RUNS MAN MARJZ

RUNS MAN MARJZ

Share

Good news

Photos from RUNS MAN MARJZ's post 12/07/2026

🚨 LABARI MAI DAƊI: Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 15 Daga Hannun Ƴan Ta’adda A Kebbi

Dakarun Operation FANSAN YAMMA na Sashi na 2 sun samu gagarumar nasara bayan sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su a yankin Marge, ƙaramar hukumar Danko-Wasagu ta jihar Kebbi.

Rahotanni sun ce an kai wannan samame ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan motsin ƴan ta’addan. Da s**a hango isowar dakarun soji, maharan sun tsere cikin gaggawa tare da barin waɗanda s**a sace.

An tabbatar da cewa an haÉ—a dukkan waÉ—anda aka ceto da iyalansu cikin koshin lafiya.

Muna addu’ar Allah Ya ci gaba da kare dakarun tsaronmu, Ya ba su ƙarfi da nasara wajen yaƙi da ta’addanci tare da dawo da zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.

12/07/2026

AN KAWO ƘARSHEN SANI YELLOW! Fitaccen Shugaban ’Yan Bindiga Ya Mutu a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaro na haɗaka sun kashe fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Sani Yellow, a wani samame da aka kai bayan samun sahihan bayanan sirri.
An ce an yi masa kwanton ɓauna ne yayin da ake zargin ya je karɓar kuɗin fansa da kuɗaɗen shanun da aka sace. Bayan kashe shi, wasu daga cikin dakarun sun yi murnar nasarar da s**a samu kan ɗaya daga cikin manyan jagororin ’yan bindigar da s**a addabi yankin.
Sani Yellow na daga cikin waɗanda ake zargi da jagorantar hare-hare, sace mutane domin neman kuɗin fansa, satar dabbobi da tilasta dubban mazauna karkara barin gidajensu a ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru na Jihar Zamfara.

Haka kuma, jami'an tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan domin hana duk wata yiwuwar harin ramuwar gayya daga sauran 'yan ƙungiyarsa.

12/07/2026

Murna ta ɓarke yayin da, jami'an tsaro s**a kashe fitaccen jagoran ’yan bindiga Sani Yellow a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun tsaro na haɗaka da ke taimakawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma sun kashe wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da aka fi sani da Kachalla Sani Yellow a Jihar Zamfara.

Majiyoyin tsaro sun shaida cewa an kashe Sani Yellow ne bayan wani shiri na musamman da aka gudanar bisa bayanan sirri da aka samu daga mazauna yankin, inda aka yi masa kwanton ɓauna yayin da ake zargin ya je wata kasuwa domin karɓar kuɗaɗen shanun da aka sace da kuma kuɗin fansa daga wasu da aka yi garkuwa da su.

Rahotannin sun ce bayan kashe shi, wasu daga cikin dakarun haɗakar sun ja gawarsa a kan babur yayin da suke gudanar da abin da s**a kira murnar nasarar da s**a samu kan ɗaya daga cikin shugabannin ’yan bindigar da s**a fi addabar yankin.

Majiyoyi sun bayyana cewa rundunar haɗakar ta ƙunshi masu sa-kai daga al’umma da kuma wasu tsofaffin mayaƙan Boko Haram da s**a tuba, waɗanda ke aiki tare da jami’an tsaro a wasu yankunan domin tattara bayanan sirri da kuma kai farmaki kan ƙungiyoyin ’yan bindiga.

An bayyana Sani Yellow a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin ’yan bindiga da ke gudanar da hare-hare a dazukan ƙananan hukumomin Anka, Bukkuyum da Maru da wasu sassan Jihar Zamfara.

Ana zarginsa da jagorantar hare-haren da s**a yi sanadin rasa rayuka, sace mutane domin neman kuÉ—in fansa, satar dabbobi da kuma tilasta dubban mazauna karkara barin muhallansu.

Wasu majiyoyin al’umma sun kuma yi zargin cewa ƙungiyar tasa na cin zarafin waɗanda aka sace, ciki har da mata, musamman idan iyalansu sun kasa biyan kuɗin fansa.

Sani Yellow na da alaƙa da marigayi Kachalla Yellow Danbokolo, wani shahararren shugaban ’yan bindiga da aka ruwaito an kashe a shekarar 2025 tare da sama da mayaƙa 170 a wani samame da dakarun sa-kai na Yankin Shinkafi s**a kai.

Jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan sa ido a yankunan da lamarin ya sha

07/07/2026

GWAMNATIN TINUBU TA FARA BINCIKEN META, GOOGLE, X DA KAMFANONIN AI KAN ZARGIN TAUYE HAƘƘIN KAFAFEN YAƊA LABARAI NA NIJERIYA

Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta umarci Hukumar Kula da Gasa da Kare Haƙƙin Jama'a Masu Sayayya ta Tarayya (FCCPC) da ta gudanar da bincike kan wasu manyan kamfanonin fasaha na duniya bisa zargin tauye gasa, amfani da labaran kafafen yaɗa labarai ba tare da izini ba, da kuma wasu halayen kasuwanci da ake zargin ba su dace da dokokin Nijeriya ba.

Binciken zai shafi manyan kamfanonin fasaha da s**a haɗa da Meta, Alphabet (Google), X, da kuma wasu dandamalan fasahar ƙirƙirar basirar wucin gadi (Generative AI) da ke gudanar da ayyuka a Nijeriya.

Daraktan Harkokin Hulɗa da Jama'a na FCCPC, Ondaje Ijagwu, ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan ƙorafin haɗin gwiwa da Ƙungiyar Kafafen Yaɗa Labarai ta Nijeriya (NPO) ta gabatar wa Fadar Shugaban Ƙasa. Ƙungiyar ta haɗa da NPAN, NUJ, BON da GOCOP.
A cewarsa, Ministan YaÉ—a Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya isar da umarnin gwamnatin tarayya ga FCCPC domin fara gudanar da binciken.

Mataimakin Shugaban FCCPC kuma Babban Darakta, Mista Tunji Bello, ya ce hukumar za ta gudanar da binciken cikin adalci, ba tare da nuna son kai ba, tare da bai wa dukkan ɓangarorin damar gabatar da bayanansu kafin a yanke hukunci.

Ya bayyana cewa manufar binciken ita ce tantance ko akwai take dokokin gasa da kare haƙƙin masu sayayya, ko kuma wasu halayen kasuwanci marasa adalci da s**a shafi amfani da labarai da sauran abubuwan da ke ƙarƙashin kariyar haƙƙin mallaka wajen horar da tsarin Generative AI ba tare da izinin masu su ba.

Haka kuma hukumar za ta binciki ko akwai rashin daidaito a mu'amalar kasuwanci tsakanin manyan kamfanonin fasaha da kafafen yaÉ—a labarai na Nijeriya, musamman game da biyan diyya ko cimma yarjejeniyar amfani da labaran da suke samarwa.

A baya dai, FCCPC ta taɓa hukunta kamfanin Meta kan wasu laifukan da s**a shafi take dokokin kare haƙƙin

29/06/2026
Photos from RUNS MAN MARJZ's post 29/06/2026
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Tudun Jukun
Kaduna
NASNEWS

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when RUNS MAN MARJZ posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kaduna.