Ishaq Magaji Kwankiyel
HASBUNALLAHU WANI IMAL WAKIL
Ana maganar Tsaro wa yake ta Samun ƴancin Nigeria na wasu shekaru.
NIGERIA AT 63 🇳🇬
1st October 1960 to 2023
1. Ina alfahari da ƙasata ta gado Najeriya, ina alfahari da Jahata ta Bauchi, zuciya ta na tsinkewa idan na tuna yanda jinin bayin Allah maza da mata da yara da manya ke kwaranya a cikin ƙasar da magabatan mu s**a yi yaƙi da rayuwa kan su domin gina mana ita. Sanadiyyar rashin kishin ƙasa na shuwagabannin mu.
1. Boko Haram
11. Masu Garkuwa da mutane (ƴan fashin daji)
111. Faɗan ƙabilanci da addini
2. Ina matuƙar baƙin cikin yanda Damakoradiyya ta gaza samun ƴanci a ƙasa ta, sbd har gobe ana ɗauki ɗora ne, cuwa-cuwa da murɗiyar zaɓe, talaka bashi da ƴanci ko da kuwa na samun abinda zai ci ma cikin sa a nutse, yunwa da tsananin talaucin da aka ƙaƙaba mana, mun yi hannun riga da cigaban rayuwa sai dai a wasu ƙasashen.
3. Ƙasata babu zaman lafiya matsalar tsaro, babu isashshiyar wutar lantarki, ilimin yafi ƙarfin talaka. Ɗan abinda s**a tarar na sauƙin rayuwa sun kwace, amanar da s**a ɗauka sun ci.
UWATA NAJERIYA UBANGIJI ALLAH YA KAWO LOKACIN DA ƳAƳAN KI ZA SU SAN DARAJAR KI. Allah ya kawo ƙarshen bautar da bayin Allah kai tsaye .
Duk da haka sai na yi alfahari da kasancewa ta Ɗan Najeriya. Ina alfahari da yare na da addinina da ƙabila.
Ishaq M Abubakar Konkiyel
1st October 2023
Nikan bazan Iya ba gaskiya
Click here to claim your Sponsored Listing.
Contact the business
Telephone
Website
Address
Bauchi
KONKIYEL