Aisha's friends

Aisha's friends

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Aisha's friends, Health/Beauty, Nassarawa, Kano.

12/04/2026

Shirin Labarina Dafa-Duka Ne

Duka waÉ—annan, wasu bangarori ne daga cikin shirin da ke tafe.

Duk wani abu da ku ke son gani da ma wadda ba ku yi tunani ba, duk ya na cikin wannan sabon shirin na mu.

Season guda 3 mu ka dauka na shirin. Season 15, Season 16 da kuma Season 17 da mu ke kan aikin sa yanzu haka. Sakonni ne fal a cikin sa da su ka shafi rayuwar yau da kullum.

- Ahmad Nagudu

**


searie15

Photos from Aisha's friends's post 12/04/2026

Abubuwan da s**a faru Bodyguard din su Hanan Yana Neman Hana mansur zuwa wajen Hanan Amma daga baya ya samu zama da mahaifin su Hanan Sannan maman don nass ta fada don nass magana Mai daci tace ita aganinta Mansur ma watakila Yana can Yana hutawarsa da GLA
Mansur yayi wa baban su hanan bayani cewa babban coin din shi ne ya fashe👀😅
Bello yana cikin wani Hali Zabi biyu season 2 episode 5 yanan zuwa yau a talabijin na Arewa 24 da Kuma on demand ku kasance damu Koda yaushe✨

Photos from Aisha's friends's post 12/04/2026

LABARINA SEASON 15 OFFICIAL TEASER...

Tallan yayi kyau duk da mutane sunyi zaton zasu ga ci gaban Labarin su Abba Galadima Presido da Kilishin Gabas, sai s**a ga wani sabon labarin daban k**ar yadda Movies s**a tsara.

Zamu iya cewa wannan shine labari na uku kenan bayan labarin Labarin su Al-ameen Mai Nasara da Maryam.

Wannan labarin an gina shi akan matsalolin tsaro yadda ake sace Mata a kauyuka da makarantun kwana a ringa cin zarafin su a daidai lokacin da gwamnati take nuna halin ko in kula ta bar iyaye suyi ta ƙuncin rashin ƴaƴansu.

Amma bisa al'adar mafi yawancin Kannywood Series idan suna son jan labari yayi tsayi su kan shigo da wasu abubuwan da tun farko ba'a gina ginshikin labarin akansu ba.

Na yarda da ƙwarewar Saira Movies kuma suna yin duk mai yiyuwa wajen ganin labari bai ƙwace musu ba yadda ba zai yi saurin ginsar ƴan kallo ba.

Budget Babbar matsalar da take damun masana'anatar Kannywood a yanzu shine Budget saboda a harkar film duk kyawun labari da ƙwarewar Masu bada umarni da Jaruman da zasu taka rawa, idan har babu isassun kuɗin da za'a yi komai a zamanance sai kaga Film ya rage armashi.

Misali acikin tallan wajen da aka nuna jirgin Sojoji ya sauka a Daji Ƴan Ta'adda sunyi Bombing ɗinsa wajen yafi k**a da Insert ne ba wai Jirgin gaske bane ba, bansan nawa ne kuɗin hayar jirgi shiyasa yawanci finafinan Kannywood idan zasu nuno maka jirgi ko Mota zaka ga k**ar Insert ne kawai.

Dole kayi musu uzuri saboda hanyoyin samun kuÉ—in ne har yanzu ba k**ar na sauran film industries ba don haka kowanne Producer yana zuba kuÉ—i ne daidai da yadda yasan zasu dawo yaci riba.

04/03/2026
Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Nassarawa
Kano