D boy's
only for star's boys and girls' to make my brother's and sisters happy
10/04/2026
DUNIYA ZA TA IYA TASHI A KOWANE LOKACI
Ali Abubakar Sadiq
Jiya wani kanina ya yi posting cewa "Nan da shekaru biliyan 5 Duniya za ta tashi in ji masana". To, a gaskiyar lamari ba haka abin ya ke ba. Abinda masana Ilimin sararin samaniya ke hasashe shine cewa Rana, wadda ita ce ginshikin wanzuwar Duniya, a yanzu ta kai rabin shekarunta. Wato an haifi wannan Rana tamu kimanin shekaru biliyan 5 da su ka wuce, kuma za ta iya sake kai wasu shekaru biliyan 5 din kafin ta mutu. Masana sun gane haka ne sak**akon nazarin ragowar mak**ashin nukiliya da ke ci a Rana, wato tamkar dai ace ka zuba kwalbar kananzir guda a fitila. Kuma wannan kananzir ya na kai awa goma kafin ya kare. Duk inda ya ci na awa biyar, ka san saura wasu awanni biyar ke nan kafin ya kone.
Sak**akon fahimtar yadda taurari, k**ar halittu a Doron Duniya su ke, to, ana haihuwar su, su balaga su tsufa sannan su mutu. A yanzu Ranar mu na ganiyar balagar ta, nan da wasu biliyoyin shekaru zata tsufa kafin ta mutu. Idan ta mutu, kuma Duniya na nan a wannan lokaci, wajibi ne yayin mutuwar tata su mutu tare da duniyar mu. Domin a lokacin da Rana ta kone mak**ashin ta, za ta yi wata irin bindiga (supernova) da zai watso wuta ta lakume duniyoyi hudu makusantanta (Mercury, Venus, Earth da Mars). Kafin abinda ya rage nata ya dunkulule a tsakiyarta, ta yi wata irin takurewa waje guda wadda ko dai ta haifar da Neutron star, wato dunkulalliyar Rana mara haske ko kuma idan nauyinta ya kai ta zama Black Hole, wato bakar tauraruwa wadda ba a iya gani saboda karfin maganadisunta zai sa ko haske ba zai iya fita daga cikinta ba.
Wannan shine sak**akon nazarin masana yadda taurari irin Rana ke mutuwa a sammai kuma ake hasashen ita ma ranarmu haka zata kare.
To amma mu sani cewa ita duniyar mu, zata iya kaiwa wannan lokaci amma kuma ba lallai ba ne. Domin a yau, idan Allah ya so duniyar nan tamu na iya karewa idan wani daga cikin manyan duwatsun sammai (meteorites) ya fado kan wannan Duniya ta mu, zai iya wargaza ta nan tak
02/04/2026
Tana zaune k**ar yadda ta saba, yazo ya ce, ranki daɗe ga shayin an kawo.
Ta ce: Na gode!
Ya ce: Ranki daɗe wannan shi ne Kofi na uku da na kawo miki amma baki sha ko ɗaya ba!
Ta ce: Saboda bana shan shayi!
Ya ce: Me yasa k**e siya toh?
Ta ce: Menene ruwanka a ciki?
Ya ce: Ina aiki ne a nan wajen, kuma na san ajinmu ɗaya dake a Jami'a. Na san baki taba lura dani ba, amma kullum in ana darasi bani da aiki sai kallonki kuma duk in da kika sanya ƙafarki ina biye dake..!
Ta ce: Duk saboda me kake aikata hakan..!?
Ya ce: Saboda sha'aninki yana bani mamaki......!
Wani lokacin kina dariya ba tare da dalili ba. A wani lokacin kuma sai na ga kin turbune fuska....!
Wannan aikin ina zuwansa ne, kuma ina ƙaunarsa saboda kullum sai kin zo wurin nan, ni kuma ina jin daɗin tozali da ke.
Baki san duk sa'ar da naga wani ko kallon banza ya yi miki a Aji sai mun yi rigima da shi ba...!
Ta ce: Me ka ce....!
Ya ce: Abin da kunnuwanki s**a ji.
Bana samun nutsuwa har sai na kalli fuskarki, sai n biki a baya a baya in kina tafiya. Ki yi haƙuri, Ki yafe mini....!
Ta ce: Akan me ka ke bani haƙuri ne...!?
Ya ce: Saboda ina bin diddiginki ba tare kin sani ba! Kuma kullum da daddare in ki ka zo nan kika zauna sai na koma gefe ina ta kallonki.... Ki yi haƙuri....!
Ta ce: Babu komai maganar ta wuce. Mu dawo kan batun farko da muke tattaunawa...
Ya ce: Ai babu wani batu d muka fara magana akai!
Ta ce: Ba ka tambayi me yasa nake sakawa a kawo mini shayi amma bana sha ba...!?
Ya ce: Ƙwarai da gaske...!
Ta ce: Da gaske bana shan shayi, kaɗai dai in cewa a kawo ne saboda aikinka ne, dole kai zaka kawo, ni kuma ina jin daɗin kallonka... Saboda na ganka kaɗai nake siyan abin da bana buƙata....!
26/02/2026
Ishaq da Shmuel wasu Yahu**dawa ne guda biyu da s**a ɓace a cikin Sahara. Sun gaji sosai ga yunwa ga ƙishirwa, ana haka suna cikin tafiya kawai s**a ga wani ƙauyen Musulmi. Ishaq ya ce wa abokinsa: Mu yi k**ar mu Musulmi ne domin su ba mu abinci da ruwa.” Shmuel ya ya ce masa: “Ni zan faɗi gaskiya, ba zan yi ƙarya ba.” ai kuwa suna isa ƙauyen, aka tambaye su sunayensu. Ishaq ya ce: “Sunana Abdullah.” Abokinsa kuma ya ce: “Sunana Shmuel, kuma ni Baya**hude ne.” Sai shugaban Musulman ya ce: “Ku ba Baya**huden abinci da ruwa. Kai kuma Abdullahi, ka san dai muna watan Ramadan ne. Ka jira zuwa faɗuwar rana sannan mu ci abinci tare.!"
19/02/2026
Ana fa maganar tsuntsun da yafi kowanne girman fuka-fukai ne a duniya.
Tsuntsun Wandering albatross da ke rayuwa a bahar maliya na duniya, yana da tsawon fuka-fukai da s**a kai ƙafa goma sha daya.
Ban da wannan fintinkau din, Wandering albatross na iya shafe tsawon shekaru yana shawagi a sararin samaniya bai sauka a tudu ba.
Akwai wani tsuntsun Wandering albatross da masana kimiya s**a bibiya da ya shafe kilomita kusan dubu tamanin kafin ya sauka a tudu.
17/02/2026
Alhmdlh alhmdlh alhmdlh
Yau Ina zaune a gurin kasuwata inata tunani ya dauremin Kai narasa me kemin Dadi saboda yanayain rayuwa kawai sai naga motoci biyu aciki harda Hilux da ma aikata
Sun nufo inda nake kasuwancina Wani saurayi ya sauko a cikin motar ya karaso gurina yace barka nima na amsa nace masa barka
Yace shin ka ganeni kuwa nace a.a yace haba Zaharadini Ishaq Koda yace haba zaharadini sai kaina ya daure nake mamaki Ina wannan bawan Allah ya sanni
Yace nine safwan Dan gidan alhaji munir Mai gwala gwalai Wanda mukayi aikin kamfani tare
A lokacin nazo Ina bako kanunamin kauna Inda nazo kamfanin bansan kowaba ka daukeni k**ar Dan uwa kome kasamu tare mukece naji dadin Hakan sosai
Wanda Hakan danayi kawai nayi basaja ne Amma har kamfanin shinkafar na mahaifi nane nayi haka domin naga masu tausai a cikin ma aikatanmu domin Koda zamu karawa wani matsayi musan Waye shi kafin lokacin yazo
Yacemin malam zaharadini tabbas bayan nabar kamfani na Dade bana kasar Nan Ina EngIand domin hutawa
Shine yanzu Ina sauka a kasarnan nace dole na kawo Maka ziyara
Yacemin yazomin da albishir masu Dadi inada yacemin
Yanzu haka zai bani
Kawai sai naga takardu ya bani ta farko yacemin wannan gidane a cikin G R A
Yabani kyauta
Takarda ta biyu Kuma takarda mota kirar GLK Benz
Ta uku Kuma takarda machine sabo Wanda zan rinka zagayawa gari yawo
Nayi farin ciki sosai
Sai yacemin ga key din machine din kozan Dan hau naji
Nahau machine Ina bugawa machine ya tashi nima na tashi a barci Ashe mafarki nake
17/02/2026
Sakarai ma fi Sa'a a Duniya.
Wannan lakanin wani bature ne da ake kira Timothy Dexter a Shekarar 1747. Tabbas Dolo ne na Karshe Amma abun mamaki Yana da Sa'a daga Allah na yawan shafarsa, Hakan ya sa ma ya zarce tsararrakin sa a harkar kasuwanci duk da sun fi shi basira.
Akwai ranar da mutane s**a zaulaye shi cewa a yankin west indies ana matukar bukatar littafin Baibul da Kuma safar hannu saboda Sanyi alhalin yankin suna fama da tsakanin Zafi.
Dexter ya samo kudi ya siyo safar hannu guda dubu goma (10,000). Sannan ya siyo Baibul Shima guda dubu goma. Ya Shirya ya hau jirgin ruwa da kayansa ya nufi yankin west indies.
Yana isa Kuma sai Allah ya sa wani jirgi na Yan Kasar Rasha (Russia) ya yi fakin a gabar tekun west indies. Su Kuma yankin Rasha suna fama da tsakanin Sanyi na dusar Kankara. Haba! Ai suna ganin Dole Dexter da dilolin safar hannu a take s**a saye su, Kuma s**a linka masa riba sannan su ka ce bayan wata 6 ya kara kawo mu su. Kun ji sa'ar farko ko? To Kuma abun mamaki baibul-baibul din da s**a saya suma a lokaci guguwar sauyin addinin kiristanci ke kadawa, shi ma a take aka siye su Kuma aka ce ya koma america ya karo wasu.
Dexter ya dawo America Cankas da kudi. Abokan kasuwancin sa sai s**a ji haushin cewa sun masa mugunta Amma ta zama alheri. Sai s**a Kara Shirya masa wani tuggu.
Watarana suna zaune sai s**a ce masa ai yankin Newcastle suna matukar bukatar mak**ashin Coal alhalin a zahirin gaskiya can ne deport din coal. Can ne ake haqo sa a sayar wa Sauran garuruwa. Amma cikin rashin sani Dexter ya kwashe kudinsa duka ya sayi Coal na Pennsylvania ya loda a jiragen ruwa ya nufi Ingila (Newcastle). Abun mamaki maimakon ya yi hasara sai ya tarad da Coal yayi karanci saboda masu hakarsa sun tafi yajin aiki. Kafin ka ce Kobo! Mutane sun siye coal din, Dexter ya samu riba Mai yawa ya dawo gida.
Tabbas Dexter yana da sa'a, Amma dakiki ne na karshe, Amma duk da haka ya na daukar Kansa a matsayin wani philosopher masanin ilmi alhalin ko firamare bai gam
11/02/2026
Ba zan taɓa mantawa da Sani ba. Mun taso tare a Gwale, Kano. Mun yi mafarkin zama manyan ‘yan kasuwa. A lokacin da yake da shekara 25, yana da ƙaramin shago a Kantin Kwari, kuɗi na shiga, mutane na girmama shi, iyayensa na alfahari da shi. Ni da kaina na taɓa cewa, “Sani zai yi nisa.”
Ban san cewa zan zo ina ba da wannan labarin ba.
Komai ya fara ne a hankali. Sabbin abokai, sabbin wurare, sabbin halaye. Ya kan ce min, “Ka kwantar da hankalinka, ni ba ƙaramin yaro bane. Na san iyaka.” Da farko da giya ya fara, Yace don rage damuwa.
Yace kasuwanci yana masa nauyi. Daga baya aka haɗa da ƙwaya. Har yanzu yana cewa komai yana ƙarƙashin ikonsa.
Amma ni na fara ganin canji kafin shi ya gani. Yana jinkirta buɗe shago. Yana saɓa alƙawari. Idonsa ya daina haske k**ar da. Idan na yi masa magana sai ya ce, “Ka bar ni mana, ka daina min wa’azi.”
Shekara ɗaya kacal ta isa komai ya fara rushewa. Bashinsa ya taru. Ya fara sayar da kayansa a ɓoye. Ya fara guje wa mutane saboda kunya. Ranar da na je gidansu da safe, mahaifiyarsa ta riƙe hannuna tana kuka. Ta ce, “Don Allah ka taimake shi, bana gane ɗana yanzu.”
Na shiga ɗakinsa. Ya zauna a gefen gado, idonsa ja, jikinsa na rawa. Na ce masa, “Sani, ka tsaya tun kafin lokaci ya ƙure.” Ya kalle ni cikin ido, ya ce kalma guda da har yau tana binsa… tana binsa… tana binsa:
“Da na sani…”
Amma gaskiyar ita ce, ya riga ya fara rasa komai.
A shekaru 28 ya rasa shago. A Shekaru 29 muka kai shi asibitin Murtala sak**akon haɗa giya da ƙwaya. Na tsaya a wajen ɗakin jinya ina tunanin yadda komai ya fara da abin da ya yi k**a da ba komai ba.
Yau yana raye. Amma ba rayuwar da ya taɓa mafarki ba. Kuma ni ina rayuwa da darasi mai ƙarfi mai taɓa zuciya.
Idan kana da shekaru 25 zuwa sama, ka saurare ni sosai. Wannan shekarun ba na wasa bane. Abin da ka bari ya shiga rayuwarka yau, shi ne zai mallaki makomarka gobe.
Shaye-shaye ba ya zuwa da sunan hallaka; yana zuwa da sunan shaƙatawa. Amma a hankali suna sace maka kuɗi, lokaci, mutunci, har ma da
06/02/2026
Ban san cewa soyayya na iya juyawa ta zama yaƙi ba, sai da ya faru a kaina.
Labari ne a kan yadda tsohuwar masoyiyarka za ta dawo babbar mai adawa da kai a rayuwa.
Daga group assignment, muka shaƙu da juna.
Alawiyya ta fito daga wani babban ahalin Faila ne.
Soyayya ta haɗa mu, ba siyasa ba. Saboda haka, mun lula izuwa gajimare ba tare da ɗaya ya tambayi aƙidar ɗaya ba.
Muna tsaka da taku a campus, wani ɗan Alhajin Kaduna ya hallara. Ya baza capacity, ya ƙwace ta.
Na ji ba daɗi. Ƙarfin addu'a ne ya sa ban faɗi dukkan courses da na ɗauka wannan semester ba.
Amma dai CGPA ya sauƙa.
Har bayan ɓaɓewarmu kuma, ƴan'uwanta mata s**an ƙira ni, mu gaisa.
Musamman ma wata ƙanwarta mai suna Mufida. Yarinya mai hankali.
Da na ga abin da ya haɗa ya raba, wata rana da Mufida ta ƙira, sai na daure na zayyana mata gaskiyar halin da ake ciki.
Ta yi ajiyar zuciya ta ce:
“Lallai Sayyada ba ta kyauta maka ba.”
Ta yi min adu'ar Allah ya zaɓa min mafi alkhairi.
Bayan sati guda, ta ƙara ƙira:
“Yayana, yaushe za ka zo Nassarawa?”
Na ce mata, ba na tunanin zan taɓa zuwa saboda igiyar da za ta ja ni zuwa Nassarawa ta tsinke.
Ta ce, a’a.
"Zumuncin da Allah ya haɗa bai k**ata ya rabu ba. Ka shirya ka zo. Ni kuma zan shirya maka tarba ta musamman.”
Bayan kwana biyu, ta ƙara ƙira ta maimaita buƙata guda.
A ƙarshe dai na yanke shawarar zuwa Nassarawa.
Ko ba komai zan ziyarci dangin mahaifina da ke a can. Da ma suna ƙorafin ba ma ziyartarsu.
Daga nan, Mufida ta samu damar ƙirana ba dare ba rana. A gaban kowa da kowa. Abin ka da ƙaramar yarinya.
Wata rana da sassafe muna waya da Mufida, Alawiyya ta tsinkayi muryata ta window. Da yake ɗakunan kwanansu jere suke.
Sai ta faɗa ɗakin Mufida:
“Ke kuma da ɗan Izala k**e soyayya?”
“Ɗan Izala ba Musulmi ba ne, Auntie?”
“Amma ai ba sa ganin girman Shehu. Wato kina so ki zubar mana da mutuncin family ko?”
“Shehu ai kogi ne. Zai fahimta ne idan ina tare da shi.”
Ko da Alawiyya ta ga wannan hanya ba ta ɓulle ba, sai ta canza salo:
“
02/02/2026
Kar Mu Cire Tsammani.
Domin mu gane halin da muke ciki yanzu, bari mu yi tunanin cewa an haife ka ne a shekarar 1900.
Lokacin da ka cika shekara 14, sai aka fara Yaƙin Duniya na Ɗaya. Aka gama yaƙin kana ɗan shekara 18, inda mutane miliyan 22 s**a rasa rayukansu.
A cikin shekarar da aka gama yaƙin, sai wata cutar mashasshara (Spanish Flu) ta ɓalle a duniya har sai da ka kai shekara 20. A shekaru biyun nan kawai, mutane miliyan 50 s**a mutu.
Kana ɗan shekara 29, sai aka shiga Babban Talauci (Great Depression) na duniya. Rashin aikin yi ya addabi kowa, tattalin arziki ya durƙushe. Wannan wahalar ta ja har sai da ka kai shekara 33.
Kuna fitowa daga wannan, kana ɗan shekara 39, sai aka fara Yaƙin Duniya na Biyu.
Tsakanin shekarunka 39 zuwa 45, mutane miliyan 75 s**a mutu a yaƙi, ciki har da mutane miliyan shida da aka kashe a kisan kiyashin Holocaust.
Kana ɗan shekara 52, aka fara Yaƙin Koriya, inda mutane miliyan biyar s**a ƙara mutuwa.
Lokacin da ka kai shekara 64, aka shiga Yaƙin Vietnam wanda aka kwashe shekaru ana yi, mutane miliyan huɗu s**a mutu.
Sa’adda kake kusan shekara 62, duniya ta kusa tashi baki ɗaya saboda rikicin mak**an Nukiliya na Kuba, amma Allah ya sa aka shawo kan lamarin.
A lokacin da ka cika shekara 75, sannan aka gama yaƙin Vietnam.
Ka yi tunani fa: Mutanen da aka haifa a shekarar 1900, ta yaya s**a iya jure duk wannan wahalar? Wani matashi a shekarar 1985 zai iya ganin kakanunsa (masu shekara 85) k**ar ba su san me ake kira wahala ba, alhalin su ne s**a ga idon kowane irin bala’i amma s**a tsira.
Halin da muke ciki yanzu ma darasi ne. Mu kwantar da hankalinmu, mu taimaki juna, kuma mu sani cewa za mu tsallake wannan ma. A tarihin duniya, babu guguwar da take dawwama. Komai tsananin dare, gari zai waye.
27/01/2026
Libya Ce Kasa Ta Farko Da Mota Ta Fara Shiga A Tsakanin Kasashen Larabawa
Shin kun san cewa ƙasar Larabawa ta farko da aka fara shigar da mota zuwa ƙasarta ita ce Libya?. Tun a shekarun 1890, wani mutum mai suna Abdullah Shaaban Al Zowaree ya kai motar Welleyes zuwa Libya.
Mota ce mai karfin doki 3 da wani kamfanin kera motoci na Italiya mallakar Giovanni Battista Ceirano, Emanuele di Bricherasio, Attilio Calligaris, Pietro Fenoglio, da Cesare Goria Gatti ya kera.
A da, mutane da yawa sun yi imanin cewa mutumin da aka nuna a cikin wannan motar Abdullah Sha'ban Al Zowaree ne da motarsa ta (Welleyes Motor), amma a zahiri, ɗansa ne, Sultan Bin Sha'ban, a cikin mota kirarFiat Zero a shekarar 1912.
Hoto📷 Sultan Bin Sha'ban a cikin mota kirar Fiat 1912
♥️♥️
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Abuja