Abba abdullahi fans

Abba abdullahi fans

Share

abab

23/12/2025

DA ƊUMI ƊUMI: Wani Maciji ya haɗiye Naira Tiriliyan (210) a Ma'aikatar NNPC, Naira Tiriliyan Ɗari Biyu Da Goma (210) Tayi Batan Dabo A Ma'aikatar NNPC Ta Najeriya.

An shiga ruɗani bayan gano wani gibin bayanai na kuɗaɗe da ya kai Naira tiriliyan 210 a cikin rahoton kuɗin Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC Limited), lamarin da ya jawo hankalin Majalisar Dattawan Najeriya.

Ɓatan kuɗaɗen ya bayyana ne a cikin rahoton binciken kuɗi na kamfanin na wasu shekaru, inda aka kasa samun cikakken bayani kan wasu alƙaluma da aka rubuta a matsayin bashin da ake bin wasu da kuma kuɗaɗen da kamfanin ke bin wasu.

Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a ya bayyana rashin gamsuwa da bayanan da NNPC ta gabatar, inda ya bukaci kamfanin da ya fito fili ya yi cikakken bayani kan asalin kuɗaɗen da kuma inda s**a dosa.

Majalisar ta jaddada cewa ba za ta lamunci duk wani sakaci ko rashin gaskiya wajen tafiyar da dukiyar ƙasa ba, tare da gargaɗin cewa za a iya ɗaukar ƙarin matakan bincike idan har ba a gamsu da bayanan da aka bayar ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, NNPC Limited ba ta fitar da cikakken bayani da zai warware gibin kuɗaɗen ba, yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da bibiyar yadda lamarin zai kaya.
Abba Abdullahi Atm
Abba Abdullahi Atm
Katsina State Environmental Protection Agency
Naraguta Hausawa, Plateau, Nigeria

Photos from Abba abdullahi fans's post 22/12/2025

Wani matashi yana a cikin motarsa ya hango wani tsoho mai babur a cikin cunkoson ababen hawa, yana tuka tsohon babur wanda yayi matuƙar lalacewa yana haya dashi. saboda mummunan yanayin babur ɗin, ba ya samun kwastomomi Masu Yawa sosai.

Matashin sai ya bi tsohon a ɓoye har zuwa wurin aikinsa, daga nan ya koma ya dawo da sabon keke mai ƙafafu uku (tricycle) domin ba shi mamaki. Tsohon ya kasa ɓoye farin cikinsa lokacin da aka ba shi tricycle ɗin, sannan matashin ya ƙara masa da wani ɗaki mai kyau da aka tanada a matsayinshi na dan cirani.

Wane Fata Zakuyi Masa ?

22/12/2025

Funtua state. Duk wanda bai yarda ba ya tafi kotu. An hana Ni comment ne shiysa na shigo ta nan kofar

Photos from Abba abdullahi fans's post 22/12/2025

Daya Daga Cikin Masu Koyar Da Tarbiyya Kenan A Msana'antar Finafinan Hausa, Wato Jaruma Fatima Kwana 90

Photos from Abba abdullahi fans's post 21/12/2025

Hakikanin Gaskiya Da Tambihi Akan Motar Gwamna Radda

Daga: Abdullahi Mohammed

Kwanan nan na ci karo da wani rahoto na ƙarya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin cewa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sayi wata motar BMW mai tsadar kuɗi da kuɗaɗen jihar. Wannan zargi ƙarya ne tsantsa, kuma yana buƙatar a fayyace shi nan take, musamman ganin cewa yana shafar mutum wanda a kodayaushe yake fifita buƙatu da muradun jama’a fiye da komai.

Tun bayan hawansa kan karagar mulki, Gwamna Radda yana amfani da motocin da ya gada daga wanda ya gabace shi. Wannan shawara ta nuna ƙwarai da gaske jajircewarsa wajen kula da dukiyar jihar yadda ya k**ata, wata ƙa’ida da ke jagorantar dukkan ayyukan gwamnatinsa.

Ba k**ar wasu gwamnonin da ke canza motocin alfarma sau biyu ko uku a lokacin mulkinsu ba, Gwamna Radda ya ci gaba da amfani da motocin guda ɗaya kusan tsawon shekaru uku. Wannan ba daidaituwa ba ce; shugabanci ne na sanin mak**ar aiki, wanda ke fifita ayyukan ci gaba a kan jin daɗin kai.

Ina iya tunawa, a lokacin da Dikko Radda yake Darakta Janar na Hukumar Raya Ƙananan da Matsakaitan Kasuwanci ta Ƙasa (SMEDAN), ya ci gaba da amfani da motocin aiki na wanda ya gabace shi. Kuma abin mamaki, ya gudanar da aikinsa yadda ya k**ata matuƙa. A yau, ana kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun abubuwan da s**a taɓa faruwa ga hukumar.

Waɗanda ke bibiyar ayyukan gwamnan da kyau za su tuna wani lamari a wata ziyarar aiki da ya kai Jihar Kogi shekaru biyu da s**a gabata, inda tayoyin motar aikinsa s**a samu matsala.

Maimakon jinkirta tafiya ko neman a sauya mota nan take, Gwamna Radda kawai ya sauka daga motar ya shiga wata a cikin jerin ayarin motocin domin ci gaba da tafiya.

Wannan lamari, ko da yake ƙanana ne, yana nuna halayyarsa sosai. Gwamna mai son jin daɗin kai da alfarma da zai yi hayaniya da buƙatu na musamman. Amma Gwamna Radda ya dace da halin da ake ciki ya ci gaba da tafiya, ya mai da hankali kan aiki, ba kan jin daɗi ba.
A lokut

21/12/2025

DA DUMI-DUMI: ƙasurgumin ɗanbindiga Isuhu Buzu ya kwanta hagu a Zamfara

Ƙungiyar haɗakar askarawa da sibiliyan JTF ta jihar Zamfara sun sami nasarar halaka wani kasurgumin dan bindiga, mai suna Kacalla Isuhu Buzu a garin Kaya na yankin karamar hukumar Maradun.

Biyo bayan wani farmaki da sojoji s**a kai wa 'yan bindiga a garin na Kuncin Kalgo.

Wani mazaunin garin Kuncin Kalgo na yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, ya ce yanzu haka suna zaune cikin gagarumin tashin hankali da barazana ta rayuwa:

Photos from Abba abdullahi fans's post 21/12/2025

Bashida abinda zamuyi mashi hassada kafin ya hau mota mai gidan mu ya hau

Mudai abinda muke Neman sani shine meyasa bai siya ba kafin yazama gwamna? Muna da masaniyar motocin da yayi Yakin Neman zabe dasu na Opay ne ? Sai Gashi yanzu mun hango shi da motar miliyan 600 !!! Kuma mun sani bashi da shago a kantin Kwari ko a Fatima baika central market,kunga kuwa dole muyi tambaya,ina aka samo kudin wannan motar ? Daga tambaya shikenn sai ace muna hassada 😒
Katsina State Environmental Protection Agency
Abba Abdullahi Atm
Bakori

21/12/2025

DA DUMI -DUMI: Chunkoso ya k**a matafiya masu Zuwa hutu a kan titin Lokoja-Abuja

Masu ababen hawa da ke bin babbar hanyar Lokoja-Abuja sun makale saboda cunkoson ababen hawa - kwanaki kadan kafin Kirsimeti.

Cinkoson ababen hawa da ke kan hanyar ya ci gaba da kasancewa na tsawon kwanaki uku.

Direbobin da Hukumar Talabijin ta Najeriya (NTA) ta yi hira da su sun ce suna kan hanya tun farkon Asabar ba tare da an ga karshensu ba.

"Yanzu karfe 8 na dare ne, kuma ina nan tun karfe 7 na safe tare da iyalina, ina kan hanyar zuwa Enugu," in ji wani direba.

Cinkoson ababen hawa ya fi tsanani a kusa da Koton Karfe.

Rahotannin sun nuna cewa cunkoson ababen hawa ya faru sak**akon faduwar manyan motoci biyu a kan hanya.
abdullahi fansAbba Abdullahi Atm

Photos from Abba abdullahi fans's post 21/12/2025

Another update 😍

zamfara state international Airport gusau

Muna godiya Governor Dauda Lawal

ALLAH yakara Yimaka jagora 🙏

Photos from Abba abdullahi fans's post 21/12/2025

BABBAN LABARI

Ƙaramar hukumar Funtua ta buɗe babban ɗakin shan magani da shugabancin karamar hukuma ya gina a cikin sama da shekaru goma.

A jiya asabar 20 ga watan Disamba Shugaban karamar hukumar Funtua Alh Abdulmutallib Goya ya jagoranci buɗe asibitin tare Babbar baƙuwa uwar gidan gwamnan jihar Katsina.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Katsina?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address

Katsina