IBM Health Talk
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from IBM Health Talk, Tudun Maliki, Zoo Road, Kano.
𩺠Health Education for Everyone
Nutrition ⢠Disease Prevention ⢠Healthy Living
đ Sharing reliable, research-based health information
đ Because your health is your greatest investment.
25/05/2026
Wannan hadin shine dai-dai shawara kyautađ
16/05/2026
Dadi a baki⌠amma jiki na iya shan wahala idan ya yi yawa.
âđžRD. Ibrahim A. Bichi, RDN
15/05/2026
Yawaita cin taliyar yan yara (instant noodles) tare da soyayyen nama na iya Ćara haÉarin kamuwa da hawan jini (high blood pressure), musamman idan ana yinta akai-akai.
âď¸ RD. Ibrahim A. Bichi, RDN
TAMBAYA ga kowa mai ake Nufi da TA MUTU TA DAWO sunan Abinci ne !
âIdan kina jin gajiya ko yunwa da wuri, ayaba na iya taimaka miki sosai.â
âBa duk abin da ake ci a t**i yake da lafiya ba â ganda da aka Ćona da taya na iya zama kamar kana cin guba a hankali ba tare da ka sani ba.â
âShin wannan abinci ya cika adequate diet? đ¤
Breakfast: Koko da burodi
Lunch: Shinkafa da miya
đ YES ko NO? Ka bada dalili a comment!â
ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU
Sunana RD.Ibrahim A. Bichi, CEO na SmartDiet Wellness Clinic.
A SmartDiet Wellness Clinic, muna taimakawa mutane da ke fama da matsalolin lafiya da s**a shafi abinci da salon rayuwa, kamar:
â˘Kiba da tumbi
â˘Ciwon sugar (Diabetes)
â˘High BP da Low BP
⢠Ulcer
⢠Mata Masu ciki da shayarwa
⢠Tsofaffi Mata da maza
Matsalolin lafiya da s**a shafi tsarin abinci.
Muna ba da shawarwari na musamman kan tsarin abinci domin taimakawa mutane su samu ingantacciyar lafiya duka ta Online.
Ba sai ka wahala ba, muna jagorantar ka mataki-mataki domin ka inganta lafiyarka, Insha Allah.
Ina roĆon goyon bayan ku ta hanyar:
⢠Patronage
⢠Share
⢠Adduâa
⢠â Comments/Likes
⢠Referral ga wanda zai amfana
Allah Ya ba mu lafiya gaba Éaya. Amin.
CONSULTATION IS NOT FREE!
RD. Ibrahim A. Bichi , RDN
CEO, SmartDiet Wellness Clinic
Phone: 09162125753
Email address: [email protected]
08/04/2026
Assalamualaikum đ
04/04/2026
Amfanin Citta (Ginger) ga Lafiya â Abin Mamaki da Mutane Da Yawa Ba Su Sani Ba
Citta na daga cikin abubuwan da muka saba amfani da su a girki, amma gaskiya amfaninta ya fi haka nesa. Daya daga cikin abin da ta fi shahara da shi shi ne taimakawa wajen rage tashin zuciya da amai.
Masana sun gano cewa citta na iya taimakawa:
tashin zuciya na mata masu ciki (morning sickness)
tashin zuciya yayin tafiya (motion sickness)
amai bayan tiyata
amai da wasu magungunan HIV ke haddasawa
har ma da amai da ake samu yayin chemotherapy
Ba nan kaÉai ba, citta na da tasiri sosai wajen rage ciwo.
Misali, an gano cewa Ćaramin adadi kamar kashi Éaya cikin takwas na cokali (1/8 teaspoon) na garin citta na iya aiki kusan daidai da maganin ciwon kai na migraine (Imitrex), amma ba tare da illolin da magani ke da su ba.
Haka kuma, ga mata masu fama da ciwon alâada (menstrual cramps), citta na iya zama babban taimako. Bincike guda huÉu (randomized trials) sun nuna cewa:
idan aka sha citta a kwanakin farko na alâada, tana rage ciwo sosai
adadin da ake bukata yana tsakanin 1/3 zuwa cokali 1 a rana
Wani abin Ćara ban shaâawa shi ne, citta na iya taimakawa wajen rage yawan jinin alâada.
Idan mace ta rika shan:
1/8 teaspoon na garin citta sau uku a rana,
tun daga ranar da ta gabaci fara alâada,
ana iya rage yawan jinin da kusan rabin yadda yake fitowa.
Kuma abin mamaki, wannan tasiri yana Ćara inganta ne duk lokacin da aka ci gaba da amfani da ita wata bayan wata.
A Ćarshe:
Citta magani ne mai sauĆi, arha, kuma mai sauĆin samu. Idan aka yi amfani da ita yadda ya dace, tana iya taimakawa sosai wajen rage tashin zuciya, ciwo, da kuma wasu matsalolin da mata ke fuskantaâba tare da manyan illa ba.
âď¸RD. Ibrahim Abdulsalam Bichi
Click here to claim your Sponsored Listing.
Website
Address
Kano
700224