The Healer’s Pen Novels

The Healer’s Pen Novels

Share

Free Hausa and English Novel Series.

27/09/2026

Assalamu alaikum warahmatullah
Allah yayi wa mahaifina rasuwa ranar Juma'a. Saboda haka zamu dakata da kawo muku shirye-shiryen mu na wani lokaci.

Muna barar addu'a 🙏

25/09/2026

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un

Allah ya yi wa mahaifina rasuwa

22/09/2026

ƁOYAYYIYAR DAMA CHAPTER 10

FEDERAL MINISTRY OF COMMUNICATIONS, INNOVATION AND DIGITAL ECONOMY NATIONAL HEADQUARTERS, ABUJA.

Duk in da ka duba lungu da saƙo na wannan ma'aikatar motoci ne ta ko ina. K**a daga kan motocin jami'an tsaro, motocin gwamnati da kuma na manyan attajirai a wajen da aka tanada domin a jiye motoci.

Sannan duk wanda zai shiga sai an tabbatar ya shige ta na'urar tantance tsaro kafin a barshi ya shiga.

Babban ɗakin taro na National Executive Conference Hall, ƴa ɗau saiti. Ko ina a gyare tsaf bisa tsari gwanin sha'awa.

Sannan tsakiyar ɗakin taron, ɗauke yake da wani dogon taburi mai siffar U-shape ya mamaye tsakiyar ɗakin taron.

kowace kujera tana ɗauke da sunan wanda zai zauna a gabanta. A gaba kuma w**k babban allo ne (LED screen) Wanda yake ɗauke da taken taron k**ar haka:

NATIONAL TELECOMMUNICATIONS INFRASTRUCTURE DEVELOPMENT STRATEGIC MEETING.

Manyan jami'an gwamnati, ƙwararrun masu ilimin fasaha, da wakilan International Telecommunications Consulting Firm suna zaune cikin nutsuwa suna jiran isowar baƙi.

Shigowar Ministan Sadarwa, da Babban Sakataren Ma'aikatar da wasu manyan jami'an gwamnati ne ya saka kowa ya miƙe tsaye cikin girmamawa.

Sai da s**a zauna sannan kowa ya zauna.

Shigowarsu ke da wuya, Alhaji AL-Hassan Ibrahim Ɗanbatta ya shigo cikin nutsuwa, sanye da wata farar babbar rigar shadda da ƴar ciki da hula mai tsadar gaske. Ƙafarsa sanye da wani takalmin fata baƙi, fuskarsa ɗauke da farin glass ɗin sa mai matuƙar ɗaukar hankali.

A bayansa kuma, Mu'azzam ne yake biye dashi cikin shiga ta alfarma, hannunsa riƙe da wata baƙar jaka wadda take ɗauke da takardu masu muhimmanci.

Shigowarsu kaɗai ta ja hankalin mahalarta taron.

Wasu daga cikin manyan attajiran s**a miƙe suna musabaha dashi cike girmamawa. Kasancewarsa babban mutum mai daraja abun girmamawa wanda ya daɗe da shahara a duniyar kasuwanci.

A hankali waje ya cika da manyan baƙi kowa ya hallara ciki harda manyan attajirai nan guda huɗu:

Senator Idris Baƙo, mamallakin Green Marine Oil & Gas.

Chief Patrick Okafor, shugaban babban kamfanin sadarwa a yankin Kudu maso Kudu.

Alhaji Musa Galadima, shugaban Galadima Group.

Sai na ƙarshe, Alhaji Kabiru Sani, mamallakin bankunan All The Way, da kamfanin haƙar ma'adinai da manyan kamfanonin gine-gine.

Sai da kowa ya zauna a mazauninsa wajen taron yayi tsit sannan Minister ya gyara zamansa ya kalli kowa na wajen ya fara magana:

"Gentlemen... thank you for honoring the invitation of the Federal Government. What we are about to discuss today has the potential to reshape Nigeria's digital future."

Sake gyara zamansa yayi. Sannan ya sake kallon mutanen ya ci gaba da bayani:

"Today's meeting concerns a project that has the potential to redefine Nigeria's digital future for the next fifty years."

Da hannunsa yayi umarni, take aka rage hasken ɗakin kaɗan.

Take hasken babban kallon LED Screen da ya ke a wajen ya ƙaru. Taswirar Nigeria ce ta fara bayyana a jiki.

Daga bisani kuma wasu layuka blue s**a fara bayyana suna ratsa jihohi daban-daban.

Wani Bature da ke wakiltar International Telecommunications Consulting Firm ya miƙe tsaye ya karɓi remote ya fara bayani k**ar haka:

"Good morning, ladies and gentlemen."

"My name is David Anderson, Lead Infrastructure Consultant."

Cikin nutsuwa ya danna remote ɗin.

Take hoton tsarin tauraron dan adam (satellite), igiyoyin hasken sadarwa (fiber-optic), cibiyoyin adana bayanai (Data Centres) da dogayen ƙarafen sadarwa (communication towers) s**a bayyana.

Sannan ya ci gaba da bayani:

"Ladies and gentlemen..."

"For over three years, the Federal Government of Nigeria, together with our international team, has conducted satellite imaging, geological surveys, environmental studies and digital infrastructure assessments across the country."

Sannan ya sake danna remote, take wani yankin mai girma da ka yi wa alama da launkan blue ya bayyana a taswirar Jihar Kano

Sannan ya ci gaba da da bayani:

"Our findings revealed that one location stands above every other location in Nigeria."

Ya nuna wurin da laser pointer da take hannunsa

"Gonar Kaka."

Cike da mamaki Alhaji AL-Hassan da Mu'azzam s**a gyara zamansu suna nazarin wajen.

Take attajiran nan guda huɗu s**a fara kallon junansu.

Numfasawa yayi, sannan ya ci gaba.

"This land possesses a combination of geographical elevation, stable bedrock, low electromagnetic interference, excellent climate conditions and strategic connectivity that makes it the ideal location for Nigeria's future National Telecommunications Corridor."

Sannan ya sake danna remote ɗin. A wannan karon wani hoton ya bayyana na yadda wajen zai kasance bayan an gina wannan katafaren Digital City.

Sannan ya fara bayanin abubuwan da za su aiwatar a wajen:

"Under this master plan, Gonar Kaka will host Nigeria's largest Digital Infrastructure Hub."

"National Artificial Intelligence Data Centres..."

"Satellite Communication Control Centre..."

"Cloud Computing Facilities..."

"Fiber Optic Distribution Hub..."

"Emergency Digital Operations Centre..."

"And West Africa's largest Telecommunication Exchange."

Wani irin shuru ne ya mamaye ɗakin.

Ministan ne ya katse shurun da faɗin:

"The estimated investment for this multi-phase project is approximately 3.06 billion Dollars, which is equivalent to 4.2 Trillion Naira."

Take ɗakin ya ɗauki surutai ƙasa-ƙasa, kowa yana faɗin albarkacin bakinsa tare da jinjina girman wannan aikin da za'a yi.

Shi kuwa Alhaji AL-Hassan kallon Mu'azzam yayi sannan ya mayar da hankalinsa kan screen ɗin yana faɗaɗa tunaninsa.

Sai yanzu ya fahimci dalilin da ya saka a lokaci guda aka fara harin siyen Gonar Kaka.

Wato babbar hanyar cibiyar sadarwar 5G Network da ake shirin haɗawa da zata ratsa ta wasu ƙasashen Yammacin Afirka da s**a haɗa da Nijar, Mali, Senegal, Togo da Nigeria za ta ratsa ta cikin Gonar Kaka.

A ciki za'a gina dukkan abubuwan nan da s**a lissafo...kai tsaye dai zata zama wata babbar cibiyar da za'a sarrafa network ɗin wannan ƙasashen...

Minister ne ya katse masa tunaninsa da faɗin:

"Alhaji AL-Hassan Ibrahim Ɗanbatta..."

"Congratulations."

"Duk binciken da aka gudanar ya tabbatar mana da cewa gonar ka ita ce ta fi dacewa da wannan aiki fiye da kowanne fili da aka gwada a dukka faɗin waɗannan ƙasashen."

Take idanun al'ummar da take wajen ya koma kansa.

Sannan Minister ya ci gaba da bayaninsa:

"This is why the Federal Government requested this meeting. Before any decision is taken, we believe it is only fair that the legal owner of the land understands its strategic importance to the nation."

Alhaji AL-Hassan ya ɗan gyara zamansa, sannan ya sake kallon Mu'azzam da ya ƙurawa screen ɗin ido, ga dukkan alamu ya lula cikin nazarin bayanan, sannan ya sake mayar da kallonsa kan Ministan yace:

"First and foremost, I would like to express my sincere appreciation to the Federal Government for inviting me to this important meeting and for considering me worthy of being part of such a historic discussion."

Sannan ya gyara mic ɗin gabansa ya ci gaba da magana:

"What I have seen today is far beyond anything I could have imagined. If this project will truly transform Nigeria's digital future and benefit generations to come, then it is undoubtedly a remarkable vision, one every patriotic citizen should be proud of."

Numfasawa yayi sannan ya ɗora:

"However... Gonar Kaka is not just another piece of land to me. It is my family's heritage. My parents are buried there. My elder brother rests there. My two beloved wives are buried there. And, by the will of Almighty Allah, it is where I hope to be laid to rest when my time comes."

Take ɗakin yayi shuru kowa yana jiran ya ji mai zai ce:

"For that reason, I cannot make such a decision today. I will need time to reflect carefully, consult my family, and seek Allah's guidance before giving the Federal Government my final position.

I sincerely hope you will understand and respect my request."

Take mamaki ya cika kusan kowa na cikin ɗakin ciki har da Minister. Saboda ba kowa ne za'a zo masa da maganar ƙaruwa ta kasuwanci irin wannan ba yace zai jira sai yayi shawara ba.

Wannan ya ƙara masa kima da daraja a idon mutane.

Ban da Mu'azzam da yake gefen sa wanda tuntuni ya riga ya san kwanan zancen.

To da wannan bayanin nasa aka ƙarƙare taron.

Kai tsaye wajen tawagar motocinsu s**a nufa. Yana tafe Mu'azzam yana take masa baya.

Cikin zafin nama Suhaib ɗan gidan Alhaji Musa Galadima ya nufi in da Alhaji AL-Hassan yake yana dab da shiga mota.

Cikin zafin nama Mu'azzam ya sha gabansa.

Kallon Mu'azzam yayi, s**a tsaya suna kallon-kallo.

Cikin zafin rai Mu'azzam ya kalle shi yace:

"Ba zamu siyar muku da gonar ba, kuma ba zamu baku auren Nabila ba..."

Murmushin takaici Suhaib ya yi, sannan ya kalli cikin idon Mu'azzam yace:

"And so..."

"Mu'azzam!"

Kiran da Baba yayi masa ne ya saka ya zubarwa da Suhaib wani kallon banza, sannan ya zagaya ya shiga motar, take s**a bar wajen s**a bar Suhaib a tsaye yana huci.

Shima daga ƙarshe ya nufi tasu tawagar s**a tafi.

Suna tafe amma ransa sam babu daɗi. Ya lura da yadda Mu'azzam yake ta huci amma bai ce masa komai ba sai ma murmushi kawai da yayi ya kawar da kansa.

Can kuma yace dashi:

"Mutane suna tunanin komai na rayuwa kuɗi yana iya siya, basu san da cewar akwai abubuwan da sai dai ido ya kalle su kawai amma ba zasu taɓa taɓuwa ba."

Wata sanyayyiyar ajiyar zuciya Mu'azzam yayi sannan ya kalli Baba yace:

"Sun samu bayanan sirri daga wasu hukumomin shiyasa s**a fara lallaɓowa domin su siya, saboda suna tunanin sun fi mu sanin daɗin kuɗi."

Wannan maganar ta saka sai da Baba yayi dariya sosai, saboda a yanayin da Mu'azzam ya furta ta. Saboda shi kaɗai yasan halin kayansa.

Lallai yau ya da ɗa tabbatarwa da kansa yadda Mu'azzam yake tsananin son Nabila.

Suna isowa gida kai tsaye private part ɗin gidan ya shiga. Yana shiga ya iske Nadia da Sanaya a babban parlor a zaune.

Sam bai ji daɗin ganin su ba, saboda shi kai tsaye wajen Nabila yazo.

Cike da alamar tambaya Nadia ta hau tambayarsa.

"Babe...lafiya kuwa? Me ya shigo da kai nan kuma?"

Jigib! ya zauna akan kujera, sannan ya kalle ta da alamar gajiya yace:

"Ai na san kina nan."

Murmushin jin daɗi tayi, sannan ta taso ta zauna kusa dashi ta fara matsa masa kafaɗunsa saboda ta ga alamar gajiya a tare dashi.

Suna cikin wannan yanayin Nabila ta fito daga hanyar kitchen hannun ta riƙe da wani matsakaicin tray. Da doguwar Abaya a jikinta baƙa ta yafa mayafin.

Da gani zata ɗan yi nisa ne.

Kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kanta ta fice.

Take ya ji yana neman ya rasa nutsuwarsa. Yana son ya bi bayan Nabila yana tsaron Nadia kar ta gano shi, saboda ya san ta da wayon tsiya shiyasa tsawon shekarun nan yake taka tsan-tsan da ita.

Haka ya daure ya ci gaba da zama tana matsa masa jikinsa tana yi masa hira amma sam hankalinsa ba a tare da ita yake ba.

Suna cikin wannan yanayin wayarsa ta yi ringing.

Cikin ladabi ya ɗaga saboda ganin number Baba ne.

"Ka zo kai da Nadia ina son ganin ku."

"Ok Baba."

Abinda ya furta kenan. Sannan ya kalli Nadia saboda ya tabbatar ta ji abinda yace. Sannan s**a miƙe s**a nufi ɓangarensa.

A can s**a iske Nabila tana zuba masa kunun gyaɗar da ta dama masa da soyayyen dankalin turawa. Suna shigowa ta miƙe zata fita. Baba ya tsayar da ita.

Dole ta dawo ta zauna ba don tana so ba.

"Nadia zaki ci gaba da kula da Construction Company, anan Abuja. Mu'azzam kuma zai koma Lagos zuwa nan da next month ya ci gaba da kula da Ɗanbatta Group a can."

Cikin rashin fahimta dukkansu s**a ɗago s**a kalli Baba. Ita kanta Nabila sai da abun ya bata mamaki.

Amma ita Nadia na ta mamakin da sauƙi, saboda murnar wannan babban company da aka bata damar jagoranta. Saboda za ta ci karen ta ba babbaka zata taka kowa son ranta.

"Duk lokacin da ɗayan ku yake free sai yaje ya ya duba ɗan uwansa."

"Ok Baba godiya nake. Allah ya ƙara girma."

Abinda Nadia ta furta kenan tana murna.

Shi kuwa Mu'azzam jikinsa ne yayi sanyi, saboda tabbas yasan akwai abinda Alhaji yake shiryawa.

**************************************

BAYAN SATI UKU

Tsawon wannan lokacin ban da takura da matsin lamba babu abinda Alhaji yake fuskanta daga masu buƙatar siyen Gonar Kaka. Daga bisani da s**a lura ba zai siyar ba, sai ƙudurin nasu ya koma saka hannun jari.

Duk da Alhaji da Mu'azzam basa bin ta kansu kuma sun ƙi yarda suyi zaman tattaunawar da suke nema, amma abun ya fara ɓatawa Alhaji rai, musamman da ya ranar sake zaman tattaunawarsu da Minister ta ƙarato.

Ranar da taron ya zo, sun sake halarta k**ar yadda s**a halarta a wancan karon sai dai wannan lokacin Alhaji AL-Hassan ne ya kusa jagorantar taron saboda kowa ta bakinsa yake son ji.

Bayan kammala gabatarwa ɗakin yayi shuru. Daga nan ya fara bayaninsa da harshen turanci k**ar haka:

"Over the past few weeks, I have reflected deeply, consulted my family, sought legal advice, and most importantly, sought the guidance of Almighty Allah regarding this matter.

I stand before you today not as a businessman alone, but as the custodian of a family legacy that is over a century old."

Ya numfasa sannan ya ci gaba:

"Therefore, I am prepared to support this national project, but only under my conditions."

Take kowa na ɗakin ya sake tattara hankalinsa kan su.

"My first condition...The graves of my parents, my elder brother, and my late wives shall remain untouched forever. That section of Gonar Kaka shall be legally protected as a family heritage site."

Minister ya jinjina kansa alamar gamsuwa.

"Second...Every family currently living or working on that land must be relocated with dignity. They must receive better homes, better livelihoods, and fair compensation before a single machine enters the site."

Ɗakin ya sake yin shuru kowa ya mayar da hankalinsa kansa. Mayan jami'an gwamnati suna rubuta dukkan shsruɗɗan da yake bayarwa.

"Third...At least seventy percent of the workforce employed during construction and operation must be Nigerians. This project must create opportunities for our people—not import unemployment."

Take ɗakin ya ɗauki tafi saboda wannan sharaɗin na ɗaukar ma'aikata ƴan asalin Nigeria tabbas zai rage matsalar rashin aikin yi a Najeriya.

Sannan ya ci gaba.

"And finally...This project is too important to become another private empire."

Ya faɗa yana kallon waɗannan hamshaƙan attajiran guda huɗu.

Sannan ya kalli Minister ya ci gaba da bayaninsa.

"Therefore, no private billionaire, no private consortium, and no individual investor shall own shares or equity in the National Telecommunications Corridor.

The project shall remain under the ownership of the Federal Government of Nigeria. Any private company that participates may only serve as a contractor, consultant, or service provider. Once its contractual obligation is fulfilled, its involvement ends."

"No one will own this project."

"No one will inherit it."

"No one will monopolize it."

"It belongs to Nigeria, and it must remain Nigeria's forever."

Sannan ya juya ya kalli Minister yace:

"If these conditions are acceptable to the Federal Government, then I will make Gonar Kaka available for this project. If not...then I respectfully decline, regardless of the amount of money placed before me."

Ba tare da yace komai ba ya koma ya zauna a mazauninsa.

Take ɗakin taron yayi shuru. Kowa yana saƙe-saƙe a ransa musamman waɗannan shahararrun attajiran guda huɗu.

Wato kenan Alhaji AL-Hassan ya fitar dasu daga cikin wannan gagarumar kwangilar wadda zata lashe a aƙalla Naira trillion 4.2.

Ya ƙi ya siyar musu da gona saboda mahimmancinta a gare shi, sannan kuma ya kafa wasu sharuɗɗa masu tsauri, k**ar barin hakkin mallakar gonar ga iyalansa kawai wato gwamnati zata din ga hayar wajen ne, ba siyarwa yayi ba, da kuma ƙayyade iyakar in da za'a yi aikin ba tare da an taɓa shiyyar da ahalinsa suke kwance ba.

Wanda ya fi ɗaga musu hankali shine, yadda babu wanda zai saka hannun jari a tsarin.

Tabbas wannan wata dabara ce ta hana wani mallakar gonar a nan gaba.

Shiyasa ya damƙa aikin kacokam a hannun gwamnatin tarraya.

Wannan ya saka a ka tashi daga taron tare da jiran lokacin da gwamnati zata sanar da ranar da za a yi bikin saka hannu na ƙarshe (signing ceremony) domin fara gabatar da aikin.

*****************************
A zaune suke a wani sirrintaccen waje, dukkannin su kawa yana saƙe-saƙe a ransa. Saboda yadda Alhaji AL-Hassan ya ɓarar musu da wannan babbar damar da ta tunkaro su.

Ba wasu bane sai, Senator Idris Bako, Chief Patrick Okafor, Alhaji Musa Galadima, da kuma Alhaji Kabiru Sani.

Kowannesu yana bada shawarar yadda za ayi su shiga cikin wannan tsarin ta ƙarfin tsiya.
Kowa ya gama ba da shawararsa amma har yanzu ba'a samu wadda zata yi aiki ba.

"To mu kawar dashi mana sai mu karɓa a wajen magadansa..."

Alhaji Kabiru ne ya furta wannan kalmar wanda tun da aka fara tattaunawar yayi shuru bai ce komai ba.

Cike da razani dukkansu s**a ɗago s**a kalle shi. Saboda suna ganin ya faɗi abinda ba zai taɓa yiwuwa ba ne.

Ɗagowa yayi ya kalle su ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya sannan yayi murmushi yace:

"Kawar da kaza daga kan ƙwanta abu ne mai sauki. Da zarar mun kawar dashi ina mai tabbatar muku duk wanda ya gaji wannan gonar acikin ahalinsa ba zai taɓa wucewa tayin biliyoyin kuɗin da zamu yi masa ba.

Ba dai damuwarsu shiyyar da ahalinsu suke kwance ba?

To ba zamu taɓa nan ba, iyakacin ɓangaren da ya amince zamu taɓa."

Cikin zafin nama Alhaji Musa Galadima yace:

"Tabbas ka zo da shawara saboda mutum ne mai matuƙar taurin kai da tsattsauran ra'ayi in dai yana raye ba zai taɓa amincewa ba.

Amma in dai ya bar duniya dole magadansa su amince. Amma babbar tambayar itace, ta yaya zamu iya kawar dashi?"

Murmushi ya sake yi yana jujjuya lemon da yake cikin kofin glass ɗin da yake hannunsa. Sannan ya ɗago ya kalle su yace:

"Duk cikin ku nine matashi mai ƙananun shekaru shiyasa ƙwaƙwalwarta tafi taku ja."

Sannan ya gyara zamansa yace:

"Idan dukkanku kun amince to zanji da wannan ɓangaren. Ni zan aiwatar da komai."

Kallon-kallo s**a fara yi wa junansu kana daga bisani kowannesu yace:

"Mun amince."

Dariya s**a yi gabaɗayansu kana kowa ya k**a gabansa cike da farin ciki.

****************************

A zaune take akan kujerar zanen ta, hannunta sai motsi yake yi ta kasa zana komai saboda tsananin damuwar da take ciki.

A hankali ta ajiye brush ɗin tayi tagumi ta fara tambayar kanta:

Shin a haka zan zauna kullum ina soyayya a ɓoye bani da wani ƴanci?

Gaskiya bazan iya ba.

Abinda ta furta kenan a fili sannan ta miƙe ta yi wa mai aikin da take gefenta umarnin da ta haɗa kayan.

Kai tsaye ɓangarenta ta nufa ta kwanta akan gado ta fara haɗa kayanta.

Tabbas yau Kaduna zata tafi ko zata samu afuwa.

Sai da ta kammala haɗa komai nata sannan ta ji wayar ta tana ringing.

Tana dubawa ta ga Alhaji ne. Cikin ladabi ta ɗaga tare da yin sallama.

To bayan ya amsa sallamar yayi mata umarnin da ta zo yana son ganin ta.

Dole ta ajiye abinda take yi ta ɗauki mayafinta ta nufi ɓangarensa.

Sai dai tana shiga parlor ta iske kawunta Alhaji Badamasi da take shirin tafiya gidansa yanzu.
Daman tuni ya zama aminin Alhaji don duk abinda zai yi sai yayi shawara dashi.

Sai kuma Mu'azzam daga gefe, sai kuma Baba Saleh direban Alhaji na musamman.

Kanta a ƙasa ta shiga parlor. Ta durkusa ta gaishe su sannan ta kalli Alhaji tace:

"Gani Baba."

Jinjina kansa yayi sannan ya kalli Mu'azzam da tuni ya gama shiga ruɗani saboda ya kasa gane abinda yake shirin faruwa yace:

"Ina cash ɗin da nace ka taho dasu?"

Hannunsa yana rawa ya saka su acikin aljihunsa ya fito da wata farar envelope da take ɗauke da bandir ɗin ƴan dubu-dubu guda uku ya ajiye akan center table ɗin da yake tsakiyar parlor.

Sannan Alhaji ya kalli Alhaji Badamasi yace:

"Ga sadaki nan ina son za'a ɗaura auren Mu'azzam da Nabila a yanzu..."

Cikin matsanancin tashin hankali Mu'azzam ya ɗago ya kalli Alhaji bakinsa sai rawa yake yi ya kasa magana.

"Ba ka son ta ne?"

Alhaji ya tambaye shi tare da tsare shi da ido.

Waiwayawa yayi ya kalli Nabila da ta rufe bakina da hannunta ta fashe da wani irin kuka. Sannan ya sunkuyar da kansa.

Cikin nutsuwa Alhaji ya zaro wata farar envelope da take ɗauke da wasu hotuna ya ajiye akan tabla ɗin sannan ya kalli Mu'azzam yace:

"Ɗauki ka duba, itama ka bata ta duba. Ina son nasan san su waye a cikin wannan hotunan."

Hannunsa yana rawa ya ɗakko envelope ɗin. Take hotunan ciki s**a tarwatse.

Karaf! idanuwansu s**a kai kan hotunan.

Lokaci guda s**a ji tamkar su nutse a wajen saboda kunya.

Hakan ya saka kowannesu ya sunkuyar da kansa ƙasa.

"Kun amince a ɗaura muku aure ko kuwa shiriritar ta fi birge ku?"

Alhaji Badamasi ne ya furta yana kallonsu.

Basu da zaɓi dole s**a ɗaga kansu alamar "Eh"

Take aka gabatar da siga aka ɗaura aure bisa yadda addinin musulunci ya tsara.

Sai da aka kammala sannan Alhaji ya kalli Mu'azzam yace:

"Ka ɗauki matarka ku tafi Lagos a yau an shirya muku komai. Nadia kuma zanji da ita...."

Cikin tsananin tashin hankali Mu'azzam ya kalli Alhaji yace:

"Don Allah Baba kar ka faɗa mata a yau zan faɗa mata da kaina....don Allah kar wanda ya faɗa mata zan faɗa da kaina."

Ya ƙarasa maganar yana kallon sauran ƴan ɗakin.

Jinjina kansu kawai s**a yi. Sannan ya juyo ya kalli Nabila da take ta gursheƙen kuka daga zaune ya sunkuyar da kansa.

Alhaji ne ya gyara zamansa yace:

"Wannan kuma zaɓin ka ne iyalinka ne kai kasan yadda zaka tafi dasu.

Ni dai nawa shine toshe hanyar ɓarna. Abinda dai nake so dakai shine kayi adalci don ko ni nan da nake babanka ban iya haɗa mata biyu ba."

Wannan kalmar ta sa ce ta saka Alhaji Badamasi da Baba Saleh murmushi.

Sannan ya sake kallon sa yace:

"Ka tashi ka ɗauki matarka ku tafi."

Jikinsa yana rawa ya miƙe tsaye ya fara diri-diri saboda kukan da Nabila take yi yayi matuƙar ɗaga masa hankali.

"Ke Nabila!

Ki tashi ki bi mijinki ku tafi.

Sakarya kawai."

Alhaji Badamasi ne ya furta wannan kalmar saboda yaga alamar k**ar ba zata tashi ba.

Miƙewa tayi tsaye fuskarta a rufe da mayafinta tana jan ƙafa, sai da ta kai dab ta fita taji Alhaji yace:

"Ki zo ki karɓi sadakin ki."

A sanyaye ta juyo tana tafiya k**ar wadda ƙwai ya fashewa a ciki, Alhaji Badamasi ya miƙa mata envelope ɗin, sannan ta juya ta fice waje Mu'azzam ya bi bayanta.

Bin bayansu kawai Alhaji yayi da kallo tare da yin murmushi ya jinjina kansa.

Da gudu ta nufi ɓangarenta ta zube akan gado
take ta sake buɗe wani sabon shafin kukan.

Mu'azzam yana tsaye akanta ya rasa me zai ce mata.

Ya rasa ta inda zai fara rarrashinta.

Har ga Allah ya ji daɗin abinda ya faru.

Amma kuma, wannan kukan na ta ba ƙaramin ɗaga masa hankali yake yi ba...

THE HEALER'S PEN ✍️

ƘWAI BIYU (Hausa Novel) 21/09/2026

ƘWAI BIYU complete story 👇

ƘWAI BIYU (Hausa Novel) ƘWAI BIYU (Love and Betrayal) "...ya kasance yana fama da larurar rashin haihuwa wanda yan...

21/09/2026

Alhamdulillah mun gama yi muku posting ɗin labarin NI DA KANNENA
Zaku samu cikakken labarin akan Whattpad. Ga link a comment section 👇

21/09/2026

ƘARSHEN LABARIN NI DA KANNENA 👇

Shiryawa tayi cikin wata tsadaddiyar abaya baƙa mai kyawun gaske sannan itama ta fita ta nufi wajen parking in da ta iske su Daddy, Ameerah da Anuwar. Da mamakin ta ta shiga mota daga ita sai Ashraf sannan sauran motocin s**a biyo bayan su. Cike da mamakin ta taga an dauki hanyar garin Bunkure, a zabure ta ta juya ta kalli Ashraf tace:

"Kar kuyi min haka don Allah, me zai saka ku tono abinda na binne shi a zuciya ta har abada..."

Hawaye ne s**a fara zirya a fuskar ta. Duk da Ashraf yaji tausayin ta sosai amma ya dake yacigaba da tukin sa. Saboda yasan halin ta sarai ko da ya tsaya yana bata hakuri a yanzu kam ba sauraron sa zatayi ba. Haka tayi ta rubza masa kuka har s**a isa garin Bunkure.

Duk da hankalin ta ba'a jikin ta yake ba, amma hakan bai hana ta ta lura da sauye-sauyen da aka samu ba matuka a garin. An gina t**i sosai ga makarantu, an gyara babban masallacin juma'a, ga boreholes masu amfani da hasken rana birjik.

Dab da ƙarasawar su cikin unguwar Jiroji wani matashin bafulatani ya koro shanu s**a rufe musu hanya, hakan ne ya saka dolen su s**a tsaya da tafiya. Tana zaune a motar ta jingina kanta tana kallon wimdow gefen ta taji an tsaya. Hakan ya bata damar ƙarewa wata siririyar hanya kallo. Duk da wajen ya sauya, amma tabbas bata manta da wannan hanyar ba. Cikin zafin nama ta buɗe murfin motar ta fito da sauri ta nufi wannan hanyar cikin sassarfa a ƙarshe ma dai ta hada da gudu.

Da sauri Ashraf ya fara ƙoƙarin yin parking saboda a tsakiyar t**i suke, kana shima ya rufa mata baya da gudu. Haka su Anuwar ma da yake duk akan idon su abun ya faru. Duk iya gudun Ashraf kasa cimmata yayi, gashi wajen gari babu mutane,ballanta ya saka a tare masa ita, kuma da dukkan alamu tafi shi sanin kan hanyar saboda da ya ɓullo ta nan kafin ya ƙarasa sai yaga ta ɓille ta wata hanyar. Haka ta dinga sirfa gudu iya karfin ta tana kuka, har sai da ta dangana da babbar makabartar garin su.

Tana isa ta fara waige-waige, wajen ya ɓace mata, wani tsoho ta gani ga dukkan alamu shine mai gadin, ta tambaye shi kabarin Malam Abdussalam da matarsa, ai kuwa babu musu ya shige gaba tabi bayan sa. Tana isa ta tarar da an gyara tagwayen kabarurrukan, take ta zube akan gwiwoyin ta ta rusa wani irin kuka mai cike da tsananin tashin hankali.

A haka su Anuwar s**a iske ta, ya ƙarasa jikin sa a sanyaye ya rungume ta yana rarrashin ta. Haka itama Ameerah ta fashe da wani irin kuka. Su gaba daya basa tausayin kansu k**ar yadda suke tausayawa Nuratu, saboda ita tafi shaƙuwa da iyayen nasu natuka. Shi kuwa Ashraf yana gefe yana kallon su gabaɗaya tausayin su ya k**ashi, take nadamar wannan tafiyar ta faɗo masa. Amma kuma ya zama dole ko mai daren daɗewa hakan zai ya faru.

Daƙyar Daddy ya iya lallaɓata daga kwanciyar da tayi lakadan a tsakanin kabarurrukan, s**a nufi cikin gari babu abinda take ambatawa irin "Allah ya jikan ku Baffana da Inna ta"

Gidan mai gari s**a nufa direct, abinda ya bata mamaki shine yadda mai garin ya saba da Daddy sosai, sannan yana ganin Ashraf ya fara yi masa godiya akan wannan gagarumin sauyi da ya kawo musu acikin garin. Cike da mamaki ta kalle shi taga ya ɗauke kai alamar baya son hada ido da ita saboda tausayi.

Tuni gari ya dauka Nuratu tazo, waɗan da s**a santa a baya s**a fara ƙoƙarin ganin ta, amma aka hana kowa shigowa. Babban abun birgewa shine; Daddy ya toshe bakin kowa akan fito da zancen mugun asirin da kawu Ilu yayi mata, ko da Ashraf har yanzu bai san da zancen ba.

Suna zaune acikin gidan Maigari. Maigari ya saka aka je aka kirawo kakannin su na wajen uwa s**a zo domin su gana. A nan ma abun abun tausayi, cikin kuka suke bata labarin abinda ya faru bayan sun ta gudu da irin neman da akayi musu, domin su a tunanin su Ilu ya hallaka su ne suma shiyasa s**a takaita neman su.

Saboda sati guda da ɓacewar su hukuma ta zurfafa bincike, ashe yan uwan Baffa ne s**a hada kai s**a kashe shi da ɗan sandan nan da kanin mahaifiyar ta. Hakan ya saka aka k**a su, ƙarshe dai shi kawu Ilu yayi gardama, saboda matsafan sa sun bashi sa'a, haka kuwa akayi aka bada belin sa ya dawo ya gamu da larurar hauka da sai da aka kulle shi a wani ɗaki a can bayan gari yana ta tonawa kansa asiri, babu abinda bai fada ba. A ƙarshe dai ya mutu, sai daya kwana uku aka lura da mutuwar sa, da ƙyar aka samu masu yi masa sallah.

A nan fa take sake jin cewar Ashraf ya gyara ainahin gidan su, ya ɗebo kakannin ta ya zuba su aciki. Duk abun nan da akeyi kanta a jingine da jikin bango ta kasa magana, kawai bin kowa take yi da kallo.

Wayar Anuwar ce ta katse musu hira, yana ɗagawa yayi murmushi tare da fadin "Allah ya raya shi". Bayan ya kashe wayar ya kalli Daddy yace "Ka kuma samun takwara, Nawwar ta haifi namiji." Take kowa ya shiga murna da son barka. Anuwar ya juya in da Nuratu take a zaune yaga wayam ta zare jiki ta fice.

A hankali ta dinga tafiya tana bin wannan hanyar da bazata taɓa manta wa da ita ba, ƙwaƙwalwarta tana cigaba da kawo mata tunanin lokacin da suke zuwa gona da Baffan ta, lokacin da take kai masa abinci da kuma lokacin da suke dawowa idan maraice yayi. Haka ta dinga bin hanyar yanayin wancan lokacin yana dawo mata sabo fil.

A hankali ta ƙarasa gonar, gonar da take cike da tarin alƙawarukan da a yau take son cikawa. Duk da taga gonar ta zama wani kayataccen lambu da yasha gyara, abun ya bata mamaki matuka, saboda ji tayi ta kasa gano a in da ajiyar tasu take. Tana tsaye a bakin waken ta kasa shiga ta zubawa wajen kallo, sannan tace:

"Ashraf! idan ka sauya duk wasu abubuwan saboda a tunanin ka zananta komai, bazaka iya sauya abinda yake cikin ruhi na da kuma ƙwaƙwalwata ba."

A hankali taja wani numfashi, tare da lumshe idon ta, take taswirar gonar a da ta fara dawo mata, ta buɗe idon ta a hankali ta dinga bin zanen da ƙwaƙwalwarta ta bata har sai da ta dangane da wannan bishiyar mangwaron da s**a dasa shekaru ashirin da s**a wuce da ɗoriya, wadda har ta fara fitar da ƴaƴa masu kyawun gaske.

Tsayawa tayi tana shafa bishiyar, ta tayi wani murmushin dole, sannan ta saka ƙafar ta ta doki daidai wajen da s**ayi ajiyar, tare da sunkuyawa cikin zafin nama ta fara tone ƙasar da hannun ta tana faɗin "Baffa nazo zan cika alkawarin ka...." Cike da wani irin kuka mai abun tausayi.

Tana wannan yanayin s**a ka riske ta, da gudu Ashraf ya ƙaraso ya rungume ta, ya kalli hannayen ta duk sun daddauje ga jini yana zuba. Ita kuwa ɓata daina kukan ba. Anuwar ne yayi ta maza ya kwalawa wasu da suke aiki a wata gona kusa da wajen kira akan su basu aron abun haƙa. Aikuwa da kansu s**a ƙara so s**a fara haƙar wajen, sai da s**ayi haƙa mai nisa sannan s**a iske wannan akwatun ƙarfen.

Ana ciro shi Nuratu ta bar jikin Ashraf ta taso ta rufe bakin ta da hannayen ta tana wani irin kuka. Ana bude wa tayi arba da babbar rigar Baffan ta. Ta karɓa da sauri ta rungume ta, tare da durkushewa ta sake fasa wani kuka mai amon sauti tana furta:

"Baffana....an kashe min Baffana akan abinda nafi karfin sa yanzu...."

Duk yadda akayi a raba Nuratu da rigar nan ya gagara, haka aka haƙura aka barta s**a dauki wannan akwatun s**a saka a mota. s**a ɗauko hanyar dawowa zuwa Kano.

Kanta yana jingine k**ar wata gawa, idon ta a rufe, zuciyar ta tana sabunta mata raɗaɗin da bata iya jin sa ba a shekarun baya saboda ƙuruciya. Anan ta fara tunanin gwagwarmayar da tasha ta rayuwa tun daga ranar da mahaifanta s**a bar duniya har zuwa yau. Ta dinga hasaso wahalhalun rayuwa da gwagwarmayar da tasha ta ita da ƙannen ta, tunanin yadda kaddara ta dinga sauya musu al'amura daga masu kyau zuwa marasa kyau, sannan daga marasa kyau zuwa aminci da kuma kwanciyar hankali. Lumshe idon ta tayi wasu hawaye masu zafi s**a gangaro mata, sannan tace:

"Ya Ubangiji nayi imani da kai, nayi imani da ƙaddarar ka mai kyau da kishiyar haka, duk abinda ka shirya min na karɓa, kuma nayi godiya, kaci gaba da amintar dani har zuwa ranar da zanyi numfashi na na ƙarshe...."

Idan Ubangiji ya nufi alamar ɗaukaka da arziki su keto ta layin rayuwar mutum, to dole sai ya rasa wani abu daya fi so a rayuwar sa a matsayin jarrabawa. Walau iyaye, ko yan uwa, ko ƴaƴa, ko miji ko mata, ko lafiya, walau naƙasa ta zahiri ko ta baɗini, kokuma ya rasa garin su ma gabaɗaya. Saboda wannan sabon shafin na rayuwa da Ubangiji zai bude watakila da ya dogara da waɗannan abubuwan ko yana tare dasu, da wannan matsayin da daukakar ba zasu taba riskar sa ba.

Shi Ubangiji yana jarabtar bayin sa ne masu ƙarfin imani, gwargwadon imanin ka, gwargwadon jarrabawar ka, sannan gwargwadon hakurin ka da wannan jarrabawar, gwargwadon sak**akon da zaiyi maka a ƙarshe, walau a duniya ko a lahira. Idan jarrabawa mak**anciyar wannan ta riske ka, abinda Ubangiji yake so shine; kayi addu'a, kayi aiki tukuru domin gina goben ka, sannan uwa uba kayi hakuri, ka jure, ka koma gefe ka zubawa sarautar Allah ido, zai yi maka sak**ako mai kyau ta hanyar da baka taɓa tsammani ba.

Anan na kawo ƙarshen wannan labarin, ba don ina so ba zan bar shi, a'a saboda na samu damar share hawayen da yake kwaranyowa daga idanuna, na samu hutu, sannan daga bisani na ɗora muku da wani labarin.

Labarin 'NI DA KANNENA' sadaukarwa ce zuwa ga mahaifiya ta. Sannan da dukkan wata mace a duniya da take fadi tashi domin gina goben ta.

Ku kasance dani a labarina na gaba mai taken 'ƘWAI BIYU' da zai zo muku nan bada daɗewa ba.

Taku: Khadija Aliyu Ibrahim
(The Healer's Pen)

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when The Healer’s Pen Novels posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Subscribe

We will notify you when anything happens in Kano.