Iconic Times24 Hausa
Iconic Times24 Hausa, sahihiyar kafar yaɗa labarai daidai da zamani.
Jawabin Mataimakin Sakataren kungiyar RTEAN reshen jihar Kano, Badamasi Muhammad Zakari bayan sun kammala Al-Kunutu.
08/03/2026
Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya sanar a ranar Lahadi cewa an zaɓi Mojtaba Khamenei domin ya gaji mahaifinsa a matsayin jagoran addini na ƙasar.
Sanarwar ta tabbatar da jita-jitar da aka daɗe ana yi cewa Mojtaba, wanda aka dade ana kallonsa a matsayin wanda zai iya gaje kujerar, zai iya hawa wannan muƙami mai matuƙar daraja a ƙasar.
Duk da irin tasirin da yake da shi a cikin tsarin siyasa da na addini a Iran, Mojtaba bai taɓa riƙe wani muƙami da aka zaɓe shi ta hanyar zaɓe ba, kuma bai yi aiki a wata hukuma ta gwamnati a hukumance ba.
Naɗin nasa ya zo ne bayan harin Amurka da Isra'ila ya kashe mahaifinsa, Ayatollah Ali Khamenei.
08/03/2026
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a ƙaramar hukumar Lamurde.
Gwamnatin jihar ta bayyana a yammacin ranar Lahadi cewa dokar hana fitan ta fara aiki nan take, bayan sake barkewar rikici da karya zaman lafiya a wasu al’ummomi da ke yankin.
“Gwamnati na kallon wannan tashin-tashina a matsayin abin da ba za a amince da shi ba, don haka ta umarci jami’an tsaro su tabbatar an aiwatar da dokar hana fitan ba tare da sassauci ba,” in ji Fintiri a cikin wata sanarwa da Sakataren yada labaransa, Humwashi Wonosikou, ya fitar.
Gwamnan ya kuma yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana karya wannan umarni, ko mutum ɗaya ko ƙungiya, za a k**a su kuma a hukunta su bisa doka.
Sai dai ya bai wa al’ummar da ke bin doka tabbacin cewa gwamnatinsa na da kudurin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da tabbatar da tsaron kowane ɗan ƙasa.
08/03/2026
Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da cewa mutum ɗaya ya rasu, yayin da wasu biyar s**a shiga hannun ‘yan bindiga a wani hari da aka kai ƙauyen Mallamawar Yari da ke gundumar Gawakuke, a ƙaramar hukumar Kware.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar lokacin da wasu ‘yan bindiga s**a mamaye ƙauyen, suna harbe-harbe ba kakkautawa wanda ya jefa mazauna yankin cikin firgici.
Tun da farko, wasu rahotanni da ke yawo a kafafen sada zumunta sun yi zargin cewa maharan sun sanya hijabin mata ne domin kauce wa zargi yayin kai harin.
Sai dai kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmed Rufai, ya musanta wannan ikirari.
DSP Rufai ya ƙara da cewa mutanen da aka sace sun haɗa da mata uku da maza biyu. Ya ce jami’an tsaro sun fara bincike tare da ƙoƙarin gano inda maharan suke domin ceto waɗanda aka sace cikin koshin lafiya.
08/03/2026
Shugaban karamar hukumar Nassarawa kuma Mataimakin Shugaban ALGON na Kano ta Tsakiya, Ambasada Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye), ya kaddamar da wani shirin tallafawa mata sama da 200.
Shirin na bayar da tallafin kuɗi na ₦50,000 ga kowace mace daga cikin wadanda aka zaba domin taimaka masu wajen bunƙasa ƙananan sana’o’insu tare da ƙarfafa masu gwiwa wajen samun ‘yancin tattalin arziki.
An kaddamar da shirin ne a madadin shugaban karamar hukumar ta hannun Sakataren Karamar Hukumar, Hon. Ado Muhammad Mai Kaba Hotoro. Ya bayyana cewa an samu damar aiwatar da wannan shiri ne sak**akon goyon baya da jajircewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wajen tallafawa mata da kuma ƙarfafa rawar da suke takawa wajen bunƙasa tattalin arziki.
A cewar sanarwar da jami'ar hulda da jama'a ta karamar hukumar,
Hadiza Yusuf Idris ta fitar, an ce
mata na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban al’umma, don haka tallafawa sana’o’insu zai taimaka wajen inganta rayuwar jama’a tare da ƙarfafa ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa.
Da yake jawabi a madadin kansilolin karamar hukumar, Shugaban Majalisar Karamar Hukumar, Hon. Aliyu Musa Jibo, ya yaba da ƙoƙarin Shugaban Karamar Hukumar Nassarawa da kuma Gwamnan Jihar Kano bisa jajircewarsu wajen inganta walwalar al’umma, musamman mata da matasa.
Waye Olatunji Rilwan Disu, Sufeton ƴan sanda Najeriya na 23?
Fatima Jafar Muhammad na dauke da rahoto a kan tarihin sabon Sufeton ƴan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a ranar 24 Fabrairu, 2026.
A taimaka a rika dawo mana da kwanuka bayan mun haɗa 'Ramadan basket.'
Abin da wasu ƴan mata a Kano ke faɗi a ranar mata ta duniya.
08/03/2026
Mambobin RTEAN a Kano sun yi sallar Al-ƙunutu kan rikicin ƙungiya
Mambobin ƙungiyar sufuri ta Najeriya (RTEAN) reshen Kano sun gudanar da sallar Al-ƙunutu domin neman taimakon Allah SWT da adalci kan rikicin cikin gida da zargin tsige masu hakkokinsu.
An gudanar da addu’ar ne karkashin jagorancin shugaban ƙungiyar a jihar, Abdullahi Yahaya Baba Maiduniya a ƙasan gadar Muhammadu Buhari bypass da ke Hotoro a Kano.
Da yake magana da manema labarai bayan sallar a yau Lahadi, shugabannin ƙungiyar sun bayyana cewa suna cikin damuwa kan abin da s**a kira zalunci daga shugabancin ƙungiyar na ƙasa.
Sun ce an k**a wasu daga cikin shugabanninsu tare da tsare su a ofishin ‘yan sanda na tsawon kwanaki uku ba tare da bin ƙa’ida ba.
Daga cikin waɗanda aka k**a akwai shugaban RTEAN na Kano, Abdullahi Yahaya Baba Maiduniya, da mataimakinsa, Mustapha Jibrin. Sauran sun haɗa da sakataren ƙungiyar, Abubakar Balarabe, da kuma sakataren kuɗi, Abubakar Nuhu.
A cewar mambobin ƙungiyar, ana ƙoƙarin tilasta musu su sanya hannu a wata takarda da za ta nuna cewa sun fice daga ƙungiyar.
Mambobin RTEAN a faɗin Kano sun ce suna matuƙar damuwa da wannan lamari. Sun bayyana cewa yawancin shugabannin rassa na ƙungiyar suna goyon bayan Baba Maiduniya.
Sun ce daga cikin rassa 36 na ƙungiyar a jihar, shugabannin rassa 34 suna tare da shi, yayin da rassa biyu kaɗai ne ba sa mara masa baya.
Haka kuma, mambobin ƙungiyar sun roƙi gwamnan Abba Kabir Yusuf da ya duba matsalar da ta dabaibaye su domin kawo ƙarshen abin.
08/03/2026
Wata gobara ta kone masu haƙar zinare da safiyar ranar Lahadi a garin Dantsuntsu da ke Batsari a Katsina.
Rahotanni sun bayyana cewa ana tsoron mutum biyu gobarar ta hallaka, amma gawar ɗaya kawai aka gani.
Gobarar ta lalata kusan dukkanin shagunan da ke sayar da kayayyaki ga dubunnan matasan da ke aikin tacewa da wanke zinare.
Waɗannan matasa suna amfani da kayayyakin ne wajen sarrafa zinaren da ake haƙowa daga cikin dajin da ke yammacin garin.
Garin Dantsuntsu yana cikin yankin yammacin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Bayan wannan gari, babu wani gari a yammacin yankin sai gonaki da ke ci gaba har zuwa dajin Zamfara.
📸 Alfijir Radio
Shin, kuna kai dabbobinku asibiti? Ko kuma barin su kuke su ƙarata idan rashin lafiya ta k**a su?
ICONIC TIMES24 ta ziyarci ɗaya daga cikin asibitocin dabbobi da ake da su a Kano.
Ga rahotonmu a nan 👇
Tunatarwar Ramadan tare da Malama Binta Sa'ad kashi 5
Tunatarwar Ramadan tare da Malama Binta Sa'ad kashi na 4.
Click here to claim your Sponsored Listing.