Assalafy doguru
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Assalafy doguru, Health/Beauty, Mashi/katsina, Nigeria, Abuja.
With Ibraheem Mu'az Majia – I just got recognized as one of their top fans!
10/07/2026
TSARABAR SAFIYA🌸
An Karɓo daga Anas bn Malik 🌷(RD)🌷 ya ruwaito cewa: Wani mutum ya tambayi Manzon Allah 💓{ﷺ}💓 ya ce: "Ya Rasulallahi! Ina mahaifina yake? Sai Annabi {ﷺ} ya ce: "Yana cikin wuta.🔥"Yayin Da mutumin ya juya zai tafi, sai Annabi {ﷺ} ya kira shi ya ce: "Lallai mahaifina da mahaifinka suna cikin wuta.🔥 (Sahih Muslim)
[ƘARIN HASKE]
Bayanin Malaman Salaf (ba tare da tawili ba)
Malaman Ahlus-Sunnah na Salaf sun karɓi hadisin kamar yadda ya zo ba tare da karkatar da ma'anarsa ba.
1. Yahya ibn Sharaf al-Nawawi
Imam An-Nawawi ya ce a cikin sharhinsa na Sahih Muslim: Wannan hadisi hujja ce cewa wanda ya mutu a kan kafirci yana cikin wuta, kuma kusancin mutum da Annabi ba ya amfanar da shi idan bai mutu a kan imani ba.
Ya kuma bayyana cewa iyayen Annabi {ﷺ} sun mutu kafin aiko shi, kuma sun mutu ne a kan addinin mutanensu.
2. Ibn Taymiyyah Ya ce: Hadisin Sahih Muslim ingantacce ne, kuma wajibi ne a gaskata abin da Annabi{ﷺ}ya faɗa ba tare da ƙaryata shi ko karkatar da ma'anarsa ba. (Majmū‘ al-Fatāwā)
3. Ibn al-Qayyim Ya ce: Wanda saƙon Annabi bai riske shi ba, hukuncinsa yana ƙarƙashin adalcin Allah. Amma wannan hadisi na musamman ya zo da bayani daga Annabi {ﷺ} game da mahaifinsa, saboda haka ana gaskata shi kamar yadda yake. (Ṭarīq al-Hijratayn)
4. Ibn Kathir Ya ambaci wannan hadisi a cikin tafsirinsa lokacin bayanin ayoyin da s**a shafi mushrikai, yana nuna cewa: Dangantaka da Annabi ba ta wadatar idan babu tauhidi.
5. (Muhammad Nasiruddin al-Albani) Sheikh Al-Albani ya tabbatar da ingancin hadisin, kuma ya ce: Bai halatta a ƙi wannan hadisi ko a yi masa tawili saboda yana cikin Sahih Muslim.
Abin da Salaf s**a tsaya a kai: Sun tabbatar da ingancin hadisin. Sun gaskata lafazinsa kamar yadda ya zo. Ba su ƙaryata shi saboda tausayin Annabi {ﷺ} ba. Sun yi imani cewa Allah ba Ya zaluntar kowa, kuma hukuncinsa cikakken adalci ne. Ba su karkatar da ma'anar lafazin hadisin idan ba tare da hujja ba. Allah ne Mafi sani.
10/07/2026
"A Sujjada Ake Yi Wa Iyaye Addu'a, Ba a Status Ba" — Ali Rabi'u Ali Ya Aike da Saƙo Mai Taɓa Zuciya
Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Rabi'u Ali, ya yi kira ga al'umma da su fi mayar da hankali wajen yi wa iyayensu addu'a a cikin sujjada, maimakon takaita hakan ga wallafawa a kafafen sada zumunta.
A cewarsa: "A sujjada ake yi wa iyaye addu'a, ba a status ba, domin haihuwarku s**a yi, ba downloading ɗinku s**a yi ba."
Kalaman nasa sun ja hankalin mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda wasu s**a yaba da saƙon, suna mai cewa yana tunatar da muhimmancin girmama iyaye da yi musu addu'a a asirce.
Kana ganin ya fi muhimmanci a yi wa iyaye addu'a a boye, ko kuma wallafawa da yi musu fatan alheri a kafafen sada zumunta ma yana da amfani?
10/07/2026
Dole yaro yayi biyayya ga ubangidansa kafin yayi nasara a rayuwa,
Mu matsalarmu yanxu rashin hakuri yaro so yake kawai ya buda ido yagansa a matsayin ubangidansa yana sa kalar shaddar ubangidansa, takalminsa, hularsa, motarsa, gidansa da sauransu.
Amma da zaka ji shekarun gwagwarmayarsa da zaka gane sun ci kwakwa ba kadan ba.
Kaima sai kayi haquri ka ci taka kwakwar ko, kafin ka zama wani.
Allah ya albarkaci nemanmu
10/07/2026
Janar Christopher Musa ya bayyana cewa gwamnati ta ba wa dakarun tsaro cikakken ikon daukar mataki cikin gaggawa a kan 'yan ta'adda, yana mai jaddada cewa duk wani jami'in da ya ki kashe dan bindiga ko dan ta'adda da sunan jiran umarni, za a dauke shi a matsayin mai goyon baya ga masu aikata laifuka.
Ministan ya fadi haka ne a jihar Sokoto yayin kaddamar da sabbin motocin yaki da kayan tsaro guda 62 da gwamnatin jihar ta saya domin yaki da ta'addanci.
10/07/2026
Allah yajikan malam da rahamaq😭😭😭
24/06/2026
Su karantar damu su koya mana tarbiyya, idan aikin addini ya taso suyi da kudin su lokacin su da karfin su.
Tabbas a wannan zamani malamai sun yi ma sauran al'umma nisa.
Allah kasa a mizani Ameen
19/06/2026
Dubban al'umma sun yiwa Ɗan takarar Gwamna a jam'iyyar ADC Sanata Ahmed Babba Kaita kyakkyawar tarba daga Kano zuwa Katsina
Ɗaruruwan al'umma sun yi kyakkyawar tarba ga Ɗan takarar Gwamna a jam'iyyar ADC Sanata Ahmed Babba Kaita bayan tabbatar da shi a matsayin ɗan takarar Gwamna a Jam'iyyar.
Masoya ɗan takarar Gwamnan da Jam'iyyar ADC daga dukkanin lungu da saƙo na jihar Katsina s**a yi dafifi domin nuna soyayya da ƙauna ga ɗan takarar Gwamna a jam'iyyar ADC tun daga iyakar Katsina da Kano har zuwa gidansa dake cikin birnin Katsina.
Al'umma da yawa ne s**a isa iyakar Katsina da Kano tare da tarbo ɗan takarar zuwa Mahaifar sa ta Kankiya, tare da gaishe da Kankiyan Katsina Hakimin Kankiya Alhaji Musa Hassan Sada zuwa Katsina.
Al'umma sun ɗaga fastoci da yafa kyallaye da tare da faɗin kalmomi da yawa da s**a haɗa da "Katsina sai Babba" da "Katsina Falle ɗaya ce" da "2027 kaine Gwamna" da sauran su.
A dukkanin garuruwa da ya wuce daga iyakar Katsina da Kano daya haɗa da Gidan Mutum ɗaya da ƙyafau da Kankiya da Charanci da Tafkin Al'umma da Lambar Rimi da Abukur zuwa Katsina, an ga yadda al'umma ke fitowa daga gidajen su suna fatan alheri da taya murna bisa tikitin takarar kujerar Gwamna da aka bashi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Abuja