Wase Connect
I'm by name Umar Salihu Ahmad,based at Wase Plateau State.And study at ASCOE,Azare,Bauchi State.
14/09/2026
Wannan shine gwarzon shekara shine matashi dan kunan farin wake dan baza ace bakin wake ba wanda yabada rayuwarsa dan ANNABI bakamarmu dakawai rubutawa mukeyi zamubayarba shikam yariga yabayar shikam yajidadi yayi shahada abunsa 🙌🙌🙏🏻
14/09/2026
DA DUMI-DUMI: Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya bayyana muhimman manufofinsa guda 12 da ya ce zai aiwatar idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Atiku ya bayyana manufofin ne a ƙarƙashin tsarin “Rescue, Revive and Restore Nigeria” — wato ceto, farfaɗo da dawo da martabar Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tattalin arziki, ilimi, tsaro, noma, wutar lantarki, lafiya da tsarin mulkin ƙananan hukumomi.
Ga muhimman manufofin da ya gabatar:
1. Mayar da tallafin man fetur:
Ya yi alkawarin dawo da tallafin man fetur da aka tsara, domin rage tsadar sufuri da kuma sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya matsin rayuwa da hauhawar farashin kayayyaki.
2. Sake duba bashin NELFUND:
Ya ce za a sake nazarin tsarin rancen kuɗin karatu na NELFUND, tare da duba yiwuwar afuwa ga wasu basuss**a, bisa hujjar cewa ɗaliban Najeriya sun cancanci tallafin karatu da ilimi mai sauƙin samu, ba bashin da zai jefa su cikin matsala ba.
3. Ƙarfafa cin gashin kan ƙananan hukumomi:
Atiku ya yi alkawarin aiwatar da hukuncin Kotun Ƙoli kan cin gashin kan ƙananan hukumomi, domin tabbatar da cewa kuɗaɗen da s**a dace da ƙananan hukumomi sun isa gare su kai tsaye kuma a yi amfani da su wajen ayyukan ci gaban al’umma.
4. Farfaɗo da tashoshin jiragen ruwa na Gabas:
Ya ce zai farfaɗo da haɓaka tashoshin jiragen ruwa na Port Harcourt, Calabar da Warri, tare da inganta ci gaban Uyo Deep Sea Port, domin ƙarfafa kasuwanci da sufuri ta teku.
5. Sake buɗe iyakokin ƙasa:
Ya yi alkawarin sake buɗe iyakokin Najeriya domin bunƙasa kasuwancin halal tsakanin ƙasashe, tallafa wa ‘yan kasuwa na gaskiya da kuma ƙarfafa harkokin kasuwanci a yankin.
6. Gyaran tsarin wutar lantarki:
Atiku ya ce zai sake duba tsarin bangaren wutar lantarki da kuma rabe-raben kuɗin wuta, domin kawo ƙarshen abin da ya kira cajin kuɗaɗen wuta cikin nuna bambanci da kuma rage wa ‘yan Najeriya tsadar wutar lantarki.
7. Tallafa wa matasa da mata:
Ya gabatar da shirin samar da dala biliyan 10 domin tallafa wa kamfanonin matasa da harkokin kasuwanci, tare da ƙara ba matasa da mata dama a nadin mukaman gwamnati da kuma fannonin tattalin arziki.
8. Ƙarfafa tsaron ƙasa:
Ya yi alkawarin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro, inganta jin daɗinsu, yaƙi da cin hanci a cikin hukumomin tsaro, amfani da sabbin fasahohin leƙen asiri da na aiki a filin daga, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da ƙasashen makwabta.
9. Mayar da ‘yan Najeriya gonaki:
Atiku ya ce zai inganta tsaron manoma, rage kuɗaɗen samar da amfanin gona, farfaɗo da harkar noma da kuma faɗaɗa hanyoyin samun tallafin kuɗi ga manoma da ‘yan kasuwa.
10. Gyaran harkar lafiya:
Ya yi alkawarin sake fasalin tsarin kiwon lafiya, faɗaɗa damar samun ingantacciyar lafiya mai sauƙin kuɗi, tare da magance ƙarancin ma’aikata, inganta albashi da kuma walwalar ma’aikatan lafiya.
11. Ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi iko:
Ya ce zai sake fasalin tsarin rabon iko tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi, ta hanyar duba Exclusive da Concurrent Legislative Lists, domin bai wa jihohi da ƙananan hukumomi ƙarin nauyi da damar gudanar da ayyukansu, yayin da gwamnatin tarayya za ta mayar da hankali kan abubuwan da s**a shafi ƙasa baki ɗaya.
12. Aiwatar da Oronsaye Report:
Atiku ya ce zai aiwatar da shawarwarin Rahoton Oronsaye domin kawar da almubazzaranci, maimaita ayyuka tsakanin hukumomi da kuma rage guraben da ke haifar da cin hanci, tare da inganta ayyukan gwamnati da samar da ingantaccen tsarin gudanarwa.
Ya ce manufofin nasa sun kasance wani ɓangare na shirinsa na “ceto, farfaɗo da dawo da Najeriya” idan aka ba shi damar jagorantar ƙasar bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
KBC Hausa
14/09/2026
14/09/2026
💙
14/09/2026
Just Distance.....
14/09/2026
Ba mu zauna tare da Manzon Allah ﷺ ba.
Ba mu ji muryarsa da kunnuwanmu ba.
Amma mun karɓi saƙonsa, mun gaskata shi, kuma muna ƙaunarsa.
Ya Allah, kada Ka hana mu kasancewa tare da shi a Aljanna. 🤲
Young Sheikh Zaria Zakeer M.S Ali
14/09/2026
Wani matashi mai suna Aminu Usman ya fito ya musanta zargin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa shi ne matashin da ya kaiwa babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Musa Ayuba Lukuwa, farmaki a masallaci.
Aminu ya bayyana cewa hoton da ake yaɗawa hotonsa ne, amma ya ce ba shi ne mutumin da ya kaiwa malamin farmaki ba.
Ya ce shi masoyin Sheikh Musa Lukuwa ne na gaskiya, kuma yana yawan wallafa bidiyon karatunsa a shafinsa na Sakkwatawan Shehu, inda a wasu lokuta yake amfani da hoton da s**a taɓa ɗauka tare.
Muhimmin Bayani
A cewarsa, bayan faruwar harin a masallacin malamin, ya yi posting game da lamarin tare da amfani da hoton nasa kamar yadda ya saba yi a baya.
Sai dai daga nan ne wasu mutane s**a fara yaɗa hoton, suna cewa shi ne matashin da ya yi ƙoƙarin kashe malamin.
Aminu ya jaddada cewa:
“Wallahi ba ni ba ne. Wallahi ba ni ba ne.”
Ya kuma yi kira ga jama’a da su daina yaɗa zargin da ba a tabbatar da shi ba, yana mai cewa irin wannan zargi na iya cutar da mutum sosai.
Abin da ya kamata ku sani
A halin yanzu, abin da Aminu Usman ya bayyana shi ne musun zargin da ake yi masa. Don haka ya dace jama’a su yi taka-tsantsan wajen yaɗa hotuna ko bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba.
Gambiza TV — Muryar Gaskiya da wayar da kai.
Muna kawo muku muhimman labarai daga Arewa da Najeriya cikin gaskiya da fahimta.
Ku ci gaba da bibiyar Gambiza Tv domin samun sabbin bayanai, kuma ku raba wannan rahoto domin mutane su san cewa ana samun musun wannan zargi.
Tambaya: Me kuke ganin ya kamata a yi kafin a danganta hoton mutum da wani babban laifi?
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Address
Jos
802