Dangel HUB
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dangel HUB, Bauchi, Kano.
Dangel HUB is a digital home for an organised grassroots movement built around, ideas, reforms and Community, we believe meaningful progress begins with organised peaple, responsible participation and putting communities First. #BeOrganised#CommunityFirst
07/09/2026
SARKIN MUSULMI YA KAI ZIYARAR TAZIYYA GUMEL KAN RASUWAR SARKIN GUMEL
Sarkin Musulmi, Mai Martaba Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya kai ziyarar taziyya Gumel, Jihar Jigawa, kan rasuwar Sarkin Gumel, Alhaji (Dr.) Ahmad Muhammad Sani II.
Gwamna Umar Namadi ya karɓe shi, inda ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama, ya sa shi Aljannatul Firdaus.
Allahu Akbar Mutuwa Rigar Kowa
06/09/2026
Fitowan Mai Martaba Sarkin Misau Alh Ahmed Suleiman MNI, domin ganin maulud na 2026.
Allah ya karawa Annabi daraja. Amin
Ran sarki yadade✊🏾
Amadadin Hukumar Gidauniyar Dengel HUB Tana sanar muku zata kawo muku Taron Muzaharar Maulidi Kai tsaye wato Live daga karamar Hukumar Misau LGA
05/09/2026
An gudanar da wani muhimmin taron Majalisar Taraiya Dana Jiha, inda Hon. Sabo Baffayo Ahmad Dagauda, Mainan Misau, tare da Hon. Baballe Abubakar, s**a gana da Ward EXCO na mazabu biyar, wato Yame, Garuza, Yanda, Janda da Jalam. Taron ya kasance wata muhimmiyar dama ta tattauna batutuwan da s**a shafi jam’iyya, karfafa zumunci da hadin kai, da kuma sauraron ra’ayoyi da shawarwarin shugabannin mazabu domin samun ingantacciyar fahimtar juna da kyakkyawan tsarin aiki tare. Wannan irin zama yana kara nuna muhimmancin hadin kai da tuntubar juna wajen gina kyakkyawar makoma da tabbatar da ci gaba a tsakanin al’umma.
31/07/2026
TAJDIDI DA JIHADIN SHEHU USMAN ƊAN FODIO: ME TARIHI YA TABBATAR?
Kashi na Bakwai
Abdussalam da Gimbana: Lamarin da Ya Kawo Rikici Kafin Tabkin Kwotto
A tarihin da ya kai ga Jihadin Shehu Usman Ɗan Fodio, akwai wani lamari mai matuƙar muhimmanci da bai k**ata mu tsallake shi ba, abin da ya faru da Abdussalam da al'ummarsa a Gimbana.
Abdussalam, malami ne ɗan Arewa, bahaushe kuma ɗaya daga cikin fitattun almajiran Shehu Usman Ɗan Fodio. Ya kasance yana da nasa mabiya tun kafin ya zama almajirin Shehu, sannan daga baya ya zama ɗaya daga cikin manyan jagororin tafiyar Shehu.
Tun kafin babban rikicin 1804, Abdussalam da mabiyansa sun yi hijira daga yankin Gobir zuwa Gimbana, a yankin Kebbi, bayan ƙara tsanantar rashin jituwar da ke tsakaninsu da masarautar Gobir. A can ne ya kafa wata al'umma wadda ta ci gaba da gudanar da rayuwarta ƙarƙashin jagorancinsa.
Daga baya, bayan Yunfa ya hau karagar mulkin Gobir, ya nemi Abdussalam ya koma ƙarƙashin ikon Gobir domin ya fuskanci hukunci. Abdussalam ya ƙi komawa.
A shekarar 1803 zuwa 1804, Yunfa ya aika da runduna zuwa Gimbana domin kamo Abdussalam. Amma Abdussalam ya samu damar tserewa daga garin kafin a k**a shi. Sai rundunar Gobir ta shiga Gimbana.
Abin da ya biyo baya shi ne abin da ya sa wannan lamari ya zama muhimmin jigo a tarihin jihadin, an washe garin, aka k**a mutane da dama, sannan aka tafi da su a matsayin fursunoni zuwa yankin Gobir. Wasu bayanan sun bayyana cewa an kuma kwashe dukiyoyi, yayin da wasu daga cikin mazauna garin s**a rasa rayukansu.
A lokacin da rundunar Gobir take dawowa da mutanen da aka k**a, hanyar da s**a bi ta kusa da Degel, inda jama'ar Shehu suke. A nan ne lamarin ya ɗauki sabon salo.
Mabiyan Shehu da ke Degel sun fahimci cewa ana wucewa da wasu Musulmi da aka k**a daga Gimbana. Sai wasu daga cikin jama'ar Shehu s**a shirya kwanton ɓauna ga rundunar Gobir.
A arangamar da ta biyo baya, mabiyan Shehu s**a yi nasara a kan waɗanda suke rakiyar mutanen da aka kamo, sannan s**a ƙwato duka mutanen da aka kamo ɗin. A nan ne aka samu wani sabon yanayi, jama'ar Shehu sun shiga arangama da sojojin Gobir kafin babban Yaƙin Tabkin Kwotto.
Wasu bayanai sun nuna cewa wannan ɗaukar matakin da jama'ar Degel s**a yi ba tare da tuntuɓar Shehu kai tsaye ba ne. An bayyana cewa Shehu bai ɗauki matakin da s**a yi a matsayin abin da ya k**ata a gaggauta ba, domin yana ganin za a iya kauce wa wannan arangama. Wannan bayani yana da matuƙar muhimmanci wajen fahimtar tarihin cikin adalci.
Domin babu wata hujja da ta nuna cewa: "Shehu ya umarci mabiyansa su kai wa Gobir hari a Gimbana." Amma idan muka ce: "An samu arangama tsakanin mabiyan Shehu da rundunar Gobir bayan an kai hari Gimbana, kuma an ƙwato mutanen da aka k**a." wannan ya fi dacewa da abin da tahiri ya tabbatar.
A nan ne kuma Yunfa ya ƙara fusata. Lamarin Gimbana da ƙwato fursunonin ya zama babban sauyi a dangantakar da ke tsakanin Yunfa da Shehu. Wasu bayanan tarihi sun danganta wannan lamari da umarnin Yunfa ga Shehu na ya bar yankin tare da danginsa, amma ba tare da ya ɗauki dukkan jama'arsa ba. Shehu ya ƙi rabuwa da jama'arsa, kuma daga nan ne hijirar Degel zuwa Gudu ta zama dole.
Saboda haka, idan muna son fahimtar tarihin Jihadin Shehu Usman Ɗan Fodio da gaskiya, ba za mu tsallake tarihin abinda ya faru a Gimbana ba. Rikicin Gimbana ya nuna mana cewa kafin y@ƙin Tabkin Kwotto an riga an samu: Hari, k**a mutane, kwanton ɓauna, arangama, ƙwato waɗanda aka k**a a matsayin fursunoni, ƙarin fusata tsakanin Yunfa da jama'ar Shehu.
Wannan jerin abubuwan za su fi taimaka mana wajen fahimtar abin da ya biyo baya fiye da cewa kawai: "Shehu ya yi hijira, sannan aka yi y@ƙin Tabkin Kwotto."
Tarihi ba haka yake gudana ba. Akwai matakai tsakanin waɗannan abubuwa, kuma kowane mataki yana da muhimmiyar rawa. Haka kuma, lamarin Gimbana yana ƙara nuna mana cewa ba za a iya bayyana rikicin da kalmar "Fulani sun yaƙi Hausawa" kawai ba.
Abdussalam kansa malami ne ɗan Arewa kuma bahaushe, sannan ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin Jihadin Shehu. Wannan lamari shi kaɗai ya isa ya nuna cewa ƙabilanci bai isa ya bayyana tsarin da ya haifar da wannan rikici ba.
Abin tambaya: Bayan abin da ya faru a Gimbana da kuma hijirar Shehu zuwa Gudu, wa ya ɗauki matakin soja na gaba? Shin Yunfa ne ya tura rundunarsa zuwa Gudu? Ko kuwa mabiyan Shehu ne su ka fara kai hare-hare? Kuma mene ne ainihin abin da ya faru kafin Y@ƙin Tabkin Kwotto?
A Kashi na Takwas, za mu bi waɗannan abubuwan ɗaya bayan ɗaya har mu isa Tabkin Kwotto, ba tare da tsallake wani muhimmin mataki ba.
Yakubu Ahmad Yaya
31/07/2026
30/07/2026
TAJDIDI DA JIHADIN SHEHU USMAN ƊAN FODIO: ME TARIHI YA TABBATAR?
Kashi na Shida
Bayan Hijira: Me Ya Faru a Gudu?
A ranar 21 ga Fabrairu 1804, Shehu Usman Ɗan Fodio da mabiyansa s**a bar Degel s**a nufi Gudu.
Amma abin da ya faru bayan wannan hijira shi ne ya fi muhimmanci wajen fahimtar yadda al'amura s**a kai ga arangamar y@ƙ!.
A Gudu, tafiyar Shehu ta shiga wani sabon mataki. Mabiyansa sun ƙara haɗuwa a ƙarƙashin jagorancinsa, kuma s**a kafa tsarin shugabanci wanda ya ba wannan al'umma sabon matsayi na siyasa da addini.
Wannan shi ne abin da ya bambanta zaman Gudu da zaman Degel.
A Degel, Shehu yana cikin tsarin mulkin Gobir ne, duk da tasirinsa da yawan mabiyansa. Bayan hijira kuwa, mabiyansa sun zama wata al'umma mai nata jagoranci, wadda s**a fara gudanar da harkokinsu ba tare da kasancewa ƙarƙashin ikon gwamnatin Gobir kai tsaye ba.
A wannan lokaci ne kuma aka ƙara bayyana sabon matsayi na Shehu a matsayin jagoran al'ummar da s**a yi masa mubaya'a.
Wannan sauyi bai kasance abin da gwamnatin Gobir za ta iya kallonsa da sauƙi ba.
Daga mahangar Gobir, wani yanki na mutanen da a baya suke ƙarƙashin ikonta yanzu sun bar ƙasar s**a kafa wata al'umma mai cin gashin kanta. Daga mahangar mabiyan Shehu kuwa, sun yi amfani da damar da s**a samu wajen gudanar da rayuwa bisa tsarin da s**a yi imani da shi.
Saboda haka, bayan hijira, rikicin ya daina kasancewa tsakanin malami da sarki kawai. Ya fara ɗaukar siffar rikici tsakanin ƙungiyoyin siyasa masu iko daban-daban.
A cikin wannan yanayi ne Gobir ta ɗauki matakan y@ƙ!.
Babban arangamar da ta biyo baya ita ce Y@ƙin Tabkin Kwotto, wanda ya faru a ranar 21 ga Yuni 1804.
Wannan yaƙi yana da muhimmiyar rawa a tarihin Jihadin Shehu, domin shi ne ɗaya daga cikin manyan arangamomin farko da s**a nuna cewa rikicin ya shiga matakin y@ƙi kai tsaye.
Amma kafin mu yanke hukunci kan wanda ya fara y@ƙin, akwai wani abu da ya k**ata mu fahimta.
Ba Fulani ne kaɗai a ɓangaren Shehu ba, kuma ba Hausawa ne kaɗai waɗanda s**a kasance a ɓangaren Gobir ba.
Fahimtar wannan yana da mahimmanci.
Akwai Hausawa da s**a shiga cikin jama'ar Shehu, k**ar yadda akwai Fulani da ba su kasance cikin tafiyar ba. Saboda haka, amfani da kalmomin "y@ƙin Fulani da Hausawa" wajen bayyana wannan rikici yana iya ɓoye ainihin yanayin siyasa da addini da ya kasance a lokacin.
Rikicin ya ƙunshi mutane da ƙungiyoyi daban-daban masu dalilai da matsayi daban-daban.
Saboda haka, idan muka koma ga tarihin Tabkin Kwotto, tambayar da za mu yi ba ita ce kawai:
"Fulani sun yaƙi Hausawa ne?"
Tambayar da ta fi dacewa ita ce:
"Waɗanne rundunoni ne s**a yi arangama, me ya kai su fagen daga, kuma wane mataki ne kowane ɓangare ya ɗauka kafin arangamar?"
Wannan shi ne bambancin binciken tarihi da labarin da aka gina bisa ƙabilanci.
Idan muka amsa waɗannan tambayoyi daidai, za mu fara fahimtar abin da ya faru ba tare da jingina wa ƙabila ɗaya dukkan abin da ya faru ba.
A kashi na gaba, za mu shiga cikin Yaƙin Tabkin Kwotto kai tsaye: yadda arangamar ta kasance, waɗanda s**a shiga cikinta, sak**akonta, da kuma abin da wannan yaƙi ya nuna game da tambayar da ta fi tayar da muhawara:
Shin Shehu Usman Ɗan Fodio ne ya fara yaƙin, ko kuwa Gobir ce ta fara kai masa hari?
Yakubu Ahmad Yaya
30/07/2026
29/07/2026
TAJDIDI DA JIHADIN SHEHU USMAN ƊAN FODIO: ME TARIHI YA TABBATAR?
Kashi na Biyar
Sarkin Gobir Yunfa da Shehu Usman Ɗan Fodio: Ta Yaya Dangantaka Ta Rikiɗe Zuwa Rikici?
Bayan rasuwar Sarkin Gobir Nafata, Yunfa ya hau karagar mulkin Gobir. Hawansa ya zama wani sabon babi a tarihin dangantakar Masarautar Gobir da Shehu Usman Ɗan Fodio.
Akwai wani bayani da ya shahara a tarihin jihadi cewa Yunfa ya taɓa karatu ko neman ilimi a wajen Shehu. Wannan bayani ya zo a cikin wasu rubuce-rubucen tarihi, kuma masana da dama sun ambace shi. Sai dai akwai bambance-bambancen bayanai kan irin zurfin wannan alaƙa. Saboda haka, abin da muke faɗa da tabbaci shi ne Yunfa da Shehu sun san juna tun kafin rikicin ya ɓarke.
Da Yunfa ya zama sarki, dangantakar da ke tsakaninsu ta fara lalacewa. Dalilin hakan ba abu guda ba ne. Masana tarihi sun kawo abubuwa da dama, ciki har da ƙaruwar tasirin tafiyar Shehu, tsoron gwamnati kan yawan mabiyansa, da kuma rashin jituwa kan yadda ya k**ata a tafiyar da harkokin addini da mulki.
A wannan lokaci, masarautar Gobir ta fara kallon al'ummar da ke kewaye da Shehu a matsayin wata ƙungiya ko al'umma mai cin gashin kanta. A gefe guda kuma, mabiyan Shehu suna ganin suna da ƴancin gudanar da addininsu da rayuwarsu ba tare da tsangwama ba.
Wannan rashin fahimtar juna ya ƙara tsananta rikicin.
Ɗaya daga cikin fitattun abubuwan da tarihi ya ambata shi ne yunƙurin kashe Shehu. Rubuce-rubucen tarihi da dama sun bayyana cewa Yunfa ya taɓa yunƙurin harbin Shehu da bindiga, amma yunƙurin bai yi nasara ba. Ko da yake masana suna da bambancin bayanai kan yadda lamarin ya faru dalla-dalla, mafi yawan tarihin jihadin Sakkwato sun ɗauki wannan a matsayin ɗaya daga cikin alamomin cewa dangantakar ta kai matakin da ba za ta iya komawa yadda take a da ba.
Bayan wannan, matsin lamba kan Shehu da mabiyansa ya ƙaru. An fara ɗaukar matakan da s**a ƙara takaita motsinsu da harkokinsu.
Abin lura shi ne cewa, duk da tsananin wannan yanayi, babu wata hujjar tarihi da ta nuna cewa Shehu ya tattara runduna ya kai wa Gobir farmaki a wannan mataki. Maimakon haka, abubuwan da s**a biyo baya sun kai shi ga yanke shawarar barin Degel tare da mabiyansa.
Wannan shi ne abin da masana tarihi s**a bayyana a matsayin Hijirar Gudu, wadda ta zama ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da s**a sauya tarihin yankin baki ɗaya.
Akwai darasi mai muhimmanci da ya k**ata mu ɗauka daga wannan babi na tarihi. Idan aka duba abubuwan da s**a faru tun daga zamanin Bawa Jan Gwarzo zuwa Nafata, sannan Yunfa, za a ga cewa rikicin bai fara ne da yaƙi ba. Ya fara ne da sauyin dangantaka tsakanin malami da gwamnati, wanda daga baya ya rikide zuwa rikicin siyasa da tsaro.
Saboda haka, ba zai zama adalci ba a taƙaita wannan tarihi da cewa:
"Shehu ya wayi gari ya yaƙi sarakunan Hausa."
Abin da tarihi ya nuna shi ne cewa an samu jerin abubuwan da s**a faru a hankali, kuma kowanne mataki ya share hanya ga wanda ya biyo bayansa.
A kashi na shida za mu shiga ɗaya daga cikin manyan abubuwan da s**a sauya tarihin yankin: Hijirar Shehu Usman Ɗan Fodio daga Degel zuwa Gudu.
Za mu bincika dalilan hijirar, abin da ya faru bayan isarsu Gudu, da kuma yadda wannan hijira ta zama mafarin sabon tsarin siyasa da addini wanda daga baya ya kai ga barkewar yaƙi.
Yakubu Ahmad Yaya
29/07/2026
28/07/2026
TAJDIDI DA JIHADIN SHEHU USMAN ƊAN FODIO: ME TARIHI YA TABBATAR?
Kashi na Huɗu
Dokokin Sarkin Gobir Nafata: Farkon Rikicin Siyasa da Addini
Bayan da wa'azin Shehu Usman Ɗan Fodio ya bazu a sassa daban-daban na Masarautar Gobir da ma wasu ƙasashen Hausa, yawan mabiyansa ya ci gaba da ƙaruwa. Wannan ci gaba ya jawo hankalin shugabannin Gobir, waɗanda s**a fara kallon tafiyar a matsayin wani barazana da zai iya tasiri a harkokin masarauta.
A zamanin Sarkin Gobir Nafata, an ɗauki wasu matakai da masana tarihi s**a bayyana a matsayin farkon takun saƙar da ya kai ga rikicin da ya biyo baya.
Daga cikin matakan da aka ɗauka akwai hana wasu mutane ƙara shiga cikin tafiyar Shehu, takaita wa'azi, da sanya wasu ƙa'idoji da s**a shafi mabiyansa. Wasu bayanan tarihi sun kuma nuna cewa an hana mutane da dama yin hijira zuwa inda Shehu yake ko shiga cikin al'ummarsa ba tare da amincewar gwamnati ba.
Ko da yake masana tarihi sun bambanta a kan cikakkun bayanan wasu daga cikin waɗannan dokoki, kusan dukansu sun yi ittifaki cewa masarautar Gobir ta fara ɗaukar matakan da s**a rage wa Shehu da mabiyansa ƴancin gudanar da harkokinsu k**ar yadda s**a saba.
Tambayar da mai bincike zai yi ita ce: Me ya sa aka ɗauki waɗannan matakai?
Akwai ra'ayoyi biyu da masana s**a fi kawowa.
Ra'ayi na farko shi ne cewa shugabannin Gobir sun ji tsoron yadda tafiyar Shehu take ƙara samun karɓuwa, musamman kasancewar mabiyansa suna fitowa daga kowane ɓangare na al'umma, ciki har da wasu masu muƙamai a masarauta.
Ra'ayi na biyu kuwa shi ne cewa sarakunan suna ganin dole ne su kare ikon gwamnati daga duk wata ƙungiya da za ta iya zama wata cibiya ta daban. A tsarin mulkin wancan lokaci, duk wata ƙungiya mai yawan mabiya tana iya zama abin damuwa ga mai mulki.
Ko wane daga cikin waɗannan ra'ayoyin aka ɗauka, abu ɗaya ya fito fili: dangantakar da ta daɗe tana tafiya cikin lumana ta fara sauyawa.
Abin lura shi ne, duk da waɗannan takunkumai, babu wata hujjar tarihi da ta nuna cewa Shehu ya ayyana yaƙi a lokacin Nafata. Maimakon haka, ya ci gaba da koyarwa da rubuce-rubuce, yana ƙarfafa mabiyansa su tsaya kan koyarwar Musulunci.
Wannan yana da muhimmanci saboda yana warware wata fahimta da ake yaɗawa a yau cewa rikicin ya fara ne da ɗaukar makami. Tarihi ya nuna cewa kafin yaƙi ya fara, an shafe lokaci ana samun saɓanin siyasa, takunkumai, da rashin jituwa tsakanin bangarorin biyu.
A ilimin tarihi, irin waɗannan matakai s**an zama farkon manyan rikice-rikice. Lokacin da gwamnati ta fara taƙaita wata tafiya mai tasiri, kuma ita tafiyar ta ci gaba da faɗaɗa, sau da yawa rikici kan ƙara tsananta idan ba a samu mafita ta lumana ba.
Saboda haka, ana iya cewa matakan da Sarkin Gobir Nafata ya ɗauka sun kasance wani muhimmin juyi a tarihin Tajdidi. Daga wannan lokaci ne dangantakar da ta taɓa kasancewa ta mutunta juna ta fara shiga sabon yanayi na rashin amincewa.
Sai dai, duk da haka, rikicin bai kai ga yaƙi ba a zamanin Nafata.
Babban sauyin da ya kai ga hijira da daga baya yaƙi ya faru ne bayan wani sabon sarki ya hau karagar Gobir.
Shi ne Yunfa.
A kashi na biyar, za mu binciki dangantakar Shehu Usman Ɗan Fodio da Sarkin Gobir Yunfa. Shin da gaske ne Yunfa ya taɓa zama ɗalibin Shehu? Me ya sa dangantakar da ta fara da kusanci ta rikiɗe zuwa gaba mai tsanani? Kuma wane matsayi wannan ya taka wajen abubuwan da s**a biyo baya?
Yakubu Ahmad Yaya
28/07/2026
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Kano