Abu ja'afar media
ku tunatar domin tunatar tana Amfanar mumini
Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Garba Ya'u, Umina Dmamana, Sabo Yunusa, Aminu Musa, Shaaibu Abubakar
19/07/2026
وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيمًا وَمُلْكًا كَبِيرًا
Iya kar wannan ayah. ta'isa tasaka Kayi duk mai yiyiwa. Idan ka mutu kashi ga Aljanna. Allah ka yarda damu ka yarda da Ayyukan mu. Kayiwa magabatan mu. Gafara muma Kayi Mana Afuwa a kan ayyukan mu. Munana. Barka da juma'a. Allah ya karbi ibadun mu. Abu ja'afar media . 👉🇳🇬🇳🇬🇳🇬🤲🏻🤲🏻🤲🏻🤲🏻
02/07/2026
Rayuwar mu tana. Da Alaqa da rayuwar magabatan mu.
Zan baku wani Labari. Wanda ya faru dani. Jibrin. Adam. Kamar wata daya baya. Wani. Almajiri. Yana zaune. Yana bara. Naje wucewa. Sai zuciyata ta tuna. Da kakata. Hajara musa. Ladan. Saina ba wannan Almajiri. Sadaka. Kimar Abin da na bashi. Bai wuce. 1k. Azuciya ta. Nace. Ya ubangiji nayi wannan Sadaka. Sabo da kakata. Ka gafarta mata ka haskaka kabarin ta. Ba yan sati. Biyu. Na kwanta barci. Sainayi mafarkinta. Naje wajenta. Data ganni maganar data fito bakin ta shine. Tana kirana da wani. sun (ciba Aiki) tacemun ciba Aiki dama kananan. ? Nace. mata eh. Inanan. Tacemin naga sakon ka nagode. na zauna. Muna hira. tsawon lokaci. Kawai saina farka. Daga. barci. saina tuna Abinda nayi mata na waccen sadakar. Duk sanda ka tuna da wani makusan cinka Wanda ya mutu. Kayi mashi. Addu'a wallahi Allah Yana. Karba. Wannan baiwar Allah Hajara. Ta koma ga Allah. Sama da shekaru. 25. Amma kuma Allah ya hadani da ita Acikin mafarki. Mu kyautata wa mama tanmu. Sakon yana isa inda suke. Dake Hajara. Musa ladan. Da Mijin ki. Malam. Musa. Ladan m/k. Allah ka kara haskaka. Kabarin su Amin summa Amin. Abu ja'afar media 👉🇳🇬🇳🇬🇳🇬🤲🏻🤲🏻🤲🏻
With Abu Ja'afar – I'm on a streak! I've been a top fan for 7 months in a row. 🎉
21/06/2026
BA ZA SU TAIMAKE KA BA, KUMA BA ZA SU BAR WANI YA TAIMAKE KA BA...
A mafi yawan al'ummomin da muke rayuwa a ciki, wannan shi ne abin da ake gani.
Shawarata gare ka, idan ka karanta wannan rubutu:
Kana da baiwa? Kana da wata ƙwarewa, sana'a ko kasuwanci?
Ka tsaya ka yi tunani. Wannan ƙwarewar taka tana ba ka abin da kake so a inda kake yanzu? Ko kuwa kana ci gaba da zama a wuri guda ba tare da wani gagarumin ci gaba ba?
Idan ƙwarewarka ta fi ƙarfin garin da kake, to ba ka da dalilin ci gaba da zama a wurin.
Ka canza muhalli (location).
Sau da yawa, canza muhalli ne ke ƙara darajar aiki, yana kuma ƙara samun kuɗin shiga.
Ko da kuwa kana da ƙwarewa sosai, idan mutanen wurin ba sa buƙatar abin da kake yi, ko kuma ba su da ƙarfin biyan kuɗinsa, zai yi wuya ka cimma burinka a wurin.
Ka yi tunani:
Da ace Aliko Dangote ya tsaya a Kano kawai ba tare da ya faɗaɗa harkokinsa ba, kana ganin zai kai matsayin da yake a yau?
Saboda haka, idan kai ƙwararre ne a aikinka kuma ka ga wurin da kake ya kasa ba ka damar bunƙasa, ka nemi sabon muhalli da ya dace da ƙwarewarka.
Aikin da kake yi a wani wuri a ba ka ₦2,000, irin wannan aikin za ka iya yi a wani wuri da ya dace da kai a ba ka ₦10,000 ko fiye.
Barka da hutun ƙarshen mako.
Allah Ya taimake mu cikin sana'o'inmu da kasuwancinmu. Ya albarkaci abin da muke yi, Ya rufa mana asiri a duniya da lahira.
Amin. 🤲🏽 Abu ja'afar media
Halin da kasar take ciki kenan
With Abu Ja'afar – I'm on a streak! I've been a top fan for 5 months in a row. 🎉
Listen to the end my brother and sharing this is very important
Click here to claim your Sponsored Listing.