Vision FM Kano

Vision FM Kano

Share

VISION FM KANO 92.5
SAMAR MUKU DA SAHIHAN LABARAI A KODA YAUSHE SHINE MURADIN MU. MIKIYA MAI HANGEN NESA

20/09/2026

Zamu duk abunda yakamata dan ganin dan takarar mu na Sanatan Kano ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya sami nasara a zaben 2027.

Hon. Garba Nuhu Sarki
Shugaban Kungiyar A.A Zaura Grassroot Mobilization

20/09/2026

Ƙungiyar Nigeria Forward ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a siyasar Arewacin Najeriya da su mutunta tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu, tare da barin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas. Mataimakin mai haɗa kan ƙungiyar, kuma Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan a wajen ƙaddamar da ƙungiyar a Abuja.
‎
‎Waiya ya ce tun bayan komawar Najeriya tsarin dimokuraɗiyya a shekarar 1999, an riƙa amfani da tsarin raba madafun iko tsakanin Arewa da Kudu domin ƙarfafa haɗin kan ƙasa. Ya ce komawa da shugabanci Arewa bayan wa’adi ɗaya kacal zai iya kawo cikas ga tsarin, yana mai cewa kammala wa’adin shekaru takwas zai ba gwamnatin Tinubu damar ci gaba da manufofi da shirye-shiryenta.
‎
‎A nasa jawabin, Ministan Ƙirƙire-Ƙirƙire, Kimiyya da Fasaha kuma mataimakin mai haɗa kan ƙungiyar, Dakta Kingsley Tochukwu Udeh, ya ce Nigeria Forward za ta mayar da hankali wajen haɗa manufofin gwamnati da jama’a, tare da ƙara fahimtar ayyuka, zuba jari da damammaki. Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya su goyi bayan sake zaɓen Tinubu a 2027 domin ci gaba da sauye-sauyen gwamnatin.

20/09/2026

‎Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce a shirye yake ya yafe wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da sasanta da shi idan ya nuna sha’awar yin hakan. Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da BBC Hausa, yayin da yake magana kan rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu bayan Gwamna Abba Yusuf ya fice daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
‎
‎Kwankwaso ya ce bai yi watsi da Abba Yusuf ba, kuma bai kore shi ko ya nemi ya sauya jam’iyya ba, yana mai cewa har yanzu yana son sa. Ya kuma ce ba mutum ne mai ɗaukar fansa ba, inda ya bayar da misalin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, cewa duk da rashin jituwar da ta shiga tsakaninsu a baya, ya yafe masa kuma s**a ci gaba da harkokin siyasa tare.
‎
‎Kwankwaso, wanda yanzu yake cikin jam’iyyar NDC, ya ce ba ya kallon kansa a matsayin jagoran da ke tilasta wa mutane abin da za su yi, yana mai cewa ya kamata a yi haƙuri da yafiya a harkokin siyasa. Ya kuma ce ba sa neman kuɗi daga mutanen da s**a samu goyon bayansu domin tsayawa takara, sannan ba sa sayar da takarar jam’iyya.

Photos from Vision FM Kano's post 20/09/2026

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gana da shugabancin jam’iyyar APC na Kano, ƙarƙashin jagorancin Umar Haruna Doguwa, domin tattauna batutuwan da s**a shafi siyasar jihar wanda ya gudana a ranar Asabar.

Bangarorin biyu sun tattauna kan hanyoyin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, inda ganawar ta mayar da hankali kan batutuwan siyasa da kuma yadda za a tsara matakai da dabarun da s**a dace da yanayin siyasar Kano gabanin zaɓen.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen shekarar 2027.

19/09/2026

Zanga-zangar wanda ɗan gwagwarmayar nan Comrade Mujahid Muhammad zai jagoranta za a gudanar da ita a ranar 1 ga Oktoba.

Mujahid ya ce zanga-zangar za ta kasance ta lumana, domin neman adalci da cikakken bincike kan lamarin.

Ya ce masu zanga-zangar za su nemi a gudanar da bincike na gaskiya, a bayyana abin da ya faru, a yi adalci ga waɗanda abin ya shafa, tare da ɗaukar matakan kare rayukan al’umma.

17/09/2026

Mutane bakwai, ciki har da ƙananan yara ’yan makaranta, sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a yankin Rimin Auzinawa, Mangoro Uku, da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.
‎
‎Comr. Mujahid Muhammad ya shaida cewa hatsarin ya faru ne a daren Laraba. Bayan faruwar hatsarin, wasu matasa a yankin sun kona wata motar ɗaukar yashi, bisa zargin cewa motar ta bi ta kansu, lamarin da ya ƙara jefa yankin cikin tashin hankali.
‎
‎Mazauna yankin sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta ɗaukar matakan rage haɗurran da ke faruwa a titin Rimin Auzinawa, ciki har da faɗaɗa titin da inganta tsarin zirga-zirga. Sun ce wannan ba shi ne karo na farko da aka samu mummunan hatsari a yankin ba.

16/09/2026

Shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafe-Ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, Saidu Yahaya, ya yi murabus daga muƙaminsa.
‎
‎Rahotanni sun ce Saidu Yahaya ya miƙa takardar murabus ɗinsa ne ranar Talata, bayan matsin lamba daga gwamnatin Jihar Kano kan zargin rashin gudanar da ayyukansa yadda ake tsammani.
‎
‎An naɗa Saidu Yahaya a matsayin shugaban hukumar a watan Agustan 2025, bayan karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado. Sakatariyar shari’a ta hukumar, Hafsat Kutama, ce ake sa ran za ta riƙe muƙamin shugabar riƙo daga yau Laraba.

16/09/2026

Martanin Zee Gombe kan fitar da tattaunawar ta da dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Gombe Farfesa Isa Ali Pantami.

Me zaku ce?

15/09/2026

Bana goyon bayan abunda akayiwa Dan bilki Kwamanda a wajen daurin aure, a dinga adawanta hankali ba ta cin mutunci ba...

S.A Yakubu Dan Gawan Jingau
Dan Jam'iyyar APC

15/09/2026

Babu maganar goyon bayan wani dan takara ba shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ba.

Jamilu Gwamna
Dan takarar gwamna na jihar Gombe

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Address

Guda Abdullahi
Kano
700101