shamsiya nura

shamsiya nura

Share

self

21/07/2026

DUKIYA BA TA FI SOYAYYA BA
pase 1💔💔💔💔
By Shamsiya nura
🥰🥰🥰🥰🥰

Kashi na 1: Sabuwar Rayuwa a Jami'a

Da sanyin safiyar Litinin ne aka fara sabon zangon karatu a Royal International University, ɗaya daga cikin manyan jami'o'in ƙasar. Harabar makarantar ta cika da sabbin ɗalibai da tsofaffi, kowa na ta murna da sake haɗuwa da abokansa.

A cikin ɗaliban akwai matasa uku da ba su san cewa ƙaddara za ta haɗa rayuwarsu ba.

Amir ɗan gidan Alhaji Bashir ne, fitaccen attajiri kuma hamshaƙin ɗan kasuwa. Duk da irin dukiyar da gidansu suke da ita, Amir mutum ne mai natsuwa, tawali'u da mutunta mutane. Ba ya son a san shi da kuɗi, yana son a girmama shi saboda halinsa.

A wannan rana, Amir ya isa makaranta da wuri. Bayan ya kammala rajistar darussa, ya nufi ajinsu domin jiran malami.

A daidai wannan lokaci, wata baƙar mota ta tsaya a ƙofar makarantar. Wata kyakkyawar budurwa ta fito cikin nutsuwa. Sanye take da kayan makaranta masu kyau, fuskarta cike da annuri.

Ita ce Amira, 'yar Alhaji Kabiru, shahararren attajiri. Ta shiga makarantar cikin ladabi, yayin da wasu É—alibai s**a fara kallonta saboda kyawunta.

Da Amir ya É—aga kai ya kalle ta, sai ya kasa É—auke idonsa.

A zuciyarsa ya ce,

"Subhanallah... Ban taɓa ganin kyakkyawar budurwa irinta ba."

Amma bai yi yunƙurin binsa ko yin wata magana da ita ba. Sai ya ci gaba da zama yana kallonta daga nesa.

Bayan Æ´an mintuna, wani matashi mai fara'a ya shigo ajin. Yana gaisawa da É—alibai cikin raha da murmushi.

Sunansa Abdul.

Abdul ya zauna a kujerar da ke kusa da Amira.

"Assalamu alaikum," Abdul ya faÉ—a cikin murmushi.

"Wa alaikumus salam," Amira ta amsa tana murmushi.

Nan s**a fara hira cikin girmamawa, suna gabatar da kansu. Ashe dukansu sabbin É—alibai ne a wannan sashe.

Malamin ya shigo, aka fara darasi. Amma duk lokacin da Amir ya É—aga kai, idanunsa kan sauka kan Amira.

Bayan an tashi daga aji, Amir ya ga Amira tana ƙoƙarin ɗaukar wasu littattafai da s**a faɗi.

Kafin ya isa ya taimaka mata, Abdul ya riga ya s

24/04/2026

Wannan labarin yayi matukar bani dariya sosae wallh Amma ku karanta kuj😂😂

😂🤣🤣Yau nayi dariyar dana Dade banyi ba Bari na Baku lbr😎

Akwai Wani Kanina idan ya kwanta bacci baya taba Tashi dakansa sedai a tasheshi koda kuwa zekai awa Nawa ne.
Haka kullum Maman mu take Fama idan ya kwanta bcc tun na dare wlh idan ba a tasheshi ba Se yakawo karfe 11 in Dai ba tashinsa Akai yayi sallah ba.
Jiya Maman mu batanan yasan Babu me tashinsa da safe Yau yai ta baccin sa Har 11 da Wani abun be Tashi ba.
Se kanwata tace mu tsoratashi tunda ance idan mutum ya rasu ze dinga Jin abinda mutane suke cewa Amma shi zeyi ta magana ba xa a jishi ba.
😎😀Shikenan Se ta tafi dakinsa ta fara Dan tattabashi alamar zata tasheshi da taga ya fara Mika alamar ze Tashi Se kuka ta Dora hannunta Akai ta zunduma Tana cewa Yaya zo kiga imam ya rasu wlh ya rasu ni Kuma na taho da gudu na fara salati Ina tabashi Ina cewa tabbas da gaske k**e ya mutu😅
Ai kuwa ya Mike tsaye Yana cewa wlh ban mutu ba kutabani ku Gani nine imam wlh nine imam🤣Mukam muka cigaba da kukan mu muna taba kan katifar sa alamar bamusan ya Mike ba azuwan shi muke tabawa 😂nafito na tsiri wayan Karya Ina cewa mama imam ya rasu fa baya motsi da alama tun cikin dare ya rasu 😅Ai kuwa ya Kara gigicewa ya biyoni falo Yana cewa Yaya kinganni fa nine wlh ban mutu ba Ni Kuma na cigaba da kukana nayi Kamar bansan Yana yiba na wuceshi na Koma Dakin nace Khadija ja bargon ki rufe gawar kixo muje mu fadawa makota azo Ai masa wanka🤣
Haba base mukaga yaro ya sulale kasa ya Fadi ba nan da nan hankalin mu ya Tashi kukan Karya ya xama na gaskiya 😥Se can mukaji yana wlh ban mutu ba ban mutu ba kar kusa abinne ni da Raina 😥😥kanwata tace imam da wasa pa muke Maka Se da kyar ya yarda seya kamo hannunta seya saki ya kamo Nawa😅😅😅
Shegen Kaya kunganshi Yau ba wnn baccin ranar da ankira sallah zakuga yatashi 🤣🤣🤣🤦

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Birnin-Kebbi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Bayan Filin Sukuwa
Birnin-Kebbi

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when shamsiya nura posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Birnin-Kebbi.