Go Again Dujiman Katsina Movement
An bude wannan Shafi ne domin Kawo irin cigaban da Dujiman katsina Abdullahi Aliyu Ahmed yake kawowa
DAGA GHANA TERTIARY EDUCATION COMMISSION (GTEC), ACCRA, GHANA 🇬🇭🇳🇬
Tawagar Haɗin Gwiwar Kwamitocin Majalisar Wakilai ta Najeriya ta ci gaba da bincike kan batun “Certificate Racketeering”
A ci gaba da ƙoƙarin Majalisar Wakilai ta Najeriya na tabbatar da gaskiya da sahihancin takardun shaidar karatu, tawagar haɗin gwiwar wasu kwamitocin Majalisar ta isa Ghana Tertiary Education Commission (GTEC), Accra, domin ci gaba da gudanar da bincike da tattara muhimman bayanai dangane da batun “Certificate Racketeering.”
Tawagar ta ƙunshi wakilan Kwamitin Harkokin Cikin Gida, Kwamitin Ilimin Jami’a, Kwamitin Kwalejojin Fasaha na Tarayya, Kwamitin Harkokin Ƙasashen Waje da Kwamitin Ci gaban Matasa.
Wannan bincike ya biyo bayan ayyukan da tawagar ta gudanar a Cotonou, Jamhuriyar Benin, da kuma Lomé, Jamhuriyar Togo, inda aka tattara muhimman bayanai da s**a shafi binciken.
A Ghana, tawagar ta ci gaba da bincike a Ghana Tertiary Education Commission (GTEC), inda ake ci gaba da tattara bayanai da gudanar da bincike kan sahihancin takardun shaidar karatu da kuma sauran batutuwan da s**a shafi Certificate Racketeering.
Bayan kammala wannan gagarumin aiki na bincike da tattara bayanai, kwamitocin za su haɗa rahotonsu tare da gabatar da shi ga Majalisar Wakilai ta Tarayyar Najeriya, domin a yi nazari da tattaunawa a kansa bisa tsarin majalisa.
Muna yaba wa Hon. Abdullahi Aliyu Ahmad (Dujiman Katsina) bisa jajircewa, sadaukar da lokaci da ƙoƙari, da kuma gudunmawar da yake bayarwa wajen ganin wannan muhimmin aiki na Majalisar Wakilai ya gudana cikin tsari, gaskiya da adalci.
22/09/2026
AMADADIN KUNGIYAR GO AGAIN DUJIMAN KATSINA MOVEMENT.
Tana taya Wasu daga Cikin Members nata da zasu rabauta da Sabbin Mashina daga mai gidan su DUJIMAN KATSINA
1 Nura Sani Milo Gwarjo
2 Garkuwan Dujima
3 Abdurraham Aliyu
4 Yusuf Zaiyana M2
5 Umar Dallami Moriah
6 Majan Kira
Allah ya ci da yan baya
19/09/2026
Zaben Gwaje Ina Masoyan Dujima
👇
https://neis.ng/elections
MAGANAR DUJIMAN KATSINA TAZAMA GASKIYA.
Idan ba mu manta ba, a kwanakin baya Mai Girma Dujiman Katsina ya yi hira da manema labarai a wani dandali mai suna “SIYASAR MU A YAU”, inda ya yi bayani kan yadda wasu mutane daga cikin al’ummarmu ke taimakawa ‘yan bindiga, duk da ƙoƙarin da gwamnati da shugabannin yankin ke yi wajen ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Sai dai abin takaici, a wasu lokuta al’umma kan ɗora dukkan alhakin rashin tsaro kan shugabanni, ba tare da duba irin gudunmawar da wasu mutane ke bayarwa ga matsalar ba.
Yanzu ga shi, abin da Mai Girma Dujiman Katsina ya bayyana a wancan lokacin ya sake bayyana a cikin wani bidiyo da ya fito jiya Talata, wanda ke ƙara jaddada muhimmancin wannan batu.
Saboda haka, muna kira ga al’ummar Musawa da Matazu da su ƙara sanya ido, su kasance masu taka-tsantsan, tare da ba jami’an tsaro da shugabanninmu cikakken haɗin kai wajen yaƙi da rashin tsaro.
Tsaro ba aikin gwamnati kaɗai ba ne. Nauyinmu ne baki ɗaya.
Mu daina kare duk wanda ke taimakawa masu aikata laifi, mu tallafa wa ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya a Musawa da Matazu.
Dujiman Gaske
13/09/2026
Alhamdullah Go Again Dujiman Katsina Movement
10/09/2026
Ubangidan Oga
Happy birthday His Excellence Dr. Dikko Umaru Radda Ph.d
05/09/2026
Happy Maulud Al'umar Musawa/Matazu
Go Again Dujiman Katsina
30/08/2026
Amadadin Go Again Dujiman Katsina Movement muna taya Hon. Balarabe Yusuf Ajah Matazu Murna
Allah yasa Alkairi
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Katsina
Alerts
Be the first to know and let us send you an email when Go Again Dujiman Katsina Movement posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.