Tsamiya Online Tv

Tsamiya Online Tv

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Tsamiya Online Tv, Health/Beauty, Kaduna.

29/09/2026

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya sallami Rashida Adamu, wadda aka fi sani da Rashida Mai Sa’a, daga mukaminta na Mataimakiya ta Musamman a ofishinsa.

A wata sanarwa da Sh*tu Madaki Kunchi, mai taimaka wa Sanatan kan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a, ya fitar ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2026, ya ce matakin ya biyo bayan zargin Rashida da yin kalaman da za su iya tunzura magoya baya, yi wa jam’iyyar APC zagon ƙasa da kuma cin mutuncin Sanata Barau.

Sanarwar ta ce sallamar na da alaƙa da wani saƙo da ofishin Sanatan ya fitar ranar Lahadi, inda aka zargi wasu mutane da ƙoƙarin kawo cikas ga Barau a siyasar Kano da cikin APC.

Ofishin Sanatan ya kuma yi iƙirarin cewa wasu daga cikin mutanen da ake magana a kai sun taɓa amfana da muk**ai da tallafin Sanatan, kafin daga bisani su koma abin da ofishin ya bayyana a matsayin yunƙurin cutar da shi da jam’iyyar.

Tsamiya Online Tv

29/09/2026

Atiku Abubakar Jama'a Mu Farka, Muceto Kasar Nigeria, Nigeria Tana Bukatar Atiku Abubakar.

Tsamiya Online Tv

28/09/2026

An K**a Matashi Kan Zargin Kashe Mahaifinsa Mai Shekaru 80 da Sanda a Jihar Katsina

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina ta tsare wani matashi mai shekaru 27, Sada Tambai, bisa zargin kashe mahaifinsa mai shekaru 80, Adamu Tambai.

Lamarin ya fito fili ne bayan Hakimin Bindawa ya sanar da jami’an tsaro cewa an gano tsohon Dagacin ƙauyen Mundadu kwance a gaban gidansa ba ya motsi.

Bayan jami’an ’yan sanda sun isa wurin, an garzaya da dattijon zuwa asibiti, inda likita ya tabbatar da cewa ya rasu.

A cewar rundunar, binciken farko ya kai ga k**a ɗan marigayin. Ana zargin Sada ya amsa cewa ya bugi mahaifinsa da sanda a kai, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa.

Kakakin rundunar, Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Asabar, 26 ga Satumba 2026.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ali Umar Fage, ya umarci a miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) domin gudanar da cikakken bincike kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

An kirkiri wannan hoton ne da taimakon Fasahar AI.
Tsamiya Online Tv

28/09/2026

Ruƙayyat Kenan, Matar Auren Da Aka K**a Bayan Wani Magidanci Ya Rasu A Yayin Da Suke Ɗakin Otal Tare A Abuja, Allah Ya Kara Karemuna mutuncin Iyalan Mu, Don Darajar Annabi Muhd S.A.w

Tsamiya Online Tv

28/09/2026

Maigirma Gwamna Comrd. Dr Nasir Idris Kauran Gwandu Babu Abunda Zamuce A Gareka Saidai Godiya Domin Al'umma Talakawa Babu Kalar Amfanuwar Da Bamuyi Ba Da Wannan Mulkin Naka.

Al'umma Dadama Suna Godiya Ga Allah Da Samun Ka A Matsayin Gwamnan Mu Kuma Jagoran Mu Domin Shugabanci Irin Naka Abun Sone Kuma Abun Alfahari Ne.

Fatan Mu Shine Allah Yaƙara Yarje Maka Kadawo Kan Karagar Mulkin Jahar Kebbi Karo Nabiyu Cikin Sauqi.

Tsamiya Online Tv

28/09/2026

Sanata Mohammed Danjuma Goje ya bayyana cewa ba zai goyi bayan zaɓen wasu daga cikin ‘yan takarar jam’iyyar APC ba, yana mai cewa al’ummar Gombe sun san waɗanda s**a taka rawa wajen hana shi sake neman takara a jam’iyyar.

Goje ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan ‘yan takarar Majalisar Tarayya na Akko da Yamaltu-Deba, da kuma takarar Sanata.

A cewarsa, "kunsan waɗanda s**a hana ni takara a APC, saboda haka ban goyi bayan ku zaɓe su ba.”

Sanatan ya kuma bayyana cewa ba lallai ne ya gaya wa al’umma wanda za su zaɓa ba, amma zai iya bayyana waɗanda bai goyi bayan a zaɓe su ba.

Tsamiya Online Tv

28/09/2026
Photos from STV online's post 28/09/2026
28/09/2026

'Yan Bindiga Sun Shiga Gida-Gida Daren Jiya, Sun Sace Mutane da Ba a Tantance Yawan su ba a garin Bungudu.

Harin ya faru ne a jiya 27 ga Satumba, 2026, inda aka bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe Babangida Kuku tare da yin garkuwa da wasu mutane da har yanzu ba a tantance adadinsu ba.

Tsamiya Online Tv

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kaduna?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kaduna