Rismawy Islamic Natural Herbs

Rismawy Islamic Natural Herbs

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Rismawy Islamic Natural Herbs, Health/Beauty, Ile-Ife.

ASSALAMU ALAIKUM

Barkan ku da zuwa zauren *RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS*

Za mu rika yin bayanin amfanin wasu abubuwan da muke da su a gida tare da maganin da suke yi da izinin ALLAH a bisa tsarin

02/09/2023

SHAWARA {130}

"Idan mutum ya tsinko wannan ganyen mai suna "KING GRASS" "MAI FARIN KAI" ya rika gogawa a goshinsa yin hakan yana maganin kowane irin ciwon kai da yaradar ALLAH, kuma idan mai ciwon ido ya matse shi yana diga ruwan a idonsa da Yardar Allah zai samu lafiya."

✍🏻 Abu Nu'aym Rismawy

31/08/2023

ZUWA GA MASU FAMA DA INFECTION

Ya zama wajibi ga dukkanin jinsin mace da namiji su rika nuna kulawa matuka wajan daukar matakai da shawarwari domin gujewa kamuwa da kowanne irin nau'i na ciwon Sanyi wanda akafi sani da Infection wanda yanzu yazama ruwan dare a al'ummar mu.

Jikin mace yana da saurin daukar cutar sanyi na Infection a ko wane irin yanayin da ake iya daukar cutar sanyin, shi yasa ake son duk mace akai akai ta rika tafasa GANYEN RAIHAN ( Doddoya/ Scent Leaf) da jar kanwa yar kadan tana shan kofi daya safe da dare idan ya huce kadan kuma tana wanke gabanta da shi ko ta rika zama/tsuguno a cikinsa musamman ga masu fama da warin gaba ko zubar farin ruwa ko wani kalar ruwa na rashin lafiya daga al'aurar su ko ma dai duk wata alama ta matsalar sanyin Infection.

Za a iya kara kanunfari ga mai bukatar haka, kuma yin hakan zaifi bayar da fa'idah kwarai da gaske cikin ikon ALLAH.

Yin amfani da wadan nan kayan hadin yana da kyau matuka ga masu fama da matsalar sanyi su rikayi akai-akai kuma idan ma lafiyarku kalau za ku iya yinsa a matsayin riga-kafi, In Sha ALLAHu duk mai yin haka za ta samu kariya daga cutar sanyin Infection ko wanne iri ne da Yardar Allah. Ba wai iya mata ne kadai za su sha ba har mazan su ma za su iya sha.

GANYEN RAIHAN da Larabci ko DODDOYA da hausa ko EFIRIN da yoruba, ba wai wani boyayyen ganye bane a kudu da arewacin kasar nan ba, ana iya samun sa a duk inda yake fitowa musamman ma yanzu Lokacin damuna ne yana yawa sosai, kuma yana da matukar kamshi sosai ko wucewa kayi ta kusa da shi za ka ji shi yana kamshi sosai b***e kuma ka taba shi ko ka sunsuna shi, shiyasa turawa ke kiransa da Scent Leaf.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine

31/08/2023

AMFANIN RUWAN ZAFI DA ZUMA

Idan ka samo ruwan zafi kimanin Kofi 1 ka sanya zuma babban cokali 1 a cikin ruwan zafin, bayan ka juya shi sai ka shanye gaba daya da safe kafin kayi karin kumallo (Breakfast).

Yin hakan yana da matukar amfani ga lafiyar mu sosai kadan daga ciki su ne kamar haka:

1- Yana magance matsalar Makogwaro/makoshi da yardar Allah.

2- Yana magance matsalar Tari da matsalar sanyin dake jikin mutum musamman ma a kirji da yardar Allah.

3- Yana karawa zuciya lafiya da Yardar Allah.

4- Yana rage Qiba da tumbi da Yardar Allah.

5- Yana rage kitsen dake jikin mutum da Yardar Allah.

6- Yana gyara matsalolin dake tattare da hanjin cikin mutum da yardar Allah.

7- Yana narkar da majinar dake dauke da bacteria ko kwayar cuta da yardar Allah.

8- Yana inganta lafiyar zirga-zirgar jini da yardar Allah.

9- Shan ruwan dumi tare da zuma yana gyara fata yasa fatar mutum tayi kyau sosai.

10- Idan aka kara da lemon tsami Yana matukar kawar da kitsen dake jikin hanta, kuma yana da matuka amfani ga masu fama da ciwon Hepatitis A/B da C.

_"Wannan kadan kenan daga cikin amfanin shan zuma da ruwan zafi, idan kacigaba da amfani da haka kullum da safe kafin kaci abinci za kaga wani amfanin a tattare da jikinka wanda ma ban ambaceshi anan ba da Yardar Allah."_

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine

31/08/2023

AMFANIN DANYAR KUBEWA GA MATA

Kubewa tana karawa mata ni'ima, ko da ace kuwa mace ta bushe to idan har ta dage da amfani da ita tana samun mafita ta banmamaki da yardar Allah.

Kubewa tana daga cikin abincin da yake karo ovulation (kwayayen halitta) din mace ga wacce take da matsalar kwayayen halitta, har ma ya lullunka kwayayen wato ( Hyper ovulation) tayadda za suyi yawa sosai, kuma hakan ka iya sanyawa cikin ikon Allah a iya samun haihuwar yan biyu ( Twins) kamar yadda masana kimiyya s**a fadi.

Kubewa tana dauke da sinadaran ZINC, FOLATES, IRON da kuma VITAMIN-B wadanda duk suna da amfani ga bincika da kuma jin dadin mu'amilar saduwar aure.

_YADDA AKE AMFANI DA ITA_

1- Za a iyayin miyar danyar kubewa amma yadda baza a barta ta dahu sosai ba har yaukinta ya ragu ko yagushe ba, anaso ne a cita ko a shata da yaukinta sosai.

Shima ganyenta ana iyayin miya da shi kamar yadda binciken yatabbatar shima yana da amfani sosai kamar yadda Kubewar take da shi. Allahu A'alam.

2- Ko kuma a samu kamar kwayar kubewa 5 sai a yayyanka kubewar sala-sala sai a sanya ta a cikin roba/gora a zuba ruwan sanyi a ciki da dare sai ya kwana a jike, a cire kubewar a cikin ruwan sai a shanye ruwan da safe.

Mace mai bukatar kwayayen halitta za tayi amfani da kubewar ne bayan ta yi tsarki daga Al'adarta za ta dau kwanaki 2 zuwa 3 tana amfani da Kubewar.

Mai matsalar ni'ima kuma ko dandanon saduwar aure to za ta rika shan miyar Kubewar ne akai akai, wasu ma idan auren diyarsu ya kusa kamar sati daya sai duk satin ba miyar da za ta rika sha sai miyar Kubewa.

_GARGADI_

Ba wai na ce kubewa tana sanya haihuwa bane, ko tana sanyawa a haifi Twins ba a'a. Allah ne mai bayar da haihuwa ga wanda yaga dama kuma shike bayar da kyautar yan biyu ga wanda yaga dama, amma akwai sabubba na ilimi wanda likitoci ke bayaninsu ko a al'adance amma duk wannan sabubban ba zasu taba iya tabbatar da abinda Allah bai tabbatar ba.

Tabbas kubewa tana da amfani wajan boosting din kwayayen halitta, tana magance matsalar Infertility, tana karawa mata ni'ima da yardar Allah. WALLAHU TA'ALA A'ALAM.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine

31/08/2023

HADI MAI AMFANI GA LAFIYAR MU

Ka samo wadan nan abubuwan kamar haka:

1- Dabino guda 7

2- Ya'yan Habbatus sauda ( ba garinta ba) karamin cokali 1

3- Ζ³aΖ΄an Habbah Rashad (Ba garinta ba) karamin cokali 1.

4- Garin Kurkum/kurkur rabin karamin cokali.

5- Garin citta karamin cokali 1

Idan ka hada Habbatus sauda, Habbah Rashad, citta da kuma kurkum a wuri daya, sai ka dauko dabinon guda 7 kowanne ka bare shi biyu, sai ka barbada wadancan hadin a cikinsa sai ka cinye su gaba daya da safe kafin kayi karin kumallo da kamar awa Ι—aya ko sama da haka.

Ka dau tsawon sati kana aikata haka sai kaga yadda jikinta zai koma, ko kaje asibiti a kara auna lafiyarka na tabbata za kaga sauyi a jikinka cikin IKO DA YARDAR ALLAH.

*AMFANIN ME YAKE YI ?*

1- Yana magance duk wata matsalar dake tattare da kasusuwa wanda sanyi ke haddasawa.

2- Yana magance matsalar ciwon baya (Na bangaren sanyi).

3- Yana magance Matsalar ciwon guiwa.

4- Yan magance matsalar duk wani sanyin da yake damun kasusuwa.

5- Yana kawar da kitsen da yake jikin hanta, wanda yake kawowa hanta matsala har ta kamu da Hepatitis.

6- Yana rage Sinadarin Cholesterol ( Wanda yake haddasawa wasu kiba).

7- Ba iya nan kenan ba, wannan hadin yana matukar magance matsalolin dake damun jikin dan Adam da dama, yana da wasu amfanin dabam wanda sai har idan kafara amfani da hadinne za ka fahimci abubuwa da dama dangane da wannan hadin.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine

31/08/2023

MAN ZAITUN DA TAFARNUWA

Idan ka samu tafarnuwa ka bare bawon gaba daya, sai ka sanya tafarnuwar a cikin wata kwalba mai dauke da MAN ZAITUN a ciki sai ka rufe.

Ka barshi a rufe har tsawon sati biyu, sai ka rika shan babban cokali Uku (3) kullum da safe kafin kaci abinci.

Wannan hadin yana magance wasu cutuka da matsaloli kamar haka:

1- Yana tace jini, da Yardar Allah.

2- Yana wanke Hanta daga kitse ko wata matsala, da Yardar Allah.

3- Yana kawar da tsakuwar dake cikin QODA da yaradar ALLAH.

4- Idan har mutum yana shanshi to yana magance matsalar basur idan kuma basur din mai tsiro ne sai arika shafa shi a dubura.

5- Idan matsalar ciwon gabobine ko sanyin kashi sai a rika shafa shi a wurin da yake da matsalar.

6-Masu fama da matsalar zubewar gashi sai su rika sha kuma suna shafa wannan hadin a gashinsu

7- Idan masu fama da matsalar LOW S***M COUNT suna shan wannan hadin to da yardar Allah za su iya rabuwa da Matsalar.

8- Kuma yana magance matsalar Infertility ( wacce take iya sanadiyyar samun jinkirin haihuwa) da yardar Allah ga maza da mata.

Wasu da dama sunyi amfani da hakan kuma Allah ya sa andace.

_Tafarnuwar ta kasance kamar adadin yawan rabin kwalbar Man Zaitun din. Misali idan Man zaitun din 1Litre ne, to anaso yawan tafarnuwar takasance rabin lita (1/2 Litre). Allah yasa mun gane._

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine

Telegram: Contact @Rismawymedicine 12/06/2023

*MATSALAR RASHIN RUWAN NONO GA MAI SHAYARWA*

1- A samu RIDI a tsaftace shi sosai sai a hada shi da MAN SHANU da GARIN HULBA da kuma ZUMA a kwaba su sai mace ta rika sha akai akai, in Sha ALLAHu wannan hadin yana sabbaba Allah yasamar da ruwan nono mai kyau mai dauke da sinadaran da suke karawa yaro lafiya da kuzari cikin yardar ALLAH.

2- A samu RIDI sai ayi garin shi a kwaba shi da MAN SHANU sai a rika shafawa a nonon in Sha ALLAHu ruwan nono zai samu da yaradar ALLAH, Wadannan mujarrabi ne.

A hada su gaba daya 1-2 ayi amfani da su na sha din da an shafawa ... Allah yataimaka.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:

Telegram: Contact @Rismawymedicine

Telegram: Contact @Rismawymedicine 12/06/2023

*GANYEN GWAIBA🍐 DA GANYEN ZOGALE 🌿*

Ga wadanda ke fama da matsalolin jiki kala-kala daga wannan sai wannan.

Ga masu fama da matsalar sanyi.

Ga masu fama da matsalar karancin ni'ima ga mata da kuma rashin karfin maza.

Ga masu fama da matslar Kowa s***m count.

Ga masu fama da matsalar hawan jini

Ga masu fama da matsalar Diabetics

Kusamo GANYEN GWAIBA da GANYEN ZOGALE sai ku wanke kuma ku tsaftace su sai a sanya yar jar kanwa kadan a ciki, sai a tafasa su, sai a tace a rika sha safe da rana da dare Kofi 1, ko ma dai mutum yazamar da shi tamkar ruwan shanshi har tsawon kwanaki 5 ko sati 1.

Za ku iya sanya zuma a ciki amma Banda mai fama da Diabetics.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:

Telegram: Contact @Rismawymedicine

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS 20/05/2023

*_KADAN DAGA CIKIN WASU AMFANIN DA GANYEN BAURE (TEEN) KEYI A JIKIN MU_*

Ka samo ganyen BAURE sai ka tafasa shi sannan ka tace shi ka rika shan kofi 1 a sanya zuma ko a sha shi haka ba komai a kullum safe da yamma, yin hakan yana da matukar amfani ga lafiyar mu kamar haka:

1- Yana karawa zuciya lafiya kuma yana daidaita jini ta yadda Allah zai kubutar da kai daga ciwon hawan jini da ciwon Diabetic da izinin Allah.

2- Yana ragewa mutum nauyin jiki, kuma ya dakatar da sinadaran da suke karawa mutum qiba, da izinin Allah.

3- Yana taimakawa wajan narkar da abinci ga wanda yake fama da matsalar rashin narkewar abinci a cikin cikinsa, da izinin Allah.

4- Yana taimakawa maza wajan sanya iyalansu farin ciki a yanayinsu na ma'aurata, da Izinin Allah.

5- Yana karawa kasusuwan mutum karfi da kwari, da izinin Allah.

6- Yana karawa idanuwa lafiya musamman ma matsalar yanar ido ga wadanda s**a manyanta har ma ga wasun su, da Izinin Allah.

7- Yana bayar da kariya daga kamuwa da cutar Daji (Cancer), kuma yana karawa fata lafiya, da izinin Allah.

Wannan kadan kenan daga cikin abinda za mu iya kawowa al'umma dangane da amfanin itaciyar nan mai tarin albarka ta Baure ( Teen).

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullubemu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS ASSALAMU ALAIKUM

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS 20/05/2023

*WASU DAGA CIKIN AMFANIN TAZARGADE*

Tazargade tana daya daga cikin dadaddun ciyawoyin da ake amfani da su a bangarori mabambanta na kiwon lafiya, kuma ana sanyata a ruwan wanki domin fitar da karni ko wari da dai sauran su.

Yanzu insha ALLAH za mu kawo muku wasu daga cikin amfanin da takeyi ga lafiyar mu, daga cikin abubuwan da take magancewa da yardar Allah su ne kamar haka:

1- Zazzabin cizon sauro, ko duk wani zazzabi na (Maleria).

2- Yawan ji da yin Amai

3- Masu matsalar Cutukkan da ke samun hanji, ko ciwon ciki.

4- Masu matsalar ciwon shanyewar barin jiki.

5- Mau matsalar ciwon Qoda

6- Tana daidata jinin al'ada.

7- Idan aka sanyata a ruwa aka karanta Ayoyin Alqur'ani aka sha kuma ana wanka da shi, tana magance matsalar Sihiri, Kambun-baka, Mayu, hassada da Shafar Shedanun Aljanu. Da yardar Allah.

8- Idan jinin al'adar mace baizo ba na tsawon lokaci, idan tayi amfani da Tazargade insha ALLAH zaizo.

9- Taba magance ciwon kan yara da kuma zazzaΙ“in yara, idan aka sanyata a ruwa ( normal mara zafi) akayi musu wanka da ita. Da yardar Allah.

*YADDA AKE AMFANI DA ITA*:

Ana dafata ne kamar yadda ake dafa shayi ( Tea) a sanya zuma ko s**ari ( amma mai fama da ciwon Diabetics ba sai ya sa komai ba a haka zaisha), sai a rika shanta da dumi kamar shayi safe da yamma.

*SHIN KOWA NE ZAI IYA SHA?*

Eh kowa zai iya sha amma banda wadan nan:

1- Mai ciki ( Don zata iya haifar mata da matsalar lalacewar cikin ko da kuwa ya kai wata nawa).

2- Mai shayarwa
3- Mai ciwon farfadiya
4- Sai Ζ™ananan yaran da basu wuce Shekarau 2 ba.

*SHANTA YANA DA IYAKA NE ?*

Eh ana so mutum yarika shanta a ko da yaushe amma kar ya kuskura ya haura sati 4 yana shanta a jere. ALLAHU A'ALAM.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS ASSALAMU ALAIKUM

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS 06/05/2023

MAI MATSALAR WASWASI GA MAFITA DA IZININ ALLAH

1- Ka samo garin Qustul Hindi Ζ™aramin cokali 1 ka sanya shi a ruwa kofi 1, sai ka garwaya shi ya garwayu sosai, sai ka karanta masa Ayoyin Alqur'ani Kamar su *"Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Ikhals, Falaqi da Nasi"* , sai ka riqa sha kuma kana shaqawa a hancin Ka (irin shaqa ruwan da kakeyi a alwala).

2- Ka rika karanta wannan Addu'ar sau 7 da safe da yamma ma sau 7:
"حسبي Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ω„Ψ§ Ψ₯Ω„Ω‡ Ψ₯Ω„Ψ§ Ω‡Ωˆ ΨΉΩ„ΩŠΩ‡ ΨͺΩˆΩƒΩ„Ψͺ ΩˆΩ‡Ωˆ Ψ±Ψ¨ Ψ§Ω„ΨΉΨ±Ψ΄ Ψ§Ω„ΨΉΨΈΩŠΩ…."

"HASBIYALLAHU LA ILAAHA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHIL AZEEM."

- Yawaita yin ISTIGFAARI a ko da yaushe ba tare da qayyade adadin da zaka yi ba.

- Karanta AYATUL KURSIYYU a bayan kowace sallar farillla da lokacin da za kayi bacci.

- Yawaita karanta Alqur'ani a hali ko yanayin da shari'a ta amince.

- Karanta suratul Baqara da suararonta a kullum ko da baka karance ta dukkanta ba.

- Yin alwala a kullum idan zaka kwanta bacci, ko da ma'aurata sun sadu da junansu basu samu damar yin wanka da daren ba, su samu suyi alwala ko da sabi 1 ne ba sai sabi 3 ba.

- Idan kazo alwala kadaina yin almubazzaranci da ruwan, ka riga dibar iya wanda zaka iya amfani da shi.

- Adaina sauraron kade kade da wake wake.

- A rika yawaita sauraron Alqur'ani.

- Karanta Suratul Ikhlasi, falaqi da Nasi sau uku safe da yamma, da sauran Azkaar na safe da yamma.

- A rika shiga cikin jama'a, mutum ya daina kebewa shi kadai.

Kuma idan anga sauyi kar a daina yin azkaar din, acigaba da yinsu.
Insha ALLAHu za ku daina yin waswasin cikin iko da yardar Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS ASSALAMU ALAIKUM

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS 06/05/2023

ZUWA GA MASU FAMA DA CUTAR ASTHMA ( ASMA)

Cutar Athsma itama daya ce daga cikin sauran cututtukan numfashi wadanda yara da manya ke fama da ita.

Abinda mai fama da cutar Athsma yakamata ya nema saboda samjn saukinta ko ma rabuwa da ita gaba data cikin iko/da yardar Allah su ne kamar haka:

1- Zuma

2-Garin sassaken marke

3- Tafarnuwa( a markada ta)

5-Garin Citta

6- Garin Habbatus saudah.

Sai a kwaba su wuri guda suyi kauri sosai (amma a sanya zumar da dan yawa), sai a rika dibar cokali 2 ana sanyawa a ruwan dumi Kofi 1 madaidaicin Kofi, ana sha safe da rana da daddare, kuma a rika lasar mai kaurin akai-akai, adau kamar tsawon sati 2 ana amfani da ita sai aje aga likita.

Karamin yaro kuma idan ya fara cin abinci sai arika bashi karamin cokali ( wacce aka sirka da ruwan dumin, kuma ana lasa masa mai kaurin kadan kadan a bakinsa), Idan kuma bai fara cin abinci ba sai a rika lasa masa kadan a bakinsa kuma idan ana shayar da su sai itama uwar ta rika shan hadin manyan da yake a sama.

Insha Allahu za Ku samu natija a wannan hadin.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🀲🏻)

Domin karin bayani:
πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

WhatsApp
+2348031542026

Gmail:
[email protected]

Telegram Channel:

RISMAWY ISLAMIC NATURAL HERBS ASSALAMU ALAIKUM

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Ile-Ife?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Ile-Ife