Husaini sahal
Husaini sahal
24/03/2026
Duk inda akaje aka dawo dai, ke mace ce wadda rayuwarki take bukatar tsantseni da kulawa akoda yaushe.
Yana da kyau ki sani cewa Jikinki ba kayan gwaji bane, da zaki baiwa ko wanne fasiki damar gwajin soket da sunan soyayya ba.
A matsayin ki na 'ya mace Shin a ina kika bar darajarki da mutunciki ?
Shin menene abunda saurayi zaiyi miki na rayuwa wanda iyayenki bazasu iya yi miki shi ba, ? Da har zaki bashi damar keta miki ragar mutunci kawai Saboda yayi miki karyar cewa yana sonki kuma zai aure ki.Yau wasu ‘yan mata suna banzatar da kansu da sunan soyayya.
Wallahi Ina mamakin yadda wasu matan suke mika jikinsu ga samari, suna zaton hakan shine soyayya.
Ya kamata mata ku sani cewa sufa Wasu samarin ba soyayya suke nema a wajenku ba, Magana ce ta bukata kawai, idan saurayi ya ganki yaji yana sha'awarki zaiyi maza ya lallabo da sunan soyayya, ya samu ya lallaba ki ya zare zaren yaci gaba da tafiya.
Shiyasa idan naga mace mai son abun duniya sai naji ina tausayin ta, Saboda yadda samari suke mai da ita motar haya kowa ya ganta a hanya kawai tarewa zaiyi ha hau.
Saboda haka Ina mai baku shawara tun kafin lokaci ya kure muku mata masu baiwa samari dama suna taba jikinku da sunan soyayya daku nake Wallahi muyiwa kanku fada duk namijin da kika sake kika baiwa dama yasan yadda k**e, to Ina mai tabbatar miki bazai aure ki ba, Wannan ita gaskiyar magana.
Ita Soyayya ta gaskiya tana tare ne da girmamawa, hakuri, da niyyar aure ba amfani da yaudara ba wajen cimma MURADUN marasa kyau ba.
Yana da kyau Ki kare kanki, Ki kare daraja kanki sannan Ki guji duk wanda yake neman jikinki kafin ya nemi zuciyarki da mutuncinki, Domin kuwa ke ba abar wasa bace ke daraja ce da allah ya shimfida sharuda kafin mallakarki.
Rubutuna na gaba zanyi shine akan .....!!
Daga karshe ina rokon ubangiji allah ya shiryar damu bisa tafarkin dai dai ya yafe mana kuskuren mu amin ya rabbil alamin 🤲
awacreation ✍️
21/01/2026
Tinkiya Uwar Timɓele, Bakisan Gariba Kace a Gaba 🚶🚶🚶🚶🚶🚶
Tsoro Na Kada Su gama Cinye wasan nasu Tun kafin A Tafi Knockout, Ana Fitowa a Musu irin na Liverpool 🤡
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano
KANO