Fadakar wa Ilmantarwa Nishadantarwa
Alhamdulillaah
Murnar mutuwa murnar banza ce wallahi domin kai ma sai Ka ji
06/09/2023
Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un
Allah ya yiwa Sheikh Abubakar Giro Argungu Rasuwa.
Marigayin ya rasu ne bayan jinya da yayi na 'dan lokaci a Birnin kebbi. Za'a masa sallar janaza Gobe alhamis insha Allah. Zamu sanar da lokaci nan gaba.
Fatan alkhairi ga kowa
TALAKA DA MAI MADAFUN IKO
Abin da talakan Nigeria ya kasa ganewa, shine ba ya gaban wani, mai mulki, mai fada aji ko mai madafun iko, walau dan siyasa, basarake ko mai kudi.
Matsalar talaka ba ta taba zama matsalar su ba, idan ka ga sun saurari matsalar talaka to fa ta shafe su ne.
duk lokacin da talaka zai tashi yayi hayagaga don wani mai madafun iko ya yi kuskure dariya suke yi don sun san babu abun da man talaka zai iya yi da ya wuce guna guni. Yanzu na ma talaka yake iya magana ta kafafen sadarwa, a baya ko ina ka ga gidan radio ko jaridar da za ka yi korafi?
misali an samu yaya da daga gidajen masu iko sun yi shigar tsiraici sun yi rawa sun chashe a bainar jama'a, mutan gari s**a ta cecekuce suna Allah wadai amma a zahiri babu abin da ya chanza sai ma karuwa ya dinga yi, aka samu daga gidajen sarautar da suke ikirarin tutar musulunci yayan su da jikokin su ka mayar da shigar banza kamar sunar gidan.
a lokacin da makarantun mu s**a lallace babu kayan aiki babu malamai a lokacin masu madafun iko wadanda alhakin gyara wadannan makarantun ya rataya a wuyansu s**a dinga tura yayansu karatu kashashen waje irin su Ingila, Amurika, kanada, sifain da saifirus, domin su tabbatar maka sun tura in ma baka sani ba, bayan yaran sun kammala karatun sai suyi tattaki irin na jirgi, da duk iyalansu su je su dauki hotuna su watso muku ku gani, irin a kudinku muke wannan hidimar.
To menene abin mamaki don ASUU na yajin Aiki wata bakwai matar shugaban kasa ta turo muku hotunan matar danta ta kammala digiri a turai? to in baka san mai ake nufi ba ana nufin, CHAN TA MATSE MUKU, ko KU KARATA CHAN ko KU CI KAN KU KU SHA BAKIN RUWA.
Ni a ganina wannan ba komai bane akan lokacin da ake tsaka da kashe mutane a Zamfara sokkoto kaduna da katsina, da fes laidi ta dinga turo mana hotunan shagulgulan bukin yusufa na kwana talatin, aka ta cece kuce ta kara turo mana na nadin sarautarsa.
wai kuna ina Bom ya tashi a Abuja aka nuno mana Goodluck Jonathan da Namadin da sauran jiga
Ka bi duniya a hankali ko ta koya ma ka hankali.
Ka bi rayuwa a sannu ko kuma azo ana ma ka sannu.
©Anas
Alhamdulillaah
Gaskiyar zance
Muhammadur Rasulullaah Sallallaahu Alaihi Wasallam
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Kano
07055250398