Masarautan gombe

Masarautan gombe

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Masarautan gombe, Health/Beauty, Gomben Emirates Place, Abuja.

Photos from Masarautan gombe's post 18/09/2025

GIWA uban shamaki uban sallama

Allah yaja da ran sarki ✊

11/09/2025

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ZANCEN ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA SALIHAN BAYINSA A ALJANNAH:

Abu Sa'eed Al Khudriy (R.T.A) yace Manzon Allah (S.A.W) yace :

"Allah madaukakin Sarki zaice wa 'yan Aljannah : "YA KU 'YAN ALJANNAH!".

Zasu ce "Labbaika (Amsawarka) Ya Ubangiji!! kuma dukkan arziki da dacewa suna gareka!!".

Sai yace musu "Shin kun yarda? (da sakamakon da aka baku).

Sai s**e "Meke garemu da bazamu yarda ba! Alhali gashi ka bamu abinda baka ba ma kowa ba, daga cikin halittunka!".

Sai yace "ZAN BAKU ABINDA YAFI WANNAN".

Sai s**e "To wanne bau ne kuwa yafi wannan?".

Sai yace musu "NA BAKU YARDATA, BAZAN TA'BA YIN FUSHI DAKU BA, HAR ABADA".

(Hadisi na 6549 cikin Sahihul Bukhariy).

Allah mai girma nake roko ya sanyani daku da iyayenmu da 'yan uwa da iyalanmu baki daya cikin wadanda zasuyi wannan zancen da Allah (Jalla jalaluhu) Bijahi Rasulillahi (S.A.W)🀲🀲🀲

Photos from Masarautan gombe's post 02/08/2025

Hoton Sada Zumunci Tsakanin Mai Martaba Sarkin Gombe da Prof. Maqari

Allah ya taimaki sarki ✊

10/01/2025

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM πŸ™πŸ™πŸ™

NASIHA CE...

"Sayyuduna Rasulillahi (S.A.W) Yace: β€œKu tausayawa marayu (Hakan zai sa) ALLAH Madaukakin Sarki Ya tausaya mana. Ku tuba ya zuwa ga ALLAH madaukakin Sarki daga zunubbanku.

Kuma ku daga Hannuwanku da addu’o’i A lokutan sallolinku, domin (lokutan salloli) sune sa’o’in da s**a fi falala, ALLAH Madaukakin Sarki zai dube ku da Rahamarsa"

Ya Ubangijin Annabi Muhammadu (S.A.W) Ka faranta Mana Rayukanmu nan Duniya kuma ka faranta mana ranar Al_Qiyama Don Darajar Sayyuduna Rasulillahi (S.A.W).

Ina Muku Fatan Alheri Da Kuma Barka Da Jumma'a.πŸ™πŸ™πŸ™

Photos from Masarautan gombe's post 20/12/2024

Ran sarki ya DadeπŸ”₯πŸ‘‘βœŠ

11/12/2024

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

NEMAN ALBARKAR MA'AIKI (S.A.W)

An ruwaito daga Safiyyah bintu Najdah (ra) cewa KHALID BN WALID (ra) ya kasance yana da wasu gashi daga cikin sumar Manzon Allah (S.A.W) wadanda ya sanya acikin hularsa. Duk lokacin da zai fita wajen yaki yakan sanya wannan hular akansa.

Rannan sai hular ta fadi awajen wani daga cikin Yakokinsa. Sai KHALID din ya sanya aka koma aka ci gaba da yakin har sai da aka dauko wannan hular. Da sauran Sahabbai s**a tuhumeshi akan dalilin da yasa yayi Umurnin akoma wannan yakin, Sai Khalid yace musu "ACIKINTA AKWAI SUMAR MANZON ALLAH (SAWW) NE. SHI YASA NAYI KOKARI NA KOMA NA DAUKOTA. SABODA KAR TA FADA HANNUN KAFIRAI, NI KUMA IN RASA ALBARKARTA".

- Aduba cikin ASH-SHIFA ta Alqadhiy Iyaadh (rah) juzu'i na farko shafi na 619.

Wannan hadisin Hujjah ce akan halaccin neman albarkar MA'AIKI (S.A.W). Da kuma halaccin rikon wani abu wanda yake da Alaqah dashi (S.A.W) domin neman albarkarsa.

Kwanakin baya ma mun kawo wani hadisi Sahihi wanda ya nuna cewar Sahabbai s**an tsoma gashin Manzon Allah (S.A.W) acikin ruwa, sannan su sha ruwan domin neman waraka daga cututtuka.

Allah shi bamu albarkarsa (S.A.W).

Photos from Masarautan gombe's post 07/12/2024

Maje jumma'a ✊

Photos from Masarautan gombe's post 23/11/2024

Hotunan sallan jumma'a daga fadan mai martaba sarkin Gombe alhj (Dr) Abubakar shehu Abubakar iii CFR

Allah yaja zamanin sarki✊✊

22/11/2024

Magajin gidan bubayero ✊

17/11/2024

Allah ya qarawa sarki yawan nasara ✊

13/11/2024

Ameen na annabiπŸ€²βœŠπŸ‘‘

10/11/2024

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM πŸ™πŸ™πŸ™

NASIHA CE:

SADAKA:

Manzon Allah (S.A.W) yace da Mu'az cikin hadithin da Tirmizi ya ruwaito mai tsawo..

"Kaga ita SADAKA tana k'one zunubai kamar yanda ruwa yake kashe wuta"...

Note:
Ya bayin Allah, babu Sadakan da take tauye dukiya sedai ta habaka ta, sannan ana yin sadaka da abinda ake so. Wanda yake da amfani.

Allah Ta'ala ya bamu iko, tare da kyakkyawan Niyya Bijahi Rasulillahi (S.A.W).πŸ™πŸ™πŸ™

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Gomben Emirates Place
Abuja
109064