da yawa daga cikin matsalolin yara da aure a yau… rashin ilimi ne yake jawo su.
Ba haka kawai yara suke tashi da ɗabi'un kirki ba, kuma aure ba haka kawai yake kyau ba?
Kamar yadda gidajen 🏠 da muke zama a ciki ba daga sama s**a faɗo ba, gina su mukayi.
To haka suma kyawawan ɗabi'u (tarbiyya) da kuma zaman aure mai kyau gina su akeyi ta hanyar nemin ilimin gina su da kuma aiki da ilimin.
A wannan zamanin da muke ciki, gaskiyar magana kusan kashi tamanin (80%) din al'ummar mu a yau tunanin suke haka kawai yaro yake zama na kwarai kuma zaman aure mai kyau haka kawai yake tabbata. Hmmmmm 😭
Wallahi idan ba muyi da gaske ba, yadda yaran mu suke rayuwa a yanzu, da yawan iyaye sai Allah ya hukunta su sanadiyar sakacin bada tarbiyya data dace.
Ɓangaren zaman aure kuma da yawa ma'aurata sai Allah ya hukunta su sanadiyar cutar da junan su.
Kamar yadda ya zama wajibi kowa yasan ilimin sallah, azumi, zakka da mak**antan su. To haka ya zama wajibi kowa ya nemi ilimin tarbiyyar da zamantakewar aure.
Wallahi idan bamu nemi ilimin nan guda biyu ba (ilimin Tarbiyya da Ilimin zamantakewar aure), da yawan mu sai Allah ya hukunta mu.
Jahilci baya zama uzuri gurin Allah akan wanda yaƙi tashi ya nemi ilimin da ya zama wajibi.
In sha Allah gaba kadan zan fara sakin wani program da muka shirya akan yadda ake tafiyar da tsarin bada tarbiyyar yara da kuma zamantakewar aure.
Dan Allah kuyi sharing domin ceton sauran ƴan uwa da ga faɗa wa hallaka. Ku danna follow domin samun ganin post din mu dake tafe.
08/05/2026
Wata rana yaran ku zasu girma…”
Wata rana:
* waɗannan ƙananan yaran na ku zasu girma
* zasu daina neman ku a kullum
* zasu fara rayuwar su daban
Amma abubuwan da kuka saka a zuciyar su…
zasu ci gaba da rayuwa tare da su.
Yara basa tuna: nawa kuka kashe masu na kudi. Amma suna tuna:
maganganun da kuka rinƙa furta musu, yadda kuka yi mu'amala dasu da kuma yadda kuka kula da su.
Kada ku jira sai lokaci ya ƙure kafin ku nemi ilimin da ya dace domin baiwa yaran ku tarbiyya da mu'amalar da ta dace.
Tarbiyya ba aikin rana daya bace… amma kowace rana tana da tasiri. Kuyi kokarin farawa tun da wuri.
Akwai programs dana shirya akan hanyoyin daura yara akan shiriya, suna nan zuwa gaba kaɗan in sha Allah.
Allah kadai ke shiryawa amma kuma ya zama wajibi akan iyaye su yi na su aikin da Allah ya daura musu na kula da yaran su.
Allah ya bamu ikon tarbiyyar yaran mu yadda ya k**ata. Ameen
Al'amarin zaman aure da kuma tarbiyyar yara wallahi sai da hikima.
Masu sanya hikima su s**afi yin nasara akan masu sanya tsauri ko karfi.
03/05/2026
⚠️ Kalma ɗaya daga bakin iyaye… na iya gina ko rusa zuciyar yaro.
Wata rana, Iyaye mata guda biyu suna tafiya da ‘ƴaƴan su.
Uwa ta farko da Ƴar ta s**a hango wani mutum a gefen hanya… tufafin sa sun yi kaca kaca da datti, yana ta aikin wahala.
Uwa ta farko ta kalli ‘yarta ta ce:
Kin ga wancan mutumin, Idan ba kiyi kokarin wajen karatu ba… haka zaki zama k**ar shi”.
Sai ‘Yar ta kalli mutumin cikin gyama da walakanci.
Ita kuma Uwa ta biyu da ta ga mutumin. Sai ta k**a hannun ‘yarta a hankali, ta ce:
“Idan kika yi kokari wajen karatu… wata rana zaki samu damar taimaka wa bawan Allah can.”
Sai ‘Yar ta, ta sake kallon mutumin nan zuciyar ta cike da tausayi da kuma son taga ta taimakawa ire iren sa.
Sanin irin magana da sanya hikima wajan yiwa ƴaƴa magana yana daga cikin hanyar tarbiyya mai kyau.
A mafi gaskiyar magana yara ba sa manta irin kalaman da iyayen su ke fada musu.
Kuyi nazari sosai... Shin kun fahimci hakan tsakanin ku da yaran ku? 🤔
02/05/2026
🤎 GASKIYA MAI TAƁA ZUCIYA A CIKIN RAYUWAR MA'AURATA DA MUKA KASA GANEWA 😭.
Yau akwai ma’aurata da:
👉 Suna kwana a gado ɗaya… amma sun daina magana da juna na tsawon kwanaki 😞
👉 Ƙananan abubuwa sun rikide sun zama babbar kiyayya tsakanin ma'aurata 😭
👉 A waje suna dariya… amma a cikin zuciya sun gaji da junan su 😞
Shin ashe bai k**ata mu tambayi kan mu ba… Shin wannan shi ne auren da iyayen mu s**a rayu a kai 🤔 ?
A da:
– Mafi yawan Iyayen mu basu da komai na dukiya ko kayan alfarma… amma suna da zaman lafiya
– Sun fi mu haƙuri… ba wai don ba su samun ƙuncin zaciya ba
– Sun fi mu boye sirrin gidan su… ba sa kai sirrin su kasuwa
– Suna ƙoƙarin gyaran cikin gidan su… ba sa jiran duniya tazo ta masu gyara musu
A yau kuma:
– Ƙananan matsaloli sai an sanar da kowa
– Ana kwatanta rayuwar aure da abin da ake gani a waya (social media da kuma fina - finai)
– Rashin haƙuri ya zama abin riƙo
– Shawarar waje ta fi karfi akan ma'aurata suyi ƙoƙarin fahimtar junan su
Gaskiya dole sai muyin da gaske. Kada mu tsaya akan tunanin gyara kadai. Dole sai mun hada da aiki.
👉 A tunanin ku, menene ainihin abin da ke lalata rayuwar aure a wannan lokacin?
👉 Menene iyayen mu s**a riƙe da mu muka saki?
👉 Idan za ku ba da shawara guda ɗaya — wace hanya ce za ta fi kawo gyara mai dorewa?
💬 Ku rubuta ta ku fahimta da kuma shawara a comment section
📌 Ku yi sharing da kuma follow. kalma daya daga gare ku na iya gyara rayuwar auren wani gida.
30/04/2026
🤔 "Mugu” da “Mahaukaciya” kalmomi biyu da ke hana aure ko kashe zaman aure a hankali 😭
Wallahi, idan ka zauna a unguwa ka saurari hirar jama’a, zaka ji irin waɗannan kalamai:
👉Maza na cewa “Mata ai mahaukata ne”
👉 Su kuma Mata na cewa “Maza ai mugaye ne”
Amma gaskiyar magana ita ce…
ba a haife mu da wannan tunanin ba.
Mun koya ne: daga tarbiyya, labaran mutane, da kuma abubuwan da muka gani ko muke fuskanta.
Sai ya zama muna shiga gidan aure da tunanin kariya, ba da tunanin gina soyayya ba.
⚠️ Abin da wannan tunanin ke haifar wa:
* Muna zargin abokan zaman mu tun kafin suyi laifi
* Muna fassara kuskure a matsayin mugunta
* Muna mayar da martani da cikin fushi
A ƙarshe kuma… Sai aure ya koma filin wahala maimakon wurin natsuwa.
* Mace zata shiga gidan aure tana tunanin: “Dole na yi hattara, maza ba abun yarda bane.”
* Namiji shi ma zai shiga gidan aure da tunanin: “Mata ai sai an sanya ƙarfi kafin su gyaru.”
⚠️ Abin da ke faruwa a rayuwa ta yau da kullum:
Miji ya dawo gida a gajiye ko kuma an ɓata masa rai daga waje. Abu kaɗan akayi, sai yayi maganar da bata k**ata ba…
Daga nan sai Mace ta ce: “Ga shi nan kuwa, wallahi muguntar sa ta fara fitowa fili 😳 .”
A dayan bangaren kuma:
Mace za ta yi kuskure ko ta ɗan yi magana mara daɗi…
Sai miji ya ce: “Ai dama na faɗa, mata mahaukata ne.”
Alhali gaskiyar magana ita ce:
gajiya ce… rashin fahimta ne… ko wata damuwa ta daban.
Amma saboda tunanin da muka riga muka ɗauka — sai mu juya komai ya zama laifi.
Kada fa mu manta Annabi (S.A.W) ya riga ya gargade mu:
“Duk wanda ya yi imani da Allah da Ranar Lahira, ya faɗi alheri ko ya yi shiru.”. Ya zamuyi da wannan hadisin? 🤔
Ba wai magana kawai ake nufi ba…
har da irin tunanin da zakayi cikin zuciya. Ya k**ata ya zama na alkhari.
Yanzu menene mafita
Dole mu fahimci cewa ba gidan da ba'a samun matsalar zamantakewa…
amma ya zama wajibi:
✔️ Mu tuna dalilin da ya haɗa mu itace Ibada, da kuma girman albarka da lada da Allah yasa cikin aure.
✔️ Mu daina kallon juna da tunani mara kyau kuma mu koyi yiwa juna uzuri.
✔️ Mu rage saurin fushi... Ba komai bane yake bukatar magana ko faɗa ba, wani lokaci shiru ya fi zama alkhari.
✔️ Mu kyautata zato ga juna
Ba kowane kuskure bane mugunta, wani lokaci rashin fahimta halin da juna suke ciki ne.
✔️ Mu fara gyara kuskuren mu, ma'ana kowa yayi kokarin kallon kuskuren sa kuma ya gyara, kafin na dan uwan sa.
✔️ Mu koyi zama mu tattauna cikin natsuwa... Ba sai matsala ta yi girma ba kafin mu yi magana.
✔️ Mu gina aure da tausayi, hakuri, yafiya, sauraron juna, gina juna, ba rusa juna ba, da fahimta su zama tushen zamantakewa.
Daga Karshe ya k**ata mu tuna: 🤝 Mu fa ba mala’iku bane… Kowa na kuskure kuma kowa na da rauni.
Wallahi… kalma ɗaya na iya lalata zuciya. Haka kuma kalma ɗaya na iya gyara rayuwa.
👉 Shin kuna fama da waɗannan matsalolin kuwa?
Ku danna follow da share idan kun ji dadin wannan tunatarwa.
Zaman auren
Miji mugu da Mata mahaukaciya
Coming soon
🥸
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Telephone
Website
Address
Abuja
840212