Sirrin Cikin Jiki
Sirrin Cikin Jiki 🧠💊
Health tips & body secrets explained simply
Daily videos 🎥
⚠️ For education only, not medical advice
Pregnant? Do you drink milk? Stop scrolling and see what it can do for your baby 👀👇
Yellow nails? 😳 Don’t assume it’s just dirt… the real reason might surprise you. 👇⤵️
29/08/2026
ÂPOLLÕ YADDA ZAKA KARE KANKA
Conjunctivitis, wadda wasu ke kira “Apollo”, Annobar da ta kunno kai a wasu jihohin Arewacin Nigeria, na iya yaɗuwa cikin sauƙi, musamman idan mutane suna yawan kusantar juna kamar a makarantu, wuraren aiki da wuraren wasa.
ALAMOMIN DA ZA A KULA DA SU
1️⃣ Ido ya yi ja sosai
2️⃣ Yawan hawaye
3️⃣ Ƙaiƙayin ido
4️⃣ Zafi ko jin rashin daɗi a ido
5️⃣ Fitar da ruwa ko majina daga ido
6️⃣ Idan ana tashi da safe, gashin ido na iya manne saboda ƙura ko majinar da ta bushe.
ME KE HADDASA TA?
Conjunctivitis ba ta da dalili guda ɗaya. Zai iya kasancewa:
🔹 virus
🔹 Bacteria
🔹 Allergy (amosanin ido)
Saboda haka, maganin da ya dace ya danganta da dalilin. Ba duk jajayen ido ne ke buƙatar antibiotic ba.
YADDA ZA KA KARE KANKA
✅ Wanke hannu akai-akai da sabulu da ruwa.
✅ Ka guji shafar ko murza ido da hannun da bai wanku ba.
✅ Kada ka raba tawul, handkerchief ko sauran kayan da ke taɓa fuska da ido.
✅ Kada ka raba kayan kwalliyar ido, kuma kada a yi amfani da kayan kwalliyar ido na mutum mai fama da cutar.
✅ Idan kana da alamomin cutar, ka guji kusantar ido da ido da wasu kuma ka kula da tsafta domin rage yaɗuwa.
🚫 KAR KA SAKA WADANNAN CIKIN IDO
Lemun tsami
Gishiri
Sabulu
Lalle
Ruwan wake
Wasu magungunan gida da ba a tabbatar da amincinsu ba.
Waɗannan abubuwa na iya ƙara fusata ko lalata saman ido.
Idan ido ya yi ja sosai, yana ciwo, gani ya fara dusashewa, akwai tsananin jin haske, ko alamomin suna ƙaruwa maimakon raguwa, yana da kyau a ga likita.
Ka tuna ba duk jajayen ido ne “Apollo” ba. A gano dalilin kafin a yi magani.
Yawan soyayyen abinci mai maiƙo da yawa kasan abinda yake haifarwa? 😱👇⤵️
26/08/2026
🚨 YA KU MATASA, KUYI HATTARA DA WANNAN KWAYA
Wannan ƙwayar ita ce Methamphetamine, wadda ake kiranta d👉" Ice" ko "Mpuru Miri". Kada ka bari sunanta ko yadda wasu suke gabatar da ita su ruɗe ka. Ba salon rayuwa ba ce, kuma ba hanya ce ta samun ƙarfi ko jin daɗi ba.
Kada ka bari abokai su zuga ka. ko son burge mutane ya sa ka lalata lafiyarka. Kuma kada ka yarda cewa amfani da ƙwaya yana nuna kai “rugged” ne
A farkon amfani, mutum na iya tunanin komai yana tafiya daidai. Amma a hankali, ƙwayoyi irin wannan na iya lalata abubuwa masu muhimmanci a rayuwa,
suna iya haifar da matsalolin tunani, rikicewa, da tashin hankali da rashin iya sarrafa kai.
Jiki — suna iya cutar da zuciya, ko hawan jini, barci da lafiyar jiki gaba ɗaya.
Abin da kayi aiki ka samu da wahala zai iya fara karewa wajen neman ƙwaya, har aikin ka da karatunka su fara lalacewa.
mutum na iya fara nisantar mutanen da suke ƙaunarsa, kuma amana ta lalace.
26/08/2026
Alamomin da ke nuna ciwon damuwa ( Depression) yafara 👇
Duba comments ⤵️
25/08/2026
👩👧👦Mahaifiya tana iya komai
uwa tana iya kula da yara, girki, da ayyukan gida a lokaci guda.
Wasu iyaye mata ba sa buƙatar gym… rayuwar yau da kullum ce take ba su workout 😂
Kada mu raina aikin uwa saboda ba a biyanta albashi. Tana iya ciyarwa, tsaftacewa, kula da yara, shirya gida, kuma har yanzu tana buƙatar kulawa da godiya.
Mutane suna neman yadda za su samu ƙarin lokaci a rana… uwa kuwa tana neman ƙarin hannaye ne 😂
iyaye mata suna buƙatar taimako, ba kawai yabo ba.
Wannan hoton yana nuna yadda uwa ke ɗaukar nauyin kula da yara da ayyukan gida a lokaci guda. ❤️
Darasin shi ne: a yabawa uwa, a taimaka mata, kuma a tuna cewa ita ma tana buƙatar hutu da kulawa. Allah ya sakawa iyayenmu da Aljanna
25/08/2026
🧄 TAFARNUWA ƘARAMIN ABU, Amma se MANYAN AMFANI. Ga abinda tafarnuwa zatayima ida kana Amfani da ita 👇 duba. Comment
23/08/2026
Kana yawan ji mara ta cika, da fitsari amma idan kaje yi sai fitsarin ya fito kaɗan?
Duba comments section 👇⤵️
Ever wondered what a carrot actually does inside your body? 🥕
From boosting eye health to clearing up constipation and lowering bad cholesterol, this little veggie does it all
Click here to claim your Sponsored Listing.