Mandella X

Mandella X

Share

Muslim | Health practitioner | Software developer | Digital marketer | Founder: Mandella International Services.

30/08/2026

😭🔥Wahala bata kisa... Amman idan ka kalle a wannan mahangar


゚

29/08/2026

Brain🧠 well cracked
DM FOR THE SIMPLIED PDF....
0702 537 2710

Johnson & Johnson Nursing

゚viralシ

28/08/2026

Hmm... Wallahi Kada a yaudareku ƴan Nigeria.

Daga tambayoyin da Maishanu tayi mashi a BBC zaku gane salon Campaign ne kawai.

Ku biyo ni ƙarfe 7pm
Zan ƙara maku wani haske...

Nr. Muhammad Mandella X

27/08/2026

👁️ KUYI HATTARA DA APOLLO!

Wataƙila ka taɓa samun Apollo ko kuma ka ga wani yana fama da shi. Ido ya yi ja, yana kaikayi, hawaye na fita, ko kuma akwai ɗan datti a idon (Kwantsa).

Abin da ya k**ata mu sani shi ne, Apollo yana iya yaɗuwa da sauri, musamman idan ana taɓa ido da hannu marar tsabta ko kuma ana amfani da tawul/kayan mutum ɗaya.

Kuma dn Allah, kda mu riƙa syen maganin ido da kanmu kawai saboda ido ya yi ja. Ba dk Apollo ne yake buƙatar antibiotic ba. Wasu virus ne suke haddasa shi, kuma antibiotic ba ya kashe virus.

👉 Ka riƙa wanke hannu sosai.
👉 Kada ka riƙa taɓa idonka da hannu marar tsabta.
👉 Kada ka r@ba tawul ko eye drops da wani.
👉 Idan ciwon ya yi tsanani, gani ya fara dusashewa, ko idon yana ciwo sosai, je asibiti a duba ka.

Mu daina yaɗa magani kawai saboda an ji an ce yana aiki. Ido abu ne mai muhimmanci sosai—mu kula da shi. ❤️👁️

Ka tura wa wani wannan post ɗin. Wataƙila kai ne za ka taimaka masa ya guji matsala.

26/08/2026

Ga dalilan da s**a sa nace Ku daina tsoron mutanan da ke dauke da HIV

Wasu zasuce anya inada hankali, Bari inyi maku bayani dalla dalla

HIV ba ya yaɗuwa ta kowace hanya 🩺
Sai ta hanya mu'amala kai tsaye da wasu ruwan jikin mutum mai ɗauke da ƙwayar HIV, k**ar jini (blood, maniyyi (S***m), ruwan farji, ruwan dubura da nono ( breast milk).

Haka kuma HIV na iya shiga jiki ta:

- Yin jima'i ba tare da kariya ba (Condom)
- Amfani da allura ko syringe da wani mai HIV ya yi amfani da shi.
- Daga uwa zuwa jariri lokacin ciki, haihuwa ko shayarwa.
- Ƙarin jini ko wasu ayyukan lafiya da aka yi da kayan aiki marasa tsabta.

Amma HIV ba ya yaɗuwa ta:
❌ Runguma (HUG)
❌ Gaisawa da hannu (SHAKE)
❌ Sumbatar juna ta yau da kullum (SIMPLE KISS)
❌ Amfani da bandaki ɗaya
❌ Cin abinci ko shan ruwa tare
❌ Cizon sauro ko sauran kwari

Ku daina tsoron mutanen da ke ɗauke da HIV. Ilimi da fahimta su ne hanya mafi kyau ta yaƙi da wariya. ❤️

Ku taimaka ku SHARE wannan bayanin domin wasu ma su amfana.

Nr. Mandella_2026

゚viralシ

26/08/2026

Ku daina tsoron mutanen da ke ɗauke da cutar HIV.

26/08/2026

Kashhhh🤣🤣🤣
MU SHAKATA DA WANNAN

24/08/2026

Wannan tambaya tana daga cikin abubuwan da ke yawan tayar da hankali ga mata da ma’aurata. A al’ada ana jin mutane suna cewa idan mace ta yi amfani da hanyoyin tazarar haihuwa na tsawon lokaci, mahaifarta za ta lalace ko kuma ba za ta sake samun ciki ba. Amma a mahangar kimiyya, wannan magana ba daidai ba ce.

A fahimtar ilimin lafiya, hanyoyin family planning suna aiki ne ta hanyar sarrafa yadda jikin mace ke shirya samun ciki, ba wai lalata mahaifa ba. A mafi yawan hanyoyi, ana amfani da hormones da ke k**a da waɗanda jiki ke samarwa da kansa. Wadannan hormones suna hana fitar ƙwai ko kuma su canza yanayin cikin mahaifa domin hana haɗuwar ƙwayar ƙwai da maniyyi. Wannan tsari yana faruwa ne a matakin aiki na jiki, ba wai a matakin lalata sassan mahaifa ba.

A kimiyya, mahaifa tana da ƙarfin sabuntawa da gyara kanta. Lokacin da mace ta daina amfani da family planning, jiki yana komawa yadda yake a da a hankali. Wannan yana nufin cewa tsarin al’ada da fitar ƙwai zai dawo, kuma damar samun ciki tana dawowa. A wasu hanyoyi k**ar allura, yana iya ɗaukar lokaci kafin hormones su fita daga jiki gaba ɗaya, shi ya sa wasu mata ke ganin jinkiri kafin su samu ciki. Amma wannan jinkirin ba lalacewa ba ne, sai dai jiki yana ɗaukar lokaci ya daidaita kansa.

Dalilin da ya sa wasu mutane ke tunanin cewa family planning na lalata mahaifa shi ne saboda canje-canjen da mace ke gani yayin amfani. Misali, jinin al’ada na iya raguwa ko ya tsaya na wani lokaci. Wannan yana faruwa ne saboda hormones suna rage kaurin bangon mahaifa, wanda a zahiri yana da anfani a wasu lokuta, domin yana rage yawan jini da zafi. Amma mutane da yawa suna ɗaukar wannan a matsayin matsala, alhali wani tsari ne na kimiyya.

Haka kuma, akwai bincike da dama da s**a nuna cewa amfani da hanyoyin family planning na zamani ba ya lalata mahaifa ko hana mace haihuwa a gaba. A maimakon haka, a wasu lokuta yana taimakawa wajen kare lafiyar mahaifa daga wasu matsaloli, k**ar kumburi ko wasu cututtuka da ke iya faruwa idan mace tana samun ciki akai-akai ba tare da tazara ba.

Sai dai k**ar kowanne magani, akwai yiwuwar samun wasu canje-canjen jiki, musamman a farkon amfani. Wadannan na iya haɗawa da sauyin yanayi, ciwon kai ko ɗan jiri. Amma yawanci suna raguwa da lokaci yayin da jiki ya saba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne a yi amfani da hanyar da ta dace da jikin mace, kuma a ƙarƙashin kulawar ƙwararren likita.

A ƙarshe, gaskiyar da kimiyya ta tabbatar ita ce: amfani da family planning na tsawon lokaci ba ya lalata mahaifa. Abin da yake faruwa shi ne sauyin aiki na hormones wanda yake wucin gadi. Idan mace ta daina amfani da shi, jiki yana dawowa yadda yake, kuma damar haihuwa tana nan.

Saboda haka, yana da kyau a guji yarda da jita-jita, a nemi ilimi daga masana, domin fahimtar yadda jiki ke aiki shi ne mafi girman kariya ga lafiya.

Nr. Muhammad Mandella X

゚

24/08/2026

Shin Amfani da maganin Family planning na tsawon lokaci yana haifar da wata illa ga mahaifa

24/08/2026

Naira miliyan ɗaya ba kuɗi bane ga majinyaci

Saboda haka kuje ku taimake Jarumi Tanimu Akawu

1. Ku bincike rashin lafiyarsa, idan aiki za'ayi masa ku biya kuɗin surgery.

2. Ku taimake iyalansa da abinci, muhalli, da ilimi

Jinya a babbar assibitin (University Of Jos Teaching Hospital) naira miliyan ɗaya kai tsaye zai ƙare acikin sati ɗaya.

Ku haɗa masa miliyan 10 ku hannun ta masa.

Dauda Kahutu Rarara , Ali Nuhu Mohammed, Bashir Mai Shadda, Sadiq Sani Sadiq, Lawan Ahmad, Sani Danja, Abba Almustapha, Adam A Zango , Umar M Sherrif, Ali Jita, Naziru sarkin waka Maishinko, Rahama Sadau, Hafsat Idris, Nafisat Abdullahi, Hadiza Gabon, Maryam Yahaya etc.

Abun kunya ne agareku idan kuka kasa ceto rayuwar jarumi Tanimu Akawu...
Idan har bakuyi haka ba shame on your.

Nr. Muhammad Mandella X


゚viralシ

Website