Kula da kai
Muna nuna yadda akeyin magani da shawara
07/11/2025
These are some sexual benefits of scent leaves.
1. It fight infections_ It has anti fungal and anti bacteria properties that helps to prevent urinary tracts infections that can affect performance.
2. There are natural compounds in scent leaves that help to stimulate sexual desires and boost performance.
3. Scent leaves helps to boost the sexual hormones. That's testosterone and oestrogen and other reproductive hormones that are essential for sexual health.
4. It improves blood circulation. It enhances blood flow to the p***s, which supports stronger and longer erections
5. It reduces stress and fatigue. The leaves have calming properties which helps to lower stress and improve sexual mood and stamina.
6. It increases s***m quality. Using scent leaves often can help improve s***m count, motility and over all fertility.
You can boil the leaves and drink 100 ml twice daily or you can blend and drink the juice one glass daily.
Stay healthy🙏🏻
29/10/2025
Da yawa daga cikinmu Muna fama da matsala irin na dankarewar gashi a yayin da mukazo wankewa😥 to matso kusa ga warwarewar matsalar ki yazo ki Sami GANYEN DALBEJIYA ki blending dinta inma babu blender ki Sami turminki da tabarya ki kirba abinki sai ki tace ruwan 👇 yawwa sai ki shafa a fatar kanki ko Ina ya samu sai ki rufe da Leda k**ar yadda k**eyi idan Kinsa relaxer ki barshi yayi 30 - 40 minutes sai ki wanke ki shafa Oil ko duk Wani Mai da k**e amfani dashi zai magance miki Amosanin Kai wato dandruff.
zaisa gashinki yayi Baki
da sheki💃💃
anasan kiyi haka duk bayan 1 month
ku sanbadamun like hiliss nidin takuce 😄
19/10/2025
Allura tana da illoli masu hatsarin gaske
Allura ta na iya zama sanadiyyar samun naƙasa ko rasa ƙafa
Allura tana iya zama sanadiyyar rasa wani sashen jiki, ko matsananciyar jinya tare da kashe miliyoyin kuɗi
———————————
Saboda haka, ku daina bari ana muku allura har sai ƙwararren ma’aikacin lafiya tare da izinin likita daga assibiti
19/10/2025
.............................................
Abinda Ya Kamata Ku Sani Game Da GENOTYPE
Wannan rubutu yana ɗauke da muhimman bayanai da za su taimaka wa kowanne mutum mai niyyar yin aure mace ko namiji. Duk da cewa rubutun yana da ɗan tsawo, Amma yana da amfani sosai idan ka karanta shi har ƙarshe. Mintuna kaɗan ne kawai zaka ka ɗauka ka karanta amma fa’idarsa na iya amfanarka na har abada. In sha Allah
••••••••••••••••••••••••••••••••••••••
KUYI FOLLOWING DAN SAMUN WASU RUBUTUKAN GAME DA LAFIYAR KU
👇👇👇👇
fateema sani
𝗠𝗘 𝗔𝗞𝗘 𝗡𝗨𝗙𝗜 𝗗𝗔 𝗚𝗘𝗡𝗢𝗧𝗬𝗣𝗘
Genotype shi ne tsarin kwayoyin halitta da ke bayyana irin gado ko halayen da mutum ya samo daga iyayensa. Wannan tsari yana bayyana nau’in jini da kuma yadda jikin mutum ke amsa wasu cututtuka ko yanayi. Genotype yana ƙunshe da abubuwan da ake kira genes, waɗanda suke cikin chromosomes, wanda su kuma suke cikin DNA.
Kowane mutum yana gadar chromosomes 23 daga mahaifinsa da kuma 23 daga mahaifiyarsa, Gaba daya 46 kenan. A cikin wannan tsarin akwai ɗaruruwan genes da ke ayyana halaye daban-daban na mutum k**ar launin ido, nau’in fata, gashin kai, har ma da nau’in jini da cututtuka da mutum zai iya ɗauka.
𝗠𝗔𝗜 𝗬𝗔𝗦𝗔 𝗦𝗔𝗡𝗜𝗡 𝗚𝗘𝗡𝗢𝗧𝗬𝗣𝗘 𝗞𝗔𝗙𝗜𝗡 𝗔𝗨𝗥𝗘 𝗬𝗔𝗞𝗘 𝗗𝗔 𝗠𝗨𝗛𝗜𝗠𝗠𝗔𝗡𝗖𝗜 ??
MU sani, jin dadin aure ba wai kawai iya soyayya bace, akwai lafiyar irin yayan da za'a haifa ta silar wannan auren.
Akwai wasu genotypes da ba su dace su haɗu ba saboda haɗuwarsu na iya haifar da haihuwar yara masu larura k**ar ciwon sickle cell. Ciwon Sickler yana da hadari sosai, yana da zafi sosai, yana ragewa ma'aurata jin dadi da zaman lafiya, uwa uba yana jawa yaran da za'a haifa radadi da ciwon da duk ya wuce yadda zaka iya kwatantashi da bakin ka
Saboda haka, sanin genotype kafin aure yana da matuƙar mahimmanci domin yana taimakawa wajen aurar wanda zaku haifi yara ba tare da wannan ciwon ba wato zak
12/10/2025
✅ MENENE TSUTSAR CIKI?
Tsutsar ciki cuta ce da ke faruwa idan ƙwayoyin cuta masu k**a da tsutsa s**a shiga hanjin mutum, suna cin abinci daga cikin jikin mutum.
Wannan na iya faruwa ga yara da manya.
IRIN TSUTSAR CIKI DA AKE DASU:
1. Roundworm (Ascaris lumbricoides)
Tsutsa mai k**a da igiya, tana rayuwa a cikin hanji.
Tana iya sa ciki ya kumbura, amai, rashin cin abinci
2. Hookworm (Ancylostoma/Necator)
Tana shiga jiki ta ƙafar mutum idan ya taka ƙasa ba takalmi.
Tana shan jini a hanji — tana iya haifar da ƙarancin jini (anaemia).
3. Tapeworm (Taenia species)
Tsutsa mai k**a da ribbon, tana girma sosai.
Tana iya sa mutum rage nauyi, jin yunwa ko amai.
4. Pinworm (Enterobius vermicularis)
Alamarta ita ce ƙaiƙayi a dubura, musamman da daddare.
ALAMOMIN TSUTSAR CIKI:
Ciwon ciki ko kumburin ciki
Rashin ci ko yawan ci amma babu nauyi ko kiba
Yawan amai
Ciki yana yin ƙara
Fitar tsutsa a bayan gida
Kaiƙayi a dubura (musamman da daddare)
Rashin kuzari, gajiya, ko ƙarancin jini
MAGANIN TSUTSAR CIKI:
🔹 Manyan magunguna da ake amfani da su:
1. Albendazole (400mg) — kwaya ɗaya kawai ana sha sau ɗaya.
Ga yara: 200mg idan ƙasa da shekara 2–5.
Ana iya maimaita bayan wata 6 domin kariya.
2. Mebendazole (500mg) — kwaya ɗaya sau ɗaya, ko 100mg sau biyu a rana na kwana 3.
3. Pyrantel pamoate ana amfani da shi musamman ga yara.
Akula mai ciki bata shan maganin tsusar ciki sai bisa umarnin likita.
08/10/2025
08/10/2025
Daidaitacciyar tsaiwa muhimmin lamari ne ga ɗorewar lafiyar jiki. A duk lokacin da wata matsala ta faru a ƙasusuwa, tsokoki, tantanai ko kuma jijiyoyin laka tsaiwar gangan jiki na iya tawaya hakan zai sa mutum ya gaza yin daidaitacciyar tsaiwa.
Ko da babu ciwo a jiki, idan ka lura tsaiwarka ta sauya to akwai buƙatar ganin likitan fisiyo domin gano matsalar tun da wuri kuma daga tushe domin magance ta.
© Physiotherapy Hausa
06/10/2025
Wanka da soso yana kashe fata
Kar kuyi wanka da tsakar rana, wanka da rana yana saka ciwon kai da kasalar jiki.
Lokuttan wanka:
1. Wanka da safe
2. Wanka da dare
So biyu ake wanka a kowace rana ✅
Bayan haka
Wanka da “soson buhu” yana lalata fatar jiki, kuma yana sanya fatar jiki yin baƙi musamman idan sabon soso ne
Ba’a wanke jiki da soso, sai dai ayi amfani da soso wurin wanke tafin ƙafa 🦶
Gangar jiki baya buƙatar wanka da soso, iya sabulu ya wadatar 🧼
———————————
Ba’a wanka da “Klin” ko “Omo”
Sinadaran dake acikin “Klin” da “Omo” suna saka fatar jiki ƙaiƙayi idan akayi wanka dasu, hakazalika suna ƙona fatar jiki.
⚠️ Idan kana fama da matsalolin fata, yanada kyau kaje assibiti domin samun ingantaccen magani da kulawa 📌
05/10/2025
ABUBUWAN DA SUKE DA TASIRI SOSAI AKAN HAIHUWAR MACE (FERTILITY)
🌸 Shekara (Age):
Shekaru na mace suna da matuƙar tasiri akan haihuwa. Yayin da mace ke girma, ƙwayoyin ɗa (eggs) suna raguwa duka a inganci da yawa.
🌸 Damuwa da baƙin ciki (Stress & Depression):
Na iya shafar hormones da ke kula da haihuwa.
🌸 Shan taba (Smoking):
Baya ga sauran haɗarurruka, yana sa mahaifar mace ta tsufa da wuri, kuma ga maza yana rage ƙwayoyin maniyyi (s***m).
🌸 Shan barasa (Alcohol):
Ko da ƙaramin adadi na iya jawo matsalar haihuwa ga maza da mata.
🌸 Kamuwa da cuta (Infections):
Cututtukan da ake ɗauka ta jima’i (STIs) na iya jawo matsalar haihuwa ga duka maza da mata.
🌸 Kiba ko rama da motsa jiki (Weight & Exercise):
Mata masu kiba fiye da kima (10–15% sama da al’ada) ko kuma rama fiye da kima (10–15% ƙasa da al’ada) na iya fuskantar matsalar hormones da ke shafar haihuwa.
🌸 Abubuwan muhalli (Environmental factors):
Wasu sinadarai, radiation, da zafi mai yawa na iya shafar haihuwa ga maza da mata.
👉 Don ƙarin bayani, ki tuntuɓi ƙwararren likitan kiwon lafiya.
05/10/2025
Dalilin Da Yasa Wanka Da Ruwa Mai zafi Ke Rage Yawan Maniyyi (S***m).
_______________________________
★Yana Da Kyau ka Karanta Har Karshe★
_______________________________
A jiya na ambaci cewa "YAWAN wanka da RUWAN DUMI yana rage yawan maniyyi" amma mutane da yawa sun dau hakan k**ar wasa ne wasu ma karyatawa su kayi kai tsaye amma yau zan bada dalili na na fadar haka.
Kafin na bada dalilin, zan so ku fahimci cewa, ruwan dumin sai ya kasance Mai zafi hakan ke faruwa.
Idan dai ba ka iya wanka da ruwan dumi da bai da zafi sosai ba to kaima hakan na faruwa da kai.
_______________________________
GA DALILAN DA S**A SA NA FADI HAKA
1. Gwaje-gwajen kimiyya ya tabbatar da cewa yan maraina (testicles) suna buƙatar zama ƙasa da zafin jiki domin su samar da maniyyi yadda ya k**ata (kimanin 34–35°C). Misali, Idan zafin jiki ya kasance 36.5°C to dole yanayin zafin yan maraina ya kasance kasa da haka dan samar da wadataccen maniyyi.
2. Idan kana yin wanka da ruwan dumi mai zafi, kuma kana zubawa har a kan yan maraina to zafin yan marainan (testicles) zai zamto daidai da na jikin ka. Hakan zai sa ƙwayoyin da ke samar da s***m (s***matogenic cells) suna lalacewa ko suna rage aikin samar da kwayar maniyyi (s***m).
3. Idan ana yin hakan kullum, yana iya rage yawan maniyyi (s***m count) da yanayin motsin sa (motility) na watanni kafin ya dawo daidai.
4. Idan aka daɗe ana aikata hakan, yana iya shafar damar samun ciki, musamman idan ma’aurata suna da wasu ƙananan matsalolin a gefe guda.
______________________________________
ABIN LURA:
Akwai bambanci tsakanin S***M da SEMEN ko SEMINAL FLUID.
S***M shine kwayar halittar da ke samar ciki. SEMINAL FLUID kuma shine ruwan da ke taimakawa s***m wajen ninkaya (swimming) zuwa ga kwai.
Dan kana fitar da ruwan maniyyi sosai ba shine yake nufin kana da wadataccen kwayoyin maniyyi ba.
Sannan, A Nijeriya, kashi 30 zuwa 50% na matsalar rashin haihuwa daga maza ne.
A wani binciken da akayi ma a Ibada
04/10/2025
“Underwear” yana nufin gajeren wando ƙarami wanda maza da mata ke amfani dashi domin kare mutunci.
Yanada kyau duk bayan 12 hours mace ta wanke ko changer “underwear”
Namiji duk bayan 48 hours.
Hakazalika yanada kyau sosai duk bayan watanni biyu ka changer sabon “underwear”
ILLOLIN RASHIN TSAFTAR UNDERWEAR:
1. Ana kamuwa da ƙwayoyin cutar (bacteria ko fungal) wanda yana iya janyo cutar sanyi (yeast infection ko urinary track infection) da sauransu
2. Rashin wanke underwear yana janyo warin jiki da ƙaiƙayi wanda zai iya hana mutum zama acikin aminci
Bayan haka;
Yanada kyau idan za’a shiga bacci a tabbatar an cire “underwear” musamman irin wanda yake matse mutum sosai.
Bacci da matsatstsen “underwear” yana hana iska ratsa jiki sosai, wanda hakan yana iya janyo matsaloli k**arsu;
1. Scrotal temperature: zafin yayan maraina
2. Optimal s***m production: yana tauye ƙwayoyin halittar maniyi
3. Restriction of blood flow: yana hana zagayawar jini, wanda hakan yana iya haifar da kunburin yayan maraina
4. Scrotal pain: hakazalika bacci da matsatstsen underwear, yana janyo ciwon yayan maraina.
Saboda haka yanada kyau a duk lokacin da zaku shiga bacci, ku tabbatar kun saka wando wanda iska ke zagayawa.
⚠️ Maza, ku bar amfani da underwear ɗaya har na tsawon shekaru. Zaka samu wani yana amfani da underwear ɗaya tun lokacin yana secondary school 🥲
✍️fateema sani
04/10/2025
SHIN NAMIJI MAI ƘARAMIN SPƐRM COUNT ZAI IYA SA MACE CIKI?
Eh, zai yiwu namiji da yake da ƙarancin adadin maniyyi (low s***m count) ya iya sa mace ciki, kodayake damar hakan tana raguwa idan aka kwatanta da na al’ada.
Ƙarancin Maniyyi (Low S***m Count)
Ana kiran wannan matsala da Oligos***mia, wato yanayi inda namiji yake da ƙasa da milion 15 na maniyyi a cikin kowanne millilita na maniyyi (semen).
Damar Samun Ciki (Chances of Impregnation)
Damar samun ciki daga namiji mai ƙarancin maniyyi na dogara ne akan wasu abubuwa:
1. Adadin maniyyi (S***m count):
Idan adadin ya yi ƙasa sosai, damar samun ciki tana ƙara raguwa.
2. Motsin maniyyi (S***m motility):
Duk da ƙarancin adadi, idan maniyyi suna iya yin tafiya da kyau, suna iya isa ga kwai su yi haduwa da shi.
3. Siffar maniyyi (S***m morphology):
Tsarin siffa da ginin maniyyi yana da tasiri wajen iya shiga cikin kwai.
4. Shekaru da haihuwar mace (Woman’s age and fertility):
Shekaru da lafiyar haihuwar mace suma suna taka rawa wajen yuwuwar samun ciki.
✍️ A takaice: Namiji mai ƙarancin maniyyi na iya sa mace ciki, amma dama ta fi ƙasa idan aka kwatanta da wanda yake da al’ada.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Abuja