AMIH TV 3
Burimmu shine isar da saƙon Addinin Musulunci ga dukkan abin halitta.
11/09/2025
https://youtu.be/lEKYAFGX5NQ?si=iASY0bkFs7xu-iju
|| An Amazing never seen B4 || Graduation ceremony || 117 students || Attarbiyah Community College. Today marks a momentous occasion for the students of Attarbiyya Community College as they celebrate a significant milestone in their academic journey.A total...
05/10/2024
https://youtu.be/KBM39E3QTfY?si=N0TWUMxOfJTukoyX
Matsayin Sallah a Musulunci || Dr Abdullahi M Getso|| Alwajeez Fee-fikhissunati wal-kitabul Azeez 21 Darasin da yake bayani game da matsayin Sallah da girmanta a cikin addinin Musulunci
01/10/2024
Allah ta'ala ya kaimu lokacin da za mu shaida Mala'iku na dora Miki kambu na zinari a farfajiyar Alkiyama
Allah ya albarkacin Rayuwarki
19/09/2024
Yadda ake yin taimama || Dr Abdullahi M Getso || (018) Al-wajeez
A ci gaba da darasin littafin Alwajeez a wannan makon darasin ya mayar da hankali ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen *TAIMAMMA* bayan kammalawa da Babin wanka a musulunci
*Taimama* shine yin wankan tsarki ko alwala amma ba tare da yin amfani da ruwa ba saboda dalilai
Ko biyo mu ta cikin wannan bidiyo don jin kaifiyyar yadda ake taimama hukunce hukuncen ta da kuma sauran darussa da suke da alaka da tsarki
Domin kallo sai ku latsa nan
👇
https://youtu.be/uwmfdVemCSo?si=PzkKnQucdXa6d7J3
Domin shiga zaurukan malaman Sunnah sai ku tura da saƙon sallama da kuma bayyana sunan ku ga wannan lamba *+2349137671784*
Amih tv Tashar Sunnah
Yadda ake yin taimama || Dr Abdullahi M Getso || (018) Al-wajeez A ci gaba da darasin littafin Alwajeez a wannan makon darasin ya mayar da hankali ne akan abinda ya shafi hukunce hukuncen *TAIMAMMA* bayan kammalawa da Babi...
11/09/2024
https://youtu.be/C595RUEW20Q?si=qUex1-PYI-vcyAO_
Yadda mace ya kamata ta yi wankan tsarki || 017 Al-wajeez || Dr Abdullahi M Getso KITABU-ƊAHARA cikin karatun littafin Alwajeez Fee-fikhissunati wal-kitabul Azeez Mai gabatarwa Dr Abdullahi Muhammad Getso Ku ci gaba da kasancewa da shafin ...
04/08/2024
https://youtu.be/vO1dnndAwf8?si=YfVjEHi9PbuCQtsh
- YouTube Enjoy the videos and music that you love, upload original content and share it all with friends, family and the world on YouTube.
03/08/2024
Zanga-Zangar Tsadar rayuwa: "ƙilu ta ja Bau" yayin da Al'amarin ke shirin barin baya da ƙura
Tun kafin ɗaya ga watan Agusta 1/8/2024 duniyar soshiyal midiya ta ɗauki ɗumi yayin da matasa s**a riƙa jifan malamai da kausasan lafuzza na cin mutuncin, zagi, tsinuwa, cin zarafi, ƙage, da aibatawa.
Ba don komai ba sai abubuwan da su malaman s**a faɗa na hangen nesa da zurfin tunani akan shirin da ɗaukacin matasa Najeriya ke yi na kaddamar da zanga zangar da s**a kira #"ENDBADGOVERNMENT" # ko #"ZANGA-ZANGAR TSADAR RAYUWA" #
Sai dai za a iya cewa *GANI YA KORI JI* yayin da tun a ranar farko al'amurra s**a sauya daga Zanga-Zangar lumana zuwa tarzoma
Tun da farko matasan sun fito cikin fushi da fusatar halin kunci, fatara da ake ciki
sai dai daga bisani ɓata garin waɗanda da dama cikin malamai s**a yi ishara da su sai ga su sun bayyana
Inda s**a fake da wannan yanayi na zanga zangar s**a tada tarzoma tare da sace-sacen kayayyaki mallakin gwamnati da ɗai-ɗaikun mutane.
AMIH TV ta zagaya faɗin kwaryar birnin Kano kuma ta tattaro rahotanni da bayanai cikin hoto mai motsi na yadda wannan zanga zangar ta kasance
domin kallo latsa nan
👇
- YouTube Enjoy the videos and music that you love, upload original content and share it all with friends, family and the world on YouTube.
26/07/2024
An kai mutane maƙura,shugabanni su saurara, lallai a sassauta, a sauƙaƙawa mutane rayuwa wannan shine zai tabbatar da nutsuwa a cikin al'umma shine zai tabbatar da kwanciyar hankali, kuma wannan shine zai tabbatar da zaman lafiya da aminci da kyautatuwar makomar al'umma.
Wannan kira ya fito ne daga bakin limamin masallacin juma'a na Jami'ur Rahma (Kundila) Kano kuma shugaban Jami'ar Al-Istiqama dake sumaila Farfesa Salisu Shehu a yayin hudubar da ya gabatar a ranar juma'a 20/Al-muharram 1445
Farfesa ya yi zazzafar khudubar ne akan yadda shugabanni ke rub da ciki da wadaƙa da dukiyar ƙasa wadda yace tamuce ta mu duka ba wasu kebantattuba
Kazalika ya ce Najeriya za ta ci gaba da zama a matsayin ƙasa mai dunkulalliyar al'umma muddin shugabanni s**a tsai da adalci a shugabanci
Haka kuma khudubar ta zo a washe garin ziyara da s**a kaiwa shugaban ƙasa Bola Tinubu dangane da halin da Nigeria ke ciki
Yan Najeriya dai na ci gaba da kokawa bisa halin matsi da tashin Gwauron kayan masarufi da suke ciki haka kuma kwanaki kaɗan ya rage al'ummar ƙasar su tsunduma Zanga-Zanga ta tsawon kwana goma domin neman samun sassauci na tsadar rayuwa.
Domin kallo latsa nan 👇
An kai mutane maƙura || shugabanni su saurara, || lallai a sassauta, || a sauƙaƙawa mutane. An kai mutane maƙura,shugabanni su saurara, lallai a sassauta, a sauƙaƙawa mutane rayuwa wannan shine zai tabbatar da nutsuwa a cikin al'umma shine zai tabba...
24/07/2024
Daur! Daura!! Daurah!!!
Ga jadawalin yadda za a gudanar da Daura karo na 19 wanda kwamitin ilimi na Almajlisul islami Hotoro ya saba shiryawa