Musa Abdu Shehu
Army base abuja
29/12/2025
Manyan Kalmomin Likitanci 25 da ya dace kowa ya sani da Hausa
✅Benign: Ba cutar daji ba (ba kansa ba)
✅Malignant: Cutar daji (kansa)
✅Anti-inflammatory: Magani da ke rage kumburi, zafi da radadi (misali ibuprofen, naproxen)
✅Body Mass Index (BMI): Auna kiba ta jiki bisa tsayi da nauyi
✅Biopsy: Daukar wani sashen nama domin gwaji
✅Hypotension: Hawan jini ya yi kasa
✅Hypertension: Hawan jini ya yi yawa
✅Lesion: Rauni, ciwo ko yanka a jiki
✅Non-invasive: Bincike/magani ba tare da shiga cikin jiki da kayan aiki ba
✅Outpatient: Ana shigowa asibiti a koma gida rana guda
✅Inpatient: Ana kwantar da mara lafiya a asibiti na kwana daya ko fiye
✅In remission: Cuta ta lafa ko ta tsaya, amma ba lallai ta warke gaba daya ba
✅Membrane: Siririyar fata ko nama da ke rufe ko hada sassan jiki
✅Acute: Cuta mai zuwa kwatsam, amma ba ta dade ba
✅Angina: Ciwon kirji da ya shafi zuciya, yana zuwa yana tafiya
✅Gastroesophageal Reflux Disease (GERD): Ciwon zuciya
(heartburn) / tashin acid daga ciki
✅Cellulitis: Kumburi ko kamuwa da cuta a karkashin fata
✅Epidermis: Fatar jiki ta waje
✅Neutrophils: Nau’in farin jinin jiki mafi yawa
✅Edema: Kumburi (taruwar ruwa a jiki)
✅Embolism: Toshewar jini (jinin da ya daskare)
✅Sutures: Dinki (stitches)
✅Polyp: Tsiro ko girman nama mara kauri
✅Compound fracture: Karyewar kashi da ya fito ta fata
✅Comminuted fracture: Karyewar kashi da ya tarwatse zuwa sassa da dama.
Musa Abdu Shehu
29/12/2025
Inason na dawo amfani da page.
Kwarai kuwa
07/12/2025
Warin jiki Yana daga abunda yake zubarwa da mutum mutunci a idon jama'a, Kuma matsalan abun shine mutum bazai iya zuwa ya tinkareka yace jikinka Yana Wari ka gyara bah.
Sbd haka kuwa ya zama dole ka kiyaye haka Koda ko zaka hanawa cikinka Abinci neh.
Da wannna dalilin na kawo muku yadda Zaku magance Warin jiki da Kuma gumin hammata
Duba comment section 👇 👇 👇 👇
Musa Abdu Shehu
07/12/2025
06/12/2025
KI KALLI HOTON NAN DA KYAU!!!!!!!
Fatar Mama(breast) takoma irin haka, alama ne na ciwon daji(breast cancer) har sai idan likitane ya tabbatar da aka sin haka.
Dan haka da anga chanji a jikin mama (breast) agar zaya asibiti dan a ɗau mataki da wuri....
Pls ayi sharing don wasu ma su amfana.
Dr Abdurrahman Dambazau
06/12/2025
SALLAR DARE: SIRRIN DA ALLAH KE BUƊEWA GA WANDA YA NEME SHI A HANKALI
Akwai wasu ibadodi da ake ji daga baki, amma sallar dare ibada ce da ake ji daga zuciya.
Ba kowa ne yake tashi cikin dare ba — amma duk wanda ya tashi, ALLAH ba ya mantawa da shi.
✨ Hadisin da yake motsa zuciya:
Annabi (S.A.W) ya ce:
“Ubangijinmu yana sauka zuwa sama ta duniya a kowace rana cikin sashen ƙarshe na dare, yana cewa:
‘Wane ne yake kiranNi in amsa masa?
Wane ne yake roƙonNi in ba shi?
Wane ne yake neman gafarata in gafarta masa?’”
— Bukhari da Muslim
Wannan kira ne daga Mahaliccinka. Idan ka ji wannan kira, ka wuce duniya ka bar bayan ta.
💧 Yaya zaka yi Sallar dare ba tare da wahala ba?
Ba don ka yi yawa ba ne, don ka yi gaskiya ne.
Tashi da zuciya mai salama.
Yi raka’a biyu kawai — idan ka ƙara, alheri ne.
Ka yi su kamar kana magana da Allah a zuciya.
Idan ka gama, kayi Witr, ko da raka’a ɗaya ce.
Sallar dare ba ce don manya kawai; don masu buƙata ce.
🌺 Abubuwan da Sallar dare ke yi maka (idan ka ɗan ɗanɗana ta):
Tana wanke zuciya daga nauyin da ka ɗauka tun safiya.
Tana sa ka ji kwanciya da abin da baka samu ba.
Tana buɗe maka ƙofofin da ka sha mantawa da su.
Tana jawo rahamar da ba a bayyane take zuwa ba.
Allah ya ce:
“Kuma a cikin dare suna tashi suna roƙon gafara.”
— Qur’ani 51:18
Mutum mai yin hakan baya da tsoro — saboda yana tare da Mai Tsaron da baya bacci.
🌌 Ka ji sirrin?
Sallar dare tana koya maka wani abu mai ƙarfi:
“Abin da kake nema a hannun Allah yake, ba a hannun mutane ba.”
Shi ya sa duk wanda ya saba da ita, ba ya sanya zuciyarsa a duniya sosai — saboda ya riga ya dandana nutsuwar da duniya bata iya bayarwa.
Giveaway now
Drop your account number
05/12/2025
mata Mutanen mu😁🥴.Gaskiya dole Nima in samo wata ustaziya mu Daidaita🥴💃.
Wani bincike da masana daga Jami’ar Stanford sukace laushin murya da salon furuci na mace na iya exciting jijiyar vagus a jikin namiji.
Wannan jijiya tana da muhimmiyar rawa wajen daidaita bugun zuciya da kawo nutsuwa.
Idan aka motsa ta, tana taimakawa wajen mayar da jiki zuwa yanayin hutu (parasympathetic state).
Saboda haka, jin murya mai taushi ta mace na iya rage damuwa kuma ya ƙara kwanciyar hankali ga mutum.
Wannan alaƙa tana nuna yadda sauti zai iya tasiri sosai ga jiki da yanayin zuciya.
shiyasa sai kaga mutum kamar karan kada Miya 😂Amma da zarar yayi aure sai ya mulmule toh matar itace sirrin 🥴😃.
Malam go and marry 😂
Mata rahama neh.
Bilal Yakubu Ballah
05/12/2025
15/10/2025
price. 🤙
09024839601
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Telephone
Website
Address
Lagos
ABUJA