Siyasa bada Gaba ba

Siyasa bada Gaba ba

Share

Siyasar Jamhuriya ta farko

18/04/2026

Kindly accept this as a formal invitation to my wedding ceremony. Your presence will be a great honor, and we sincerely look forward to celebrating this special occasion with you.

10/04/2026
06/04/2026

Ƙarin Tunatarwa kan Tsarin Shirin CDP ga Al'ummar Shinkafi 'B' - Kambarawa, Kwaɗo, Modoji, Maƙera, Bakuru da Kadafawa

JADDAWALIN WAKILAN KWAMITIN GUNDUMA (CLC) DA KUMA TSARIN GUDANARWARSU

A ƙoƙarin da muke tayi na juyo da hankulan al'ummar mu kan wannan shiri na raya Gundumomi (Ward Development) da Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON ya kawo domin kyautata rayuwar al'umma, yau, za mu fitar wa al'umma jerin wakilan da ya k**ata kowane kwamiti ya ƙunsa da kuma hanyar tafiyar da aikin shi.

A kowace gunduma/mazaɓa (ward), akwai ma'aikata guda uku (3) na ƙaramar hukuma da aka ɗauka aiki wanda kuma suke cikin tsarin ma'aikatan gwamnati tsawon lokaci, sai dai kusan ayyukan da suke yau da goben tsarin aiki ya haɗiye su. Amma ɓullo da wannan shiri na CDP ya busa masu sabon rai a cikin aikin nasu.

Waɗannan ma'aikata su ne;
1. Community Development Officer (CDO)
2. Community Learning Officer (CLO) sai kuma;
3. Community Support Officer (CSO).

Domin kiyaye ƙa'ida da sharuɗɗan aiki, sai aka damƙa alhakin jagorancin wannan kwamiti a hannun su, musamman shi/ita CDO a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran wakilan kwamiti su ne k**ar haka;

1. Kansila
2. Maigari
3. Dattawa guda uku
4. Liman Ɗariƙa
5. Liman Izala
6. Wakilin masu buƙata ta musamman
7. Wakiliyar Mata
8. Wakilin Matasa
9. Hedimasta
10. Wakilin 'yan kasuwa
11. Malamin Gona
12. Malamin Asibiti

Idan muka haɗa lissafin gaba ɗaya za mu sami mutum goma sha bakwai (17) a matsayin 'yan wannan kwamiti na gunduma, Community Level Committee (CLC).

Waɗannan bayin Allah su aka ɗora ma alhakin tafiyar da wannan kwamiti, domin gudanar da duk ayyukan da s**a shafi gundumar a ƙarƙashin wannan shiri na CDP.

Duk abinda za a nema ko za a gudanar, to wajibi ne duka sai wannan 'yan kwamiti sun zauna sun cimma matsaya kafin gabatarwa ko gudanarwa. Idan faɗin lamarin ya wuce iyawar su, to sai su tara al'umma a ofishin su na gunduma domin a tattauna a sami matsaya.

Babu wani mutum ɗaya da aka ba damar yin gaban kanshi kan duk wani abu da da ya shafi wannan gunduma ba tare da sauran wakilan kwamitin ba.

Maganar gudanar da ayyuka a cikin shirin Naira Miliyan Goma Goma (N10, 000, 000) da aka aje ma kowace gunduma a asusun ajiyar ta na banki, shirin raba kayan noma na zamani, rabon takin zamani, rabon kayan cimaka da ma duk wani abin da ya shafi gunduma, to a wannan tsarin ake tafiyar dashi, inda kuma al'umma s**a fahimci ba kan haka suke ba, to suyi maza su sanar da babban ofishin gudanarwa na CDP wanda ke ƙarƙashin jagorancin Kamaluddeen Kabir Katsina domin yin gyaran da ya k**ata.

CDP (Katsina State Community Development Programme) ɗin nan ta al'umma ce kuma don al'umma aka yi ta. Wajibi ne al'umma su maido hankulan su kan ta domin cin gajiyar alheran da tazo dasu.

Ya Allah Ka iya mana, kai mana maganin abinda ya ishe mu.

Shinkafi 'B' Consultative Forum (SCF)
Litinin, 6 ga Afrilu, 2026
18 ga Shawwal, 1447

Katsina State Community Development Programme
Wakeup Katsina-Youth

Photos from Shinkafi 'B' Consultative Forum - SCF's post 06/04/2026
05/04/2026

With Prof. Adam Muhammad Abubakar – I just got recognized as one of their top fans! 🎉

05/04/2026

Everyone has a gift from God. The Northerners are endowed by God with leadership qualities. The Yoruba man knows how to earn a living and has diplomatic qualities. The igbo man is gifted in trade, commerce, and technological innovation. God so created us equally with purpose and different gifts.

Siyasa bada Gaba ba

01/04/2026

Matashi 02

Ya kai Matashi dan uwana yana daga cikin abin da ya k**ata ka fahimta wanda ya ke a zahiri ga duk mai hankali, shine irin yadda yan Siyasar s**a riƙa yi maka Wasa da hankali, da kuma wasa da rayuwar ka!

Ka taba tambayar kan ka, wane irin tanadi yan siyasar Nigeria s**a maka don goben ka? Shin kana nazari da tunanin yadda aka sha yi maka alkawura iri iri a kan goben ka, kuma har yanzu ga goben taka tana zuwa, shin kaga wadannan alkawuran a aikace? Irin su zamu samar maka da wutar lantarki, ilimi kyauta, kiwon lafiya, Tsaro, ingantacciyar dama ta kasuwanci, shin a matsayin ka na dan Nigeria mai tarin arziki a kasa, kana samun wadancan abubuwan kyauta? Shin minene ake baka kyauta bayan Maganin Sauro, da katin zabe, da takardar zabe?

To idan ka tsaya ka natsu zaka ga dan Siyasa kasar nan yan kasuwa ne, wanda ya fi Jari shi zai mallaki haja mafi girma, shi yasa kuma zai fi yawan Costumers. Kuma su din iyali ne guda, makarantun yayan su iri daya, wurin neman lafiyarsu data ya'yan su, ba irin naka bane, wurin aikin su da na yayansu ya sha baban da naka, wadannan ma'aikatun: CBN, NNPCL, NPA... Da sauran wurare masu matski ba'a baka, baka sani an dauka sai yayansu in kaga talaka to Allah ne ya kwato mashi! Amma wurare irin su Teaching; Primary, Secondary... A nan ne kage ganin talaka yana bada gudunmawar shi, Dalili kuwa saboda kudin da ake biya su sun san adadin!

Da ka ga sun neme ka to lokacin siyasa ne, a gayyato ka kauye kauye, don su tara mutane su samu kuri'a don su ci gaba da mulki. A lokacin ne za'a baka tallafi, a lokacin ne ma'aikatu ma ke amfani da dama su matsa ma yan siyasa don biya musu hakkokansu!

Wadannan kadai ya ishe ka ka zauna lafiya da yan'uwanka matasa, gaba, fada, zagi, cin mutuncin dan uwanka matashi akan yan siyasa, ba naka bane! Abin takaici hakan har ya kai, wasu su raunata yan uwansu matasa, har akan rasa rai ma kan yan siyasa da siyasa.

Ya kai matashi ka sani, don kana da sabani da wani ta SIYASA ba shine ka samu kofar cin mutuncin shi ba, tallata dan takarar ka, shima ya tallata na shi, wanda ya fi karfin dalilai sai ya yi convincing mutane har nashi ya kai ga in da ya ke so! Ka yi kokari ka yi Siyasa bada Gaba ba !

Laraba 01/04/2026

29/03/2026

Matashi (01)
Ina tunanin ka ya ke, ina hankalin ka yake! Tsabtace siyasar ka da tunani mai kyau da basira da girmama abokin adawa, yi siyasa irin ta yan mazan jiya Siyasa bada Gaba ba.

A yau kai matashi ka wayi gari ba a bakin komai ba, baka da wutar NEPA, baka da ilimi ingantacce babu kiwon lfy, da kyar kake samun abin sanyawa aljihu, kaima bakin salati. Ka taba tunanin mine ne Makomar ka a gobe!

Shin gwagwarmayar ka ta a dauki yan canji ne a baka yau, gobe ma a baka in aka gama amfana da karfin ka a dauko kannen ka masu tasowa? Ko gwargwarmayar ka ta gina goben ka ce da ta yan'uwan ka matasa.

Kaima zaka iya zama k**ar wancan dan majlisar wakilan, ko k**ar wancan Senator, ko k**ar wancan Gwamnan, ko shugaban kasa!

Amma sai ka zama matashi da za'a yi alfahari da shi, matashi mai sanin ya k**ata, matashi mai basira, matashi mai amfani da damar da Allah ya bashi da lokacin shi wajen banbance daidai da ba daidai ba, wajen banbance shugabanni na gari wadanda za su taimaka ma goben ka, ba wadanda za su rusa ta ba!

Idan zaka yi siyasa, ka yi ta da manufa, kuma mai tsabta, mai tsari, da sanin ina aka dosa. Yi ta don ka zama fitila ga al'ummar ka ta hanyar kawo masu ci gaba don kannen ka su yi alfahari da yayyan su sun yi amfani da lokacin samartakar su. Idan zaka yi gwagwarmayar siyasa yi ta ba da gaba ba!

Zan ci gaba

Asabar 29th March, 2026.

Photos from Siyasa bada Gaba ba's post 29/03/2026

Siyasa hanya ce da mutane ke bi wajen rayuwa a hade, ko a tare, ko a kungiyance cikin manufa daya. Siyasa na nufin hada yarjejeniya tsakanin mutane domin su zauna tare duk da mabam-bantan ra'ayoyi, kabilu da addinai, a birane da kasashe. https://ha.wikipedia.org/wiki/Siyasa

Sai dai da dama daga Matasan da shugabannin mu A kasata Nigeria sun dauki siyasa wani bangare daban.

Matasa: sun dauki siyasa gaba da kiyayya da kullata ga abokan zaman su; ta yadda har takan kai ga dan'uwa gaba da dan'uwan shi a dalilin banbancin ra'ayi na yan siyasa ko banbancin Jam'iyyun siyasa! Wani lokaci har rasa rayuka ake. Ta wata fuskar kuma matashi yana daukar siyasa wata hanya ta tara makudan kudade ba taimakon al'umma ba.

Yan Siyasa: suna daukar siyasa hanya ta dawwama bisa madafun iko ko ta halin kaka, hanya ta tara makudan kudade don jin dadin su da makusantan su, hakan ke jaza suna haddasa gaba da kiyayya tsakanin wannan bangaren da wancan, wadannan kabilu da wadancan, matashin da ya k**ata a gina da ilimi da tunani mai kyau amma an maida shi mayunwaci ta yadda ba yadda za'ai kwalwar shi ta halba ya kawo ci gaba da zai amfani kasa... Hakan sai ya bayi da fadawar su a bangar siyasa ko wani mummunan abu da zai zama matsala ga yan kasa!

Ayi Siyasa bada Gaba ba !

Asabar 29th March, 2026.

29/03/2026

Da Jagora da Gwamna duk abu daya ne! Tare su ke! Siyasa ce kawai ake bugawa, an bar talaka da hayaniya!

Bari kuji yadda abun ya ke!
Jagora ya kawo Ganduje tun tenure farko s**a yi ta fada aka zo Ganduje zai yi ta biyu aka kawo Gwamna mai ci a yanzu amma Ganduje ya lashe zaben, aka taho Ganduje ya gama shekara 8.

Aka yi siyasa mai zafi Jagora ya tsaya ma Gwamna mai ci yanzu cikin taimakon Allah ya ci zabe... !

Gwamna mai ci yanzu bai gama tenure ta farko ba, sun bata da Jagora, yanzu kuma Jagora zai dauko wani (idan hasashe na ya tafi daidai zai dauki Gawuna) a tallata shi a 2027 ayi siyasa sosai amma Gwamna mai ci yanzu Ya lashe zaben don Haka s**a tsara, wannan zata wuce, ana zuwa 2031 sai a kara daga Gawuna sai ya ci zabe a matsayin Gwamna.

Wannan hasashe na ne
Jama'a shi fa Jagora yana da wayau na siyasa, Sannan yana Creating Leaders... Yana amfani da dama ta anci amanar shi yana dasa mutane.

Matasa yan'uwa na ayi siyasa ba da gaba ba, a sanya hikima da basira , siyasar kasar nan kullum "Elites ne ke juyawa" talakawa kuma na zagin juna, ana k**a su ana tsarewa ko kashewa akan hanya! Ga tsadar rayuwa, hakan ya sa da dama tunanin ma bai kaiwa ga abubuwan da yan siyasar ke kullawa! Don duk an firgita talaka, sai fada da zagin juna!

Lokaci ya yi da matasa za su bude kwakwalwar su, su fadada tunanin su don yin siyasa mai tsabta da zabar shugabanni masu tunani mai kyau don goben su a matsayin su na ginshiki na ganuwar kowane yanki ko bangare!

Allah ya sa mu dace.

Siyasa bada Gaba ba

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address

Kambarawa
Katsina
820101