Usman Adamu
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Usman Adamu, zaria Road, Funtua.
Insha Allah
01/09/2026
Yau ma dai kamar jiya muna kira ga al'ummar yankunan dukke - Gardawa - layin gara - unguwar Éahiru da sauran yankunan funtua har cikin gari ku ankare, don yanzu ake tabbatar mana miyagvn nan har sun woto layin yarkasuwa sun yo gabas, haka s**a yi mana jiya bayan mun bada report sai gasu cikin unguwar Éahiru wanda har muka rqsa mutane 3 muna Addu'ar Allah ta'ala yasa yau dai ajqli ne ya fito dasu ya kare yan uwan mu daga dukkanin mugvn nufinsu amen,
Dan Allah ayi gaggawar sanar da waÉanda basu sani ba domin ceto rayukan su
SaĆon Godiya Daga Al'ummar Garin TumÉurkai Zuwa Ga A.A Albasu
A ranar 21 ga watan Janairu, 2026, alâummar garin TumÉurkai ta bayyana muradinta cikin mutunci da girmamawa ta hanyar rubutu da na wallafa a wannan fej Éin nawa da yawun al'ummar garin TumÉurkai, wanda ya shafi aikin sanya fitilun t**i da A.A. Albasu ya kawo domin haskaka garin TumÉurkai. SaĆon ya fito ne ba da zargi ko Ćalubale ba, sai dai a matsayin roĆo na alâumma mai cike da godiya da fatan alheri.
Abin farin ciki da Ćarfafa gwiwa shi ne, saĆon bai tafi a banza ba. Bayan wallafa rubutun, na samu sahihan bayanai daga makusanta da masu kusanci da A.A. Albasu cewa saĆon ya isa gare shi, ya kuma karÉe shi da kyakkyawar fahimta. Haka kuma, an bayyana min cewa ya ji koken alâumma, kuma cikin yardar Allah, nan ba da jimawa ba za a ci gaba da aikin sanya fitilun domin su zama abin morewa ga mutanen da aka yi niyya domin su tun farko.
Wannan lamari ya sake tabbatar da muhimmancin magana cikin hikima, da amfani da kafar sadarwa ta hanya mai kyau wajen isar da saĆon alâumma. Ya nuna cewa idan aka yi magana da hujja, ladabi da girmamawa, tana iya samar da sakamako mai kyau fiye da hayaniya ko faÉa. Haka kuma, ya nuna cewa akwai shugabanni da masu hannu da shuni da ke sauraron jamaâa, kuma ke Éaukar irin waÉannan kira da muhimmanci.
Mu alâummar TuÉurkai muna miĆa babbar godiya ga A.A. Albasu bisa yadda ya karÉi wannan kira, da yadda ya nuna cewa har yanzu zuciyarsa tana tare da jamaâarsa. Wannan amsa da aka samu ta Ćara wa jamaâa kwarin gwiwa, ta kuma Ćarfafa alaĆar fahimta da amincewa tsakanin alâumma da masu hidima.
Muna adduâa Allah MaÉaukakin Sarki Ya saka masa da alheri, Ya Ćara masa arziki mai albarka, Ya ba shi lafiya da tsawon rai, tare da Ćara masa ikon ci gaba da aiwatar da ayyukan da za su amfani alâumma. Muna kuma roĆon Allah Ya sanya wannan kyakkyawan yunĆuri ya zama silar Ćarin ayyukan ci gaba a TumÉurkai da ma sauran yankuna.
Hakika, idan alheri ya fara, kuma aka saurari muradin jamaâa, kammala shi shi ne ginshiĆin nasara. Muna fatan ganin hasken fitilun TumÉurkai ba wai kawai a t**i ba, har ma a zukatan alâummaâhaske na tsaro, haÉin kai da ci gaba.
Allah Ya sanya alheri ya dore. Ameen.
âď¸
Civic-Minded Patriot
Audi Sani
SAĆON KIRA GA MAI GIRMA GWAMNAN JIHAR KATSINA MALAM Dr. Dikko Umaru Radda , PhD
Mai girma Gwamna,
Muna kira gare ka bisa haĆĆinmu na âyan Ćasa da kuma nauyin da Kundin Tsarin Mulki ya Éora wa gwamnati.
Hanyar Marabar Maska â Tumburkai âAâ â Magaji Wando âĆan Sodaâ Ćan Tankari zuwa Ćandume ta lalace Ćwarai, har ta zama barazana ga rayuka, sufuri, noma da kasuwanci. Duk da muhimmancinta ga alâummar Dandume, har yanzu ba a samu kulawa ta gaggawa a kanta ba.
Bisa Sashe na 14(2)(b) na Kundin Tsarin Mulki, jin daÉin jamaâa shi ne babban manufar gwamnati.
Haka kuma, Sashe na 16(2)(d) ya wajabta samar da abubuwan more rayuwa, yayin da Second Schedule, Part II, Item 11 ya nuna a sarari cewa gyaran hanyoyin da ba na tarayya ba na cikin ikon jiha.
Don Haka wannan haĆĆi ne na doka!
Muna roĆonka cikin ladabi amma a fili da ka:
đ ba da umarnin duba halin hanyar nan take,
đ sannan a Éauki matakin gaggawa na gyara ko sake gina ta.
Kulawarka a kan wannan batu za ta zama adalci ga jamaâa kuma abin alfahari a tarihinka na shugabanci.
Daga:
Alâummar Karamar Hukumar Dandume
(Musamman gundumar Maska, Tumburkai âAâ, Magaji Wando, Ćan Soda Da Ćan Tankari)
âď¸ Muhammad Magaji TumÉurkai
Federal Road Safety Corps Nigeria
Nigeria Police Force
Katsina Post
Legit.ng Hausa
DW Hausa
Rariya
, Phd
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Funtua
1996
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Usman Adamu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.
02/09/2026