Arewa Connect Movement
Arewa Connect Movement kungiya ce mai zaman kanta wadda ke haɗa matasa da al’umma domin ilimi, haɗin kai, tarbiyya da ci gaban Arewa.
Muna aiki da gaskiya, sadaukarwa da haɗin kai domin gina Arewa mai ƙarfi da makoma mai kyau.
PHYSICAL VIDEO EDITING TRAINING
Ina masu sha’awar koyon Video Editing a Physical Training?
09/08/2026
AREWA CONNECT MOVEMENT EMPOWERING LIVES
📅 DATE: 08 AUGUST 2026
Alhamdulillah! Jiya mun sake gudanar da Training na Eco Craft, Ɗan Kunne da Detergent ƙarƙashin Arewa Connect Movement (ACM).
Burimmu ba wai koyar da sana'a kawai ba ne burinmu shi ne mu bai wa matasa da mata damar dogaro da kansu, su samar da abin da za su iya yi da hannunsu, su samu hanyar samun halal ɗin shiga, kuma su zama masu amfani ga al'umma.
“Lokacin da ka koya wa mutum sana'a, ba ka ba shi abin yau kaɗai ba; ka ba shi damar gina makomarsa.”
Muna son ganin kowanne matashi yana da abin da zai dogara da shi, kuma kowacce mace ta samu damar amfani da baiwar da Allah Ya ba ta wajen gina rayuwarta da iyalinta.
Arewa Connect Movement Empowering Youths, Transforming Communities.
Daga koyarwa zuwa dogaro da kai. Daga dogaro da kai zuwa ci gaban al'umma.
26/07/2026
ALHAMDULILLAH! AN KAMMALA TRAINING CIKIN NASARA.
A yau, 25 July 2026, cikin ikon Allah mun samu nasarar kammala Training kan Detergent, Ɗan Kunne (Earrings), Sarƙa (Necklace) da Paper Bag ga ɗaliban makarantar Secondary da ke Nasarawa, ƙarƙashin Arewa Connect Movement.
Wannan horo wani muhimmin mataki ne na ƙarfafa matasa da ɗalibai da ilimin sana'o'i domin su dogara da kansu, su samar wa kansu hanyar samun kuɗaɗen shiga, tare da rage zaman banza da rashin aikin yi.
Muna godiya ga malamai, shugabannin makaranta, masu horaswa, da duk mahalarta wannan shiri bisa jajircewa da goyon bayan da s**a bayar. Allah Ya sanya wannan ilimi ya zama alheri ga rayuwarsu, Ya ba su ikon amfani da shi wajen gina makoma mai kyau.
Arewa Connect Movement za ta ci gaba da kai irin waɗannan shirye-shiryen zuwa makarantu da al'ummomi domin gina matasa masu ilimi, ƙwarewa da dogaro da kai.
📅 Rana: 25 July 2026
📍 Wuri: Makarantar Secondary, Nasarawa
"Empowering Youth Through Skills, Innovation & Community Development."
12/07/2026
🌍 AREWA CONNECT MOVEMENT
Ba wai muna magana kawai ba, muna samar da sauyi.
A cikin 'yan kwanakin nan mun samu nasarar horas da matasa sama da 30 a kan:
✅ Eco Craft
✅ Ɗan Kunne (Earring Making)
✅ Paper Bag Production
Mun yi imani cewa idan ka ba matashi ilimi da ƙwarewa, ka ba shi damar gina makomarsa.
Wannan tafiya ta ci gaba. Burinmu shi ne mu kai ilimi, ƙwarewa da damar dogaro da kai ga dubban matasa a faɗin Arewa.
📍 Ku kasance tare da Arewa Connect Movement domin samun damar shiga shirye-shiryenmu na gaba.
Together, We Build a Better Arewa.
Photography Training is Here!
Ka shirya koyon fasahar daukar hoto daga tushe har zuwa matakin ƙwarewa.
📢 Duk wanda yake da sha’awar shiga Training na Vedio editing (FREE), yayi magana domin a saka sunansa.
20/06/2026
Alhamdulillah
A yau 20 June 2026, cikin ikon Allah mun samu nasarar kammala Training na koyar da Eco Craft da Ɗan kunne ga mata 100 domin ƙarfafa su su dogara da kansu, su samu hanyar samun kuɗaɗen shiga da gina rayuwa mai ɗorewa.
Wannan shiri ya gudana ne a ƙarƙashin Arewa Connect Movement tare da haɗin gwiwar A.S Dan Zaki Center.
Ba koyo kawai aka yi ba an buɗe ƙofa ce ta fata, ci gaba da dogaro da kai. Allah ya sanya wannan ilimi ya zama alheri mai ɗorewa ga kowa da kowa. Arewa Connect Abubakar Shuaibu (𝐀.𝐒. 𝐃𝐀𝐍 𝐙𝐀𝐊𝐈)✍️
Date: 20 June 2026
15/06/2026
Alhamdulillah 🤍
Babu abin da za mu ce da Allah sai godiya. Mun kammala training na koyar da Eco Craft da Ɗan Kunne cikin nasara, inda sama da mutum 50 s**a amfana da wannan horo karkashin Arewa Connect Movement (ACM).
Wannan wani babban mataki ne a ƙoƙarinmu na ganin matasan Arewa sun samu sana’a kuma su dogara da kansu, domin gina rayuwa mai inganci da ci gaban al’umma.
Muna godiya ga duk wanda ya bada gudummawa da kuma waɗanda s**a halarta.
Allah Ya sanya albarka, Ya ba da nasara a gaba.
📅 Date: June 14, 2026
📢 Duk wanda yake da sha’awar shiga Training na Social Media Management (FREE), yayi magana domin a saka sunansa.
Allah ya Kara daukaka Arewa connect movement
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kano