Farin Jini Writer's Association
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Farin Jini Writer's Association, Beauty, cosmetic & personal care, Gboko.
Mun bud'e wannan shafinne domin masoyan mu dan Haka muna yiwa kowa barka da zuwa sannan muna Mai sanar daku zaku samu littafanmu harma da sauran littafai muna fatan zamu samu goyon bayanku ta hanyar comments
BABBAN MATSALA...
*Secret Writer*
Farin Jini Writer's Asso..
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
*Arrahmanu*
3️⃣&4️⃣
Baiwar Allah lafiya k**e tsaye cikin Rana Ga jariri anata miki magana bakya jin mutane ne? a firgice ta ɗago kallon jama'ar dake binta da ido take cikin wani irin kuka me taɓa zuciyar duk wani mai imani ta fara magana hawaye na zariya a ƙuncinta Dan Allah ku temaka min ku tafi dani wlh bansan inda zan nufa ba... ganin yadda suke kallonta ya hanata karasa maganar ɗaya-bayan ɗaya s**a soma ja da baya ,domin temako a wannan zamanin ya zama matsala kana zaman zaman ka zaka jefa kanka a uku, bayan kai kuma kaji tausayine ka temaka, cewar ɗaya daga cikin mutanen rumgume Al'amin tayi wanda shima zafin ranan dake taɓashi yasa ya fara kuka ƙasa ƙasa magiya take musu amma babu wanda ya kulata.
Komawa tayi inuwar bishiyar dabinon dake jikin masallacin tashar motan jijjiga Al'amin ta fara tana tunanin mafita to yanzun lna zata? gashi bata da kuɗi bata da komai bata da hanyar samu cikin ƙankanin lokaci duk ta fice a hayyacinta ɗankwalin dake kanta ta cire tare da rufe masa saman kanshi bayan ta ɗaurashi a kafaɗarta wajen garejin ta nufa gefe ta samu ta zauna shuru ganin yadda tayi kalan tausayi ne yasa wasu s**a ɗauka ko almajirace a hankali ake jefa mata sadaka kallon kuɗaɗen data samu tayi a hankali ta fara kirgawa dubu huɗu da ɗari biyu da hamsin yaye lulluɓin data rufe Al'amin tayi nan taga yana barci tare da sauke ajiyan zuciya ga yatsa biyu ya tura a baki yana tsotsewa ido ta kura mishi tana kallon yadda yake barci da ganin yanayin da yake sauke numfashi kasan barcin wahala ne miƙewa tai tare da nufar cikin tashan lokacin ana kiraye kiranye sallan magariba ɗan roba me faɗi ta samu taje gurin rijiyan da ake jan ruwa ganinta da yaro ne yasa wanda ke kan rijiyan zuba mata ruwa goya Al'amin tayi wanda ya tashi yanata mutsu mutsu ko ba'a faɗa mata ba tasan yunwa yake ji, alwala tayi tare da rage sauran ruwan ta ajiye a daddafe tayi sallah a barandan masallacin gurin me shayi ta nufa ta bashi amshin tana kallon yanda ya zuba madara kaɗan zai zuba sugar tace yasa kaɗan bayan ta karɓa ta samu gefe ta zauna se da yaɗan huce kafin ta fara ɗiba a cokali tana bawa Al'amin cikin sauri yake karɓa har yana kwarewa ganin yadda yake shane yasa ta zuba mishi ido tana zubda da ƙwalla sai da yasha sosai kafin ya fara turowa alaman ya ƙoshi sauran tasha tare sannan ta ɗaurashi saman kafaɗanta tana shafa ƙanshi zuwa bayanshi
Agurin ta zauna yanda taga rana haka taga dare domin zuwa shabiyu ya faraka da rikici sai kuka yake tayi lallashin duniya yaki yin shiru tama manta da panpas a jikinsa ashe ya ɓata ne kuma ya isheshi shiyasa yake kuka ganin baiyi shuru bane yasa ta fara duba jikinsa mikewa tayi a daren taja ruwa a rijiya rasa yadda zata wanke masa jikinsa tayi ganin ruwan yayi sanyi sosai gurin me shayin ta nufa ganin har zuwa lokacin bai tashi ba cikin marerecewa ta fara roƙonsa Dan Allah ka temaka min da ruwan zafi zanma yaro wanka n... kafirin kallon daya watsa mata ne yasata yin shuru jiki a saɓule ta bar gurin tana jin yadda wani mutumi a gurin ya fara faɗa haba sai kace ba musulmi ba temakonta fa zakayi kasan mahimmancin temako kuwa ? kasan wadda zai temake ka nan gaba kuwa? ku ringa nazarin gaba domin tafi baya yawa tsaki yayi tana barin gurin zamanta tayi tare da rumgume Al'amin ta fashe da kuka shima kuka yake jin motsi a kusa da itane yasa ta juyawa a firgice tare da ƙanƙanme yaronta ajiye mata karamin bokiti mutumin yayi kallonsa kawai take domin taji sanda yakema me shayin magana, kiyi hakuri Baiwar Allah ga ruwan mutanen yanzun sam basu da tunani kuma a wannan zamanin temako ya zama masifa Allah yasa mu dace kawai Nagode Allah yasa da Alkhairi yadda ka temaka min ubangiji ya dubeka ya biya maka bukatunka na Alkhairi ɗan murmushi yayi tare da ajiye mata baƙar leda cikin jin daɗi ta mike ledan ta duba taga sabulu harda wani panpas ɗin haɗe da riga addu'a ta ringa masa ba karamin daɗi taji ba, surka ruwan tayi dai-dai yadda zai masa tayi a hankali k**an yadda taga Anti mairo na masa wanka i'tama ta masa tana gamawa ta sanyashi cikin sauran ruwan lamo yayi yana jin daɗi ganin ya fara Gyangyaɗine yasa ta cireshi a bokitin tare da saka mishi kaya goyashi tayi tare da wanke kayan data cire masa ta shanya...
Washe gari bayan tayi sallar asuba tun kafin gari ya gama wayewa mutumin ya sake kawo mata ruwan zafi tare da wasu kayan harɗa abin shayi cikin Jok ɗan dede da burodi gaishe shi tayi tare da masa godiya wanka ta fara ma al'amin wanda tunda yafara barci jiya bai farka ba,
Shayin ta fara bashi yasha kafin i'tama tasha jama'ane s**a fara taruwa nan aka fara kiran Nassarawa Lafia fasinja masu tafiya suyi maza kafin mota ya cika cewar kwandasta cikin kayan da mutumin ya kawo mata harda kuɗi dubu biyu mikewa tayi tare da ɗaure kayan al'amin a leda ta jefe cikin bokitin ta nufi gurin motan i'tama ta shiga bayan ta biya kuɗin motan mutane na gama shiga direva ya tada motan kallon garin tayi zuciyarta na wani i'rin beating rumgume Al'amin daketa sharan barcinsa tayi yaron da baisan komai ba ana gudunsa yaron da bashi da laifi amma an ɗauki tsanar duniya a ɗauramin dashi Nida zaria har abada insha Allahu banga abinda zai dawo dani ba, Zuciyarta ne ya tuno mata da mahaifiyarta da i'rin tashin hankalin da take hangowa a idanunta lokacin da Abba i'shaqa da Baffa aliyu s**a mata koran kare har kuka taga Daada tana yi, Allah sarki Daada ban kyauta miki ba, amma babu yadda na isa na kauce abinda Allah ya kaddaromin.. a hankali ta sauke ajiyan zuciya a dai-dai lokacin da zuke shirin barin garin gabaɗaya...
Babu i'rin taimakon da likitoci basuyi don su tsayar da cikin ba amma abin ya gagara domin cikin ya lalace karshe wankin ciki s**a mata Mustafa sai kaiwa da komowa yake lokacin da likitan take sanarmasa da ɓarewan cikin sai da yayi kwalla domin ba karamin kwallafa rai yayi ba amma dake yana da tauhidi take ya barwa allah komai ya shiga addua Allah ya mabawa matarshi lafiya ya kuma kare Aminah aduk inda take kwananta biyar aka sallamota direct gida ya nufo da i'ta domin likitoci sunce tana bukatar hutu sannan kar'a takura mata da surutu domin tana fama da ciwon kai ga damuwa da yake cunkushe a zuciyarta.
tana ganin Yanda mahaifiyarta ta rame hankalinta ya kuma tashi domin tasan yanda Daada take matukar Ƙaunar Maami kullun cikin kuka take domin ba ƙaramin ciwo take ji a zuciyarta game da irin tozarcin da iyayenta s**ayiwa Ƴar uwarta ba, i'ta shaida ce tasan halin ƙanwarta ciki da bai, inba ƙaddara ba taya aminah zatayi haka? tana addu'ar Allah ya kareta damuwarta ɗaya l'na aminah zata nufa wacce rayuwa zata fisƙanta ya zata kasance ga ɗanyen jego wazai kula da i'ta? zuciyarta yace Allah mana kin bama Allah baya ɗorawa bawanshi abinda yafi karfinsa kin mata kafin Allah ya saukar da cuta saida ya saukar da maganinsa? ygaɗa kai tayi tare da faɗin tabbas hakane...
*Me karatu wani irin rayuwa kake hasasowa aminah da Al'amin shin Hukuncin data yanke na barin Zaria kuna ganin tayi dai-dai? duk inna jiran amsoshinku*
Share fisabidillah 👏🏼
Farin Jini Writer's Association Mun bud'e wannan shafinne domin masoyan mu dan Haka muna yiwa kowa barka da zuwa sannan muna Mai sanar daku zaku samu littafanmu harma da sauran littafai muna fatan zamu samu goyon bayanku ta hanyar comments
BABBAN MATSALA...
*Secret Writer*
Farin Jini Writer's Asso..
https://www.facebook.com/farinjiniwritersassociation/
Alhamdulillah Ya Allah yanda Nafara wannan littafin lafiya, ubangiji ka nufeni da gamashi lafiya Allah ka bani i'kon rubuta abinda zai Amfani Al'uma..
1️⃣&2️⃣
Dakyar take d'aga kafafuwanta sak**akon Nauyin da s**ayi mata waigawa tayi taga gurin dulun babu alamar haske kukan da jaririn ya saka da karfi ne ya kara d'aga mata hankalin fiye da wadda take ciki, tafiya ta cigaba dayi tana Tunanin abinda zataje ta tarar hawaye me zafine ya sauka a 'Kuncinta dakyar take tafiya hannunta dake makale da Alluran karin ruwa sai zugi yake mata ka Kafafuwanta da s**a Kunbura jikinta gbdy ya 'baci da jini Agalabaice taci gaba da tafiya Kiran sallar Assatu dayaratsa Kunnunwanta ne yasa ta sauke Nannauyar Ajiyan zuciya take Kuma taji gabanta Na lugude k**an zata fad'o kasa zuwa wannan lokacin Jaririn yayi shuru sai tsotar hannuwansa yake wanda babu komai jikinsa Banda jini domin ko arzikin wanka Bai samuba sannu a hankali haske ya Fara bayyana ra'bewa tayi a rumfar dake kofar Gidansu tana jijjiga yaron da yake sauke Ajiyan zuciya akai-akai Wanda gbdy daga i'ta harshi sun galabaita tana jin takun sahun iyayenta Maza da Yayyunta sai da ta tabbatar An tada sallah kafin ta fad'a Gidan Kamar wacce aka jefota Rike qirji Daada tayi sak**akon Ganin mutum , a hargitse ta Fara karaton innalillahi wainna'ilaihi rajiun dai-dai lokacin da aka kunna wutar sola take haske ya gauraye gurin a rarrabe ta kira sunanta tare da ja,da baya tana nunata A.M..E...E..N..A...kafin ta karasa jaririn ya kwala qara, dafe qirji tayi take idanuwanta s**ayo waje Ganin sai nunani dake ta kasa magana yasa na sake 'kan'kame shi jikina i'na sakin gunjin kuka ji nayi kafafuwana sun kasa ɗaukana take na zube a kasa nan komai ya tsaya min bansan me yafaru ba, farkawa nayi na gannin kwance gadon Daada wanda duk na ɓatashi da jini ga jaririna dake ta kuka kasa kasa.. muryanshi baya fita. zaburowa nayi batare da nalura da jama'ar ɗakinta na ɗaukeshi na sanya a qirjina lna jijjigashi muryan Baffa Aliyu ne ya daki dodon kunenta (Yayan mahaifinta) k**ar koda yaushe cikin zafin rai ya nunata da yatsa idanunshi sunyi jawur,...Aminah zina a zuri'ata ɗan Shege a dangina Aminah? ashe ba karatun dana turaki kikaje ba, ashe shashsanci k**e a bayan idanunmu!... shuru yayi sakamon sallamar da'aketayi tun ɗazun Ishaq ne ya miƙe jiki ba kwari ya nufi waje matane tsaye sai kananun surutai suke zaiyi magana Addar Ahmad ta dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu. ba dogon surutu ya kawomu ba kayan lefen mu muka zo, ɗauka tunda ga Aminah ta dawo da babbar tsaraba mukan bazamu haɗa i'ri... dakata Addah wannan furucin bai k**ata ba, cewar ɗaya daga cikin tawagarta gaba yayi zuciyarshi na wani i'rin tafasa shi Aminah zata tozarta, kaɗa kai yayi tare da nufar cikin gidan suna take mishi baya, guɗa Addah ta sake nan hankali kowa yayo waje mikewa s**ayi s**a fito banda Aminah data sunkuyar da kai kasa hawayen na kai komo. Kayanmu mukazo ɗauka! Addar Ahmad ta faɗa tana yatsine yatsine tare da hura hanci.
Cikin tashin hankali Daada ta ɗaura hannu akai tana sallallami tare da basu hakuri amma i'na ko sauraronta basuyi ba, Cikin zafin rai Baffa Aliyu yashiga ɗibo musu kayansu Addar ahmad tace Hankali kar a ɓata mana akwatuna haka kawai, nunata yayi da yatsa tare dayin kwafa fita s**ayi da kayansu zuwa lokacin jama'a sun fara taruwa a kofar gidan jin ihun Aminah kawai s**ayi da sauri Daada tayi ɗakin lshaq ne yake bugunta kota'ina i'takan sai kare ɗanta take domin so yake lallai saiya illatasu ni zaki tozarta ni zaki kunyata a idon mutanen da suke girmamani wallahi baki i'sa ba, na yafe ki Aminah! na cireki daga cikin Ƴa'yana Aminah kiyi nesa dani bana bukatarki cikin zuri'ata.... cak kukanta ya ɗauke riƙe masa riga tayi cikin firgicewa da kalamansa ta fara magana Abba Kayi min rai Baffa ku saurareni wallahi wallahi ban aiakata abinda kuke tuhumata dashi ba billahin'azim ban taka ɗaya daga cikin tarbiyanku ba.... marin bakinta yayi tare da kwacewa daga riƙon data masa sa kai yayi zai fita a bakin kofa s**aci karo da mairamu juyowa yayi yana kallon Daada datake tsaye jikinta sai tsuma yake Wallahi karta yarda ko minti ɗaya ta karamin a gidana! Aliyu mutafi, koran Yayyunta dake tsaye suna kuka yayi domin ba karamin tausayi ta basu ba, wani irin kallo Baffa ya watsa mata tare da jan tsaki zuciyarshi tafasata take Murya cike da kuka take roƙonsu su saurareta amma i'na zuciya ta ɗi'besu..
kasa ta sauko tare da k**a kafar mahaifiyarta Dan girman Allah kudena min wannan kallon wallahi Allah banyi komai ba.... ance miki kowa mahaukaci ne k**ar ke, ko makoho ya shafa yaji yasan ɗanki ne Aminatu jikinki ɗauke yake da ɗanye jego tarbiyan da na miki kenan kije duniya tafi bagaruwa Jima, ni kika tozarta ba? akwai Allah amma bazan miki baki ba.. ta karasa maganarta cike da kuka Daada....kul karna kara jin kin ambaci sunana tashi ki koma ɗakinki shuru mairamu tayi ganin mahaifiyartasu ta tsareta da idanuwane yasa ta k**a hannun aminah tare da ɗaunkan jaririn ta fara janta tana tirjewa Dan Allah ku saurareni Daada bayanku bani da kowa Yaya Maryam ki mata magana sunki min Uziri Ahmad sun karɓe kayan Auren mu wayyo ya zanyi da raina mai yasa Ahmad bazai rumgumeni a haka ba, laifi ne dan Allah ya jarabceni ni kaina ba a son raina hakan ta kasance dani ba wallahi ban taɓa kusantar zina ba! ban aikata komai ba.
Maami...! Mairamu ta kira sunan ta Yaya maryam dan Allah dan Annabi ki temaki wayyo Daada wallahi Allah bazan sake bijirewa maganar ki, ba. dan Allah ki barni na zauna bansan inda zanje ba, bansan wacce rayuwa zan fisƙanta duniyar nan ba kowa zai amsheka da kaddarar ka ba, ku da ya zame muku dolena kunƙi kun kukana wa kuke tunanin zai dubi lamarina ? wazai tallafi rayuwata dana marayan jaririn nan Daada ki yafe min nasan ban kyauta miki ba! ki rarrashi Abbanmu Daada... fushi duk ba naku bane jarrabice fa? juyar da kanta tayi, zuciyarta ciƙe da tausayin Ƴarta, lna ma da ana sauyawa mutum ƙaddara! Astagfurullahi Allah ta faɗa tare da zama tana sakin kuka mai cin rai..
Gidanta s**a nufa Amina banda kuka babu abinda take yi, koda s**a shiga ɗaki ta kasa zama saida Mairamu ta zaunar da i'ta tare da karɓan jaririn A hannunta murhu ta haɗa tare da ɗora ruwan zafi yaron ta fara ma wanka tare da gasa masa cibi.. kafin ta juyema Aminah sauran ruwan zuwa lokacin Mustafa (Mijinta) ya dawo duk jikinshi a sanyaye domin har mahauta sai dalabari ya iskeshi abinde ba daɗin ji domin kowa ya cika da mamakin jin wannan batun sabida aminah ko yatsa kasa mata a baki bazata ciza ba, amma yau i'ta tadawo ma sarkin fawa jika. kuma ƊanShege lamarin babu daɗin ji zama yayi Mairamu ta kawo masa ruwa gashi sai kaiwa da komowa take goye da yaro ga tsohon ciki.. maganarta ne ya katse shi daga tunanin da yake Yah musty ka dawo? ta faɗa tana zama kusa dashi tare da kwanco goyon, gyaɗa mata kai kawai yayi, jaririn ya karɓa daga hannunta ɗan murmushi yayi tare da furta masha Allah, shekarunsu shida kenan da aure sai wannan karon Allah ya bawa mairamu ciki yana matukar son yara shiyasa yaji kaunar yaron take Babu abinda za'a sanya mishi sannan dan Allah nasan yanzun Su Abba basa gida ka biya ka tawo da sauran Kayan Maami dake gurin Daada cikin hanzari ya mike ya fita kicibis s**ayi sunkuyar da kanta tayi kasa. shi kuwa tausayin tane ya kuma cika zuciyarshi Cikin mintuna kalilan ya dawo da kaya niki-niki duk da basu da karfi yayi kokari dai-dai gwargwado harda madara da su lipto ya siya mata.
koda ya dawo ya tarar ana daru domin taƙi bawa yaro nono shuru ya tsaya ganin maryam na takura mata yasa yace mata ki barta tunda taki bashi... Haba Yah musty yaron nan sai kuka yake babu komai a cikinsa fa... juyowa yayi da sauri yana laluɓan aljuhunsa tare da faɗin bari lna ruwa fita yayi can sai gashi da madaran Nunah na yara da fida, da kanshi ya dafa bakin fidan kafin ya haɗa madaran, karɓan jaririn yayi a hankali ya sanya mishi fidin ɗin a baki nan ya k**a cikin sauri yake sha ,hawaye masu zafi ne s**a sauko mata cikin kuka tace nagode Yah musty... hararanta yayi yaron na gamasha ya fara barci abinci maryam ta takura mata taci kafin i'tama ta kwanta amma sam barci yaki zuwa mata. misalin takwas suna zaune bayan sun kammala cin abinci Mustafa ya kalli aminah kafin yace Maami wani suna za'a sanyawa jaririn naki? shuru tayi tare da rike hannun yaro tana murzawa magana ake miki kinyi shuru cewar Yayarta, tunani ta fara can tace Aminullah murmushine kwance a fuskarshi yace masha Allah nan ya karɓi yaron tare da masa huɗuba Allah ka raya mana wannan Amintaccen bawan naka kasa ya ɗauki halin masu sunan Allah ka sanya soyayya da tausayin mahaifiyarshi a zuciyarshi Ubangiji kasa ya zama haske ga Al'uman Annabi (s.a.w) mikawa matarsa yayi ta karɓeshi tana hawaye rumgume yaron tayi a qirjinta Allah ka raya Al'amin bisa tafarkin islama! Allah haske rayuwarshi ka saukakawa mahaifiyarshi.. kuka kawai Aminah takeyi a zuciyarta take amshin addu'ar da sukeyi.
washe gari Mustafa ya yanka musu karamin tinkiya ba karamin daɗi abin yama aminah ba lallai ta yarda da karin maganan nan wadda ake cewa naka sai naka, daɗin zama kuma sai bare, mustafa ɗan Baffa Aliyu ne Auren zumunci a aka musu dake kuma mairamu tana ƙaunarshi ba'a samu wata matsala ba suna zaune hankalinsu kwance bame jin kansu. ya siya mata abubuwan bukata sosai suke tattalinta da Al'amin. kwananta biyar da yamma suna zaune tayi tagumi hira mustafa suke amma taki tsoma bakinta duk da yan uwanta ne wadda ada suke hira cikin nishaɗi amma yanzun ta kasa sakin jikinta sai ɗari-ɗari take dasu..
Kallonta Mustafa yayi sannan yayi kira sunanta Aminah...!
amsawa tayi batare da ta ɗago ba, amina kaddara ba kanki farau ba, kuma ba akanki zai kare ba, dukkanmu nan kowa da kalan yadda tasa kaddar zaizo masa bamu sani ba, a'a da zafi zaizo mana ko kuma da sanyi ba, fatanmu Allah karya jarabcemu da abinda bazamu i'ya ɗauka, ba. kiyi hakuri ki dena ware kanki har yanzun ke ƙnawarmuce babu wadda ya wuce kaddara, bazamu taɓa tsanarki ko ƙyamarki ba ki fauwala allah lamuranki ki cikaga da addu'a insha Allahu rayuwa zata zo miki da sauki sannan kiyi hakuri duk da nasan kinadashi amma ki kara Allah yana tare da masu hakuri bawai kuma ya jarrabceki don baya sonki bane, a'a ya jarabbceki ne don ya gwada karfin imaninki Aminah ki watsar da komai ki rumgumi kaddara tana kan kowa, ko yanzun ko anjima... Nagode da tunatarwa Yah musty insha Allahu zanyi aiki da maganark... sauran maganarta ne ya maƙale sak**akon ganin Abba ya nunata da yatsa kin warganaza naki Auren kinzo ki kashe mata nata Auren to wallahi baki isa ba zoki fice kafin na sauya k**anninki shashasha mikewa s**ayi hankali a tashe Abban dan Allah... kul Mairamu inhar na isa dake to karki ce uffam haka kaima mustafa kamin shuru zube gwigwowinta tayi a ƙasa k**an yadda aminah tayi Abban badan ni ba, badon halina ba abba kodan wannan jaririn ka barni cikin ƴan uwana karka rabani dasu.... marin bakinta yayi yana nunata baki isa ba tashi maza-maza bana bukatarki Aminah na barwa duniya ke ki mata kin taɓa sanin ahalina a rayuwarki miƙewa tayi a hankali tare da share hawayenta murmushin karfin hali tayi tare da kallon su. Nagode da taimakon ku gareni k**ar yadda abba yake so haka zanyi zan tafi tafiya ta har abada insha Allahu bazan sake juyowa ba, bare na sake shafa muku baƙin fenti hanyar waje ta nufa musty dake riƙe da kayayyakinta yana mata magana amma taki kulashi dan Allah maami karki tafi! ki tsaya murmushi ta sakar mata Yaya maryam kiyi hakuri domin ni kaina naji na tsahi nahiyar nan.... aminah ki amshi kayayyakin nan dan Allah karki tafi haka, girgiza masa kai, kawai tayi Yah musty nagode na jikina ma da dahalin cirewa wallahi dana cire nagode kunmun komai kun amshi uzirina abinda iyayena s**a gaza min shi saduwar alkhairi.. mairamu na kiranta amma ina tayi nisa ko waiwayen su batayi ba Juyin da cikinta yayi ne yasata dukawa tana riƙe cikinta jin abu na bin jikintane yasata runtsa ido tana karon innalillahi da sauri s**ayi kanta Abba na shirin taɓata ta girgiza masa kai Abba basai ka kusantoni ba, ka barni da baƙin cikin rashin yar uwa masi soyuwa a gareni Abba kayi hakuri idan na ɓata maka rai... daga haka bata sake sanin abinda ke faruwa ba hankalin mustafa idan yayi dubu a wannan lokacin ya tashi ya rasa kalan taimakon da zai mata zama yayi tare da rumgumeta zuciyarshi k**an zata fashe an rabashi da ƴar uwarshi ga matarshi cikin wani yanayi fatanshi ɗaya ubangiji yasa cikin ya tsaya...
*Toh ban sani ba ko tsari da tafiyar labarin ya muku? inhar yayi lna jiran sharhi da comments ɗinku inhar kun karɓi labarin zanci gaba, domin labarine dana tsara mai ciƙe da ma'anoni labari ne mai ban tausayi da tsuma zuciyar me karatu*
08113240980
Farin Jini Writer's Association Mun bud'e wannan shafinne domin masoyan mu dan Haka muna yiwa kowa barka da zuwa sannan muna Mai sanar daku zaku samu littafanmu harma da sauran littafai muna fatan zamu samu goyon bayanku ta hanyar comments
💞 *MAKAHON SO* 💞
*By*
*NASRULLAH*
®️🌁
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..📚📚*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]
_♡F.J.W.A♡_
https://www.facebook.com/FARIN-JINI-Writers-Association-109861227874440/
*SADAUKARWA*
NADIYA ADAM ABUBAKAR
Wattpad
*Nasrullah133*
🅿️1️⃣
__________________Rayuwar duniya abar dubawa ce a yau, abubuwa da dama a mabanbanta lokuta suna faruwa, dubi ga yadda rayuwar duniya yanzu sam komai ya canza, rayuwa tayi tsada a wanan zamanin dole mu farka daga baccin da muke, idan ko mutum ya bari yasa kankance zai ga rayuwa, wani lokacin mutum ka ganshi ya kasan ce cikin farin ciki, wani lokacin kuma ka tsinci mutum cin baƙin ciki, wani lokacin rayuwa zaka ga mutum abun gunin ban sha,awa, wani lokacin kuma abun gunin ban tausayi.
Rayuwar wasu masoya ne su biyu, tsakanin saurayi da budurwa sun yi soyayya sosai, sun shaƙu da junansu sosai, sun sha gwagwarmayar rayuwa duniya sosai wacce, A cikin ta ke ci ke da abun ban mamaki da kuma abun ban al'ajabi.
Su dai waɗanan masoyan guda biyu, sunyi soyayya a tsakanin junansu, sun so junansu sosai sona gaskiya da amana, tare da kyautatawa juna da kuma mutuntawa juna, hasalima girmamawar da take bashi ya wuce misali tsabar son da take mai.
Ita kanta Amlert idan ka tambaye ta wanne kalar so ta ke ma Mahmud bata sani ba?.
Shima haka Mahmud tsabar tsabegen tsagwaron son da ya ke mata, bai san shima ko wanne kalar so ne yake mata ba?.
Kuma su dukan su biyun sun kasance masu biyayya ne, da kuma bin umarni iyayansu. Ko wanne a cikin su yana jin maganar mahaifanshi, amma idan aka zo ɓangaran soyayya, basa jin bari ko sannu.
Domin ko a shirye suke su duka biyun domin su sadaukar da farin cikinsu, da kuma rayuwarsu akan ta junansu.
Sun ɗauki aniya tare da ƙudirin cewa, za su sadaukarwa da junansu rayuwar su a shirye suke domin bawa junansu a gaji da kuma gudunmawa, domin ƙarfafa junansu akan soyayarsu indai akan hakan ne basaji basa gani sun zama makafi, idon su ya makance akan son da suke wa junansu.
Allah sarki so hana ganin laifi, so makaho ne, so rayuwa ne, so kogi ne, so makaranta shikesa mutum ya karanci rayuwar duniya, da iya zama da mutane da kuma mu'amalantar juna a zaman takewar rayuwa mu ta duniya, inji masana ilimin so da ƙauna zamantakewar rayuwa s**a faɗi haka.
Yar uwa ko ɗan uwa tunda ka ke koh ka taɓa? shin ko kin taɓa? Tambayar ka/ki menene so? Menene ƙauna Menene rayuwa?.
Dole duk wani mai soyayya, har indai yasan da cewa ya gina tubalin soyayar shi, a tare da gaskiya da kuma riƙon amana, dole ne yasan haka, waɗanan abubuwan dana lissafo?
Kamar yadda rayuwar waɗanan, bayin Allah ta kasance, tsakanin Mahmud da Amlert.
“Haƙiƙa Mahmud na kamu da tsananin matsanancin sonka, sonka ya shiga cikin ɓargo da jijiya ya mamaye mun zuciyata, ka zamo mun jinin jikina farin cikina, ina sonka ba na so ka yi nesa da ni, bana so na yi rashinka a rayuwata. Ka tausayama zuciyata kai ne wanda ta ke so kuma ta ke ƙauna na mallaka mata ita har abadan-abadan ka damƙe ta amana. Kar kai nesa da ni bazan iya jure rashinka a kusa da ni ba, saboda zuciyata, ta saba da kai hubby. Jinin jikina kai ne bugun zuciyata ina alfahari da kai taurarona , please kar ka bar ni, na mallaka maka kaina, ta hanyar da mallaka mun naka muradin ruhina kai ne nawan". Tana gama faɗin haka fashewa tai da kuka, abun gunin ban tausayi, dole duk wani mai tausayi idan ya kalleta halin da take ci ya tausaya mata.
"Amlert ina son ki kuma ina ƙaunarki, k**ar yadda nasan da cewa kema kuma kina sona sosai, ina son ki sani cewa ina jin abunda ki ke ji cikin na ranki, na raɗaɗi da ƙuna, ina son ni da ke mu riƙe wanan a matsayin wata ƙaddara ce ta rayuwa, muyi haƙuri da junan mu, mu zurawa lamarin Ubangiji idanu muga yacce zai damu, kuma mu cigaba da addu'ah Ubangiji Allah Ya zaɓa mana abunda yafi zama alkhairi ne a garemu tsakanin ni da ke."
Sannan ya ci gaba da cewa, "Na tabbatar da cewa mai addu'ah kuma ya miƙa dukkanin lamarin shi ga Ubangiji Allah S.W.T bazai taɓe bah, ina da ya ƙinin cewa idan muka tashi tsaye muka ƙara zage damtse, muka ƙara ƙaimi domin ganin mu tabbatar da wannan kyakkyawan mafarkin da muke fata namu insha Allahu Rabbi, zamu cin ma nasara da yaddar ilahu.
Amlert ta daɗe tuni da sun kunyar da kanta ƙasa, ya yin da ta ke kuka, amma zuwa can da Mahmud ya fara magana tana sauraronshi, tsayawa tayi da kukan, kasan kukan tayi domin ko duk duniyar nan ji take babu muryar da ta fiye mata daɗin sauraro da kuma ji face ta sahibin ruhinta Mahmud.
Buɗar bakinta ta ce "Ameen suma ameen masoyina mahaɗin rayuwata, kai ne silar kasancewar murmushi a fuskata, masoyina taurarona madubin dubawana magudanar jini da shaƙar iska na jikina, ya Sahibina sam basu aiki batare da sunji sautin ka ba, kai ne dai ɗaya tak tilo wanda zuciya ta ke so kuma ta aminta dashi, hubbyna bana tunanin akwai wanda a yanzu zata aminta dashi bayan kai, zuciyata gurbin mutum ɗaya kawai ya rage kuma na riga dana samu, wannan ɗan baiwan kuma bakowa bane wanan face kai, kai ne farin cikina zaɓin rai na, muradin ruhina, love of my life."
"Masha Allah Alhmdulillah dukan yabo da godiya su tabbata ga Allah s.w.t mai kowa mai komai wanda ya zaɓa mun ke matsayin abar sona muradin zuciyata ke ce, na ke so kuma na ke ƙauna a raina ina jin cewa bazan iya rayuwa cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba, batare dake ba sameki cikin rayuwata ba, kin zama jigon rayuwata daga lokacin da aka ce baki to nima bani domin rayuwata ba tare dake ba tamkar rayuwa ce a cikin duniyar da babu iska cikinta sam."
"Nai matukar farin ciki da samunka cikin rayuwata, domin ko ka kawo mun canji da dama cikin rayuwata, da basan menene farin ciki ba basan menene baƙin ciki ba, sai da na fara soyayya da kai nasan haka, farkon ganina da kai naji zuciyata ta kamu da matsa nan cin soka, lokaci ɗaya zuciyata, ta aminta da kai, kai ne mai ɗebe mata kewa, ko da yaushe soyayyarka ƙara ruruwa take acikin zuciyata,k**ar anasa mata fetur, ina sonka sanyin idaniyata.
Mahmud numfasawa ya yi ya dafe ƙirjinshi yana faɗin, "ƙan wata kina jin abunda na ke ji kuwa cikin ƙirjina?"
"Na'am yayana a'a sai ka faɗa" ya ce, "ƙan wata kenan wallahi ji nake zuciyata tana dakan uku-uku k**ar zata tsarga ƙirjina ta fito waje haka nake ji"
"Ayyah yayana sannu, nima dan baka san yadda nakeji ba shiyasa, ni da kai abu guda ne shiyasa nima nake jin abunda ka ke ji cikin ƙirjinka, kawai ka rigani faɗi kayi yayana" kallon so da ƙauna s**ai wa junansu tare da sakin murmushi mai ratsa zuciya.
Numfasawa s**ai tare da sauke ajiyar zuciya, koma satar kallon junansu s**ai, suna murmushi.
Mahmud ya ce, "ƙan wata" ta ce "na'am" ya ce mata, "ƙan wata kinga dai yadda sauyi da kuma ƙaddara rayuwa yadda ta ke ta yi damu, bana son kina damun kanki ki kwantar da hankalinki insha Allah ke tawa ce har abada insha Allah"
"Ameen suma Ameen yayana Allah ya tabbatar mana da hakan, da zanfi kowa farin ciki da hakan yayana karka so yanzu kaji yadda nakeji yayana.
"Ƙan wata ina sonki ina son kasancewa a tare dake kina ɗebe mun kewa, zuciyata taki ce ke ce ta ke muradi."
"Nima haka yayana ina sonka, ina ƙaunarka kai ne makusancin ruhina,ina jinka a ƙalbeenah masoyina gaskiya kai ne gwani na kana burgeni da daɗadan kalaman ina sonka ruhina ka zamo mun garkuwata, kai ne lin zamina jani muje" tana gama faɗin haka ta miƙo mai hannuwata tana mai nuni ya jata kunya ce ta ka mata.
Ganin hakan ya saka shi yin murmushi ba shiri, abun dariya dariya ya bashi yana faɗin, "ke koh?" ta ce, " I'm so sorry yayana ban so hakan ya ɓata maka rai, ni nayi hakan ne saboda muyi wasa da dariya."
"No ba wani abu ƙan wata karki damu ni baki mun komai ba kawai dai..."
"Uhmm yayah! Kawai dai me faɗa mun mana kani yayana"
"Toh shikenan naji zan faɗa miki, amma dafatan idan na faɗa miki zaki murmushi"
Ta ce "Eh yayana zanyi abunda ka ke so wallahi yayana ko kuka ka ke so nayi zanyi yayana matuƙar hakan shinenan zai faranta maka yayana, ina son ka sani cewa yayana, ina sonka fiye da yadda nake son kaina."
"Nasan da haka ƙan wata, k**ar nima kenan yadda na ke sonki fiye da yadda na ke son kaina"
Share
Comments
Fisabilillahi
07055852908
★★★★★★★★★★★★★
FARIN JINI Writer's Association Local service
13/02/2022
Muna yiwa kowa barka
Click here to claim your Sponsored Listing.