Kano Daily Post
Wannan Gidan jarida An buɗushine Domin Kawo muku Sahihan labarai Abinda Yake Faruwa Asassan Najeriya dama Duniya baki ɗaya
13/09/2025
13/09/2025
Yanzu Yanzu Yanda Ake Gabatar Da Bikin Takutaha yau Asabar Abirin Kano
25/08/2025
Yadda wata mota ta kwace ta bugi ginin makarantar kwalejin Rumfa dake jihar Kano a yammacin Lahadi.
Shaidun da muka tattauna da su, sun ce ba’a samu asarar rai ba.
24/08/2025
Babu batun ɗaukar Sabbin ma'aikata a gwamnatin jihar Kano a halin yanzu -Gwamnatin jihar Kano
Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati ta Jihar Kano (CSC) ta fito fili ta karyata jita-jitar da ake yadawa cewa tana sayar da takardun neman aiki ga masu neman shiga aikin gwamnati.
Hukumar ta bakin Safiyanu Bin Usman Ajingi jami'in Rahotanni na Musamman, Hukumar Ma’aikata Jihar Kan ya bayyana cewa babu wani lokaci da ta taba bayar da izinin sayar da takardun neman aiki, don haka jama’a su yi watsi da irin wannan labari marar tushe.
Hukumar ta ja hankalin jama’a da su dogara kacokan ga hanyoyin sadarwar gwamnati na hukuma domin samun sahihan bayanai kan daukar ma’aikata da sauran ayyuka. Dukkan sanarwa na hukuma za su kasance ne ta hanyar hukumomin gwamnati kawai.
Hukumar ta kara da cewa tana da cikakken kuduri wajen tabbatar da gaskiya, adalci da bin doka a duk wani shirin daukar ma’aikata. Ta kuma gargadi masu yaudara da ke amfani da sunan hukumar wajen damfarar jama’a, cewa za a hukunta su bisa ka’ida.
Ana shawartar jama’a da kada su shiga hannun masu yaudara, tare da zama masu hankali da lura.
Domin samun bayanai na gaskiya kan ayyukan hukumar, jama’a na iya bin hanyoyin sadarwar gwamnati da aka amince da su ko kuma su ziyarci ofishin Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati na Jihar Kano da ke Audu Bako Secretariat, Kano.
18/08/2025
DA DUMI DUMI Kungiyar Kwallon ƙafa Ta Barau FC Ta Samu kyakkyawar Tarba Daga Jahar katsina Bayan Ta yanke Shawar Buga Wasanninta na Gida Acan
Biyo Bayan Rashin Samun Fahimtar Juna Da Aka Samu Tsakanin Ƙungiyar Kwallaon Kafa Ta Barau Fc Da Ɓan Garen Gwamnatin Jahar Kano A kan Bawa Barau Fc Dama Su Buga Wasanninsu Na Gida A Stadium ɗin Sani Abacha Dake Ƙofar Mata cikin Tsakiyar Birnin kano
Dan Alhajee Fagolo Ya Wallafa Ashafinsa Na Facebook Irin Tarbar Da s**a Samu Kamar Haka
Yace Ajahar Kano Ance Sai Sun biya 50 millolion Sannan Abasu Dama Su buga Wasanninsu Na Gida Da kuma Sauran Tsarabe Tsarabe Yau Sunje katsina Gwamnatin Katsina Ta Amince Barau Fc Ta b**a Wasanninsu A babbar Stadium karkanda Dake Jahar Katsina sannan Kuma Naira miliyan uku da dubu ɗari Shida Zasu biya Kuɗin Hukuma Har Agama Gasar Gaba ɗaya Yace Yanzu Haka Wani Ya cire Kuɗin Ya biya Kuma Yace Wallahi Har yanzu Basu San Ko waye ba
Mai Zakuce
15/08/2025
'Barau FC kungiyar Gwamna Abba Kabir Yusuf ce da jihar Kano-Ibrahim Sh*tu Canji'
Kungiyar kwallon kafa ta Barau FC ta koka bisa abinda ta kira yi mata kafar Ungulu dangane da basu damar buga wasannin su na kakar firimiyar NPFL ta Najeriya ta 2025/26 a filin wasa na Sani Abacha.
Shugaban kungiyar Alhaji Ibrahim Sh*tu Canji ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da kungiyar ta kira da ta bayyana cewar har yanzu an ki sahalewar tawagar buga wasannin ta a filin, kasa da mako guda da fara gasar.
"Mun yi duk abinda zamu yi na cika ka'idoji tare da amincewa da biyan kudi Naira Miliyan 10, duk da cewar a Kano muke bai kamata mu biya hakan ba amma an ce ba za a bamu damar buga wasanni ba sai mun biya kimanin Naira Miliyan 50 a cewar hukumar wasanni ta jihar Kano 'Sport Commission".
"Na tabbata duk abinda ake mai Girma Gwamna Abba Kabir Yusuf bai sani ba , domin kungiyar Barau FC ta shi ce ta jihar Kano kuma Yana alfahari da ita kamar yadda yake da Kano Pillars, don haka muna kira ga re shi da ya duba tare da sa baki don bamu damar buga wasanni kafin kammala gyaran filin mu dake Dambatta" Inji Sh*tu Canji.
Shugaban na Barau ya kara da cewa tabbas Gwamna zai yi alfahari da kafa tarihi da barin Kyakyawar makoma a harkar wasanni wanda a Zamanin sa aka samu kungiyoyin firimiya biyu dake wakiltar Kano, tare da samar da dumbin aiyyuka ga al'umma da Matasa tare da kautar dasu daga shaye -shaye da rikicin Daba da fashin Waya.Don haka suna da yakinin in Gwamna ya san halin da suke ciki zai dau matakin gaggawa don bawa kungiyar dama ta buga wasannin ta a Sani Abacha a matsayin Barau FC, kungiyar sa ta biyu a Kano kana ta Al'ummar a jihar ba wai kawai Siyasa ko banbacin jam'iyya ba.
A baya dai rahotanni sun tabbatar da cewar hukumar wasanni ta jihar Kano tare da hukumar kwallon kafa sun amincewa tawagar ta Barau FC, buga wasannin ta na gida a filin na Sani Abacha a wani mataki na bata dama kafin kammala aikin filin wasan tawagar dake karamar hukumar Dambatta.
15/08/2025
INNALILLAHI: 'Yan Bindiga Sun Tare Sani Ahmad Zangina A Hanyar Abuja Zuwa Kaduna Sun Yi Awun Gaba Da Shi
Ƙasa da Awa ɗaya da Alhaji Sani ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa an samu tsaro a hanyar, sai gashi a daren jiya da misalin ƙarfe biyu na dare ɓarayi sunyi awun gaba da shi ba a san inda yake ba.
Cikakken rahoton na nan tafe...
13/08/2025
Jami'ar Wudil Ta Yi Allah-wadai Da Abinda Wasu Dalibai Mata S**a Yi Na "Ranar Cikin Ƙarya" (Fake Pregnancy Day)
Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Kano ta yi Allah-wadai da mummunar dabiʼar da wasu ɗalibai mata s**a yi da sunan ʼRanar Cikin Karyaʼ wato “Fake Pregnancy Day” ba tare da izini ba.
Arewa Updates ta rawaito wannan na cikin sanarwar da shugaban sashen kula da harkokin dalibai na jami’ar, Farfesa Abdulkadir Muhammad Dambazau, ya fitar a ranar Laraba 13 ga Agusta 2025.
Sanarwar ta ce wannan abin ya saba ka’idojin ɗabi’ar dalibai kuma ya sabawa ƙa’idojin jami’ar, tare da jawo wa makarantar mummunar illa da ɓata suna da martabarta.
Ta kuma ce jami’ar za ta gano duk wanda ya shirya ko ya taka rawa a wannan abin, tare da ɗaukar matakin ladabtarwa.
Jami’ar ta kuma yi kira ga dukkan dalibai da su kasance jakadu nagari na jami’ar, tare da neman izini kafin gudanar da kowanne irin aiki a nan gaba.
Me za ku ce?
13/08/2025
Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Rano, Muhammad Naziru Ya'u, na tsawon wata 3.
09/08/2025
Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Nemi A Haramta bikin Sign-Out A Makarantun jihar Niger.
Majalisar Dokokin Jihar Neja ta roƙi Gwamna Umaru Bago da ya haramta shagulgulan “sign-out” da “Markers’ Day” a dukkan makarantu na gwamnati da na kudi a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan mamba mai wakiltar Mazabar Tafa, Muhammad Idris, ya gabatar da kudiri inda ya bayyana cewa shagulgulan da aka fara a matsayin na ban kwana da juna yanzu sun rikide zuwa ɗabi’u marasa kyau da rashin kunya, abin da ke barazana ga tarbiyya da ilimi.
‘Yan majalisar sun amince da kudirin baki ɗaya, tare da yin kira ga gwamnati ta hanzarta aiwatar da dokar hana hakan.
Mataimakiyar Kakakin Majalisar, Afiniki Dauda, ta ce za ta yi aiki tare da Gwamna da Ma’aikatar Ilimi don tabbatar da aiwatar da wannan doka cikin gaggawa.
Haka kuma, majalisar ta amince da gyara dokar kafa Minna Institute of Technology and Innovation domin ta dace da bukatun zamani da ci gaban ilimi.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
977689