Sayyida Ma'asuma
JAKADIYAR IMAMU HUSSAINI (A.S)
ZAMUYI AIKI TUQURU DIMIN KARE MARTABAN IYALAN GIDAN MANZON ALLAH (S A W W)
ALLAH KADAFA MANA
12/09/2026
A taron, sun jaddada haɗin kai tsakanin sojojin ƙasa da IRGC, suna bayyana wannan haɗin kai a matsayin abu mai muhimmanci da zai ƙara ƙarfafa musu gwiwa wajen tunkarar abin da s**a kira “makircin maƙiya.”
A wannan taro, Ahmad Vahidi, kwamandan IRGC, ya ce: “Ƙarfin sojin rundunar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya zarce tunanin maƙiya. A wannan yaƙi, sun gani da idonsu cewa hasashensu na ƙarya game da ƙarfin sojojinmu ba daidai ba ne, kuma ainihin ƙarfin sojin Iran na ƙara bayyana a filin daga.”
Shi ma Babban Kwamandan Sojojin Iran, Amir Hatami, ya ce a wannan yaƙi:
“Duk wani ko da ƙaramin hari da aka kai wa Iran, sojojin ƙasa da na IRGC sun mayar da martani cikin haɗin kai, cikin sauri, cikin hikima, kuma da ƙarfi.”
Babban kwamandan sojojin ya kuma bayyana cewa Iran ba za ta yi sulhu ko sassauci kan muradunta da buƙatun ƙasa ba.
12/09/2026
HOUTHI TA FAYYACE MATSAYINTA KAN JIRAGEN RUWA A RED SEA
Mai magana da yawun dakarun Houthi, Yahya Saree, ya bayyana cewa zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Tekun Red Sea na ci gaba da kasancewa cikin aminci, sai dai jiragen ruwa da ke da alaka da Saudiyya.
Saree ya kuma yi gargadin cewa hare-haren soji kan dakarun Saudiyya za su ci gaba da kara tsananta, har sai an kawo karshen abin da ya bayyana a matsayin katangar da aka kakabawa Yemen.
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin ci gaban dakarun Houthi a yankunan da ke kusa da mashigin Bab el-Mandeb, daya daga cikin muhimman hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.
Har zuwa yanzu, wasu daga cikin wadannan ikirare-ikiraren na bukatar karin tabbaci daga majiyoyi masu zaman kansu.
11/09/2026
A BANZA.......
Yanzu haka sama da mutun 150 ƙwararrun masu bada dabarun yaƙi na Sojan Amurka suna Saudi Arebiya don tattauna yadda za'a daƙile nasarorin da mayaƙan Houthi ke samu akan Saudi Arebiya da masu mara mata baya ɓangaran hambararren Shugaban ƙasar. A kwanaki biyun nan Mayakan Houthi sun samu gagarumar Nasarar da tarihi zai daɗe yana bayyanata, Alhamdulillahi.
11/09/2026
LUKUTAR ASARA GA SAUDI AREBIYA.......
Wannan shi ne abin da ya faru a mashigar iyakar Al-Wadi’ah kwanaki 5 da s**a wuce, lokacin da Saudiyya ta yi ƙoƙarin tura ƙarin sojoji da kayan yaƙi domin ƙarfafa dakarunta masu biyayya gare ta. A rahotannin da muka samu, an ce an kai hari kan motocin da ke ɗauke da kayan soja da alburusai a sansanin Al-Wadi’ah. Alhamdulillahi mayaƙan Houthi na cigaba da samun gagarumar Nasara.
10/09/2026
DAGA YEMEN, KYAKKYAWAN LABARI.
A cikin sa’o’i 24 da s**a gabata, Mayaƙan Houthi sun kwato tare da karɓe iko da wani yanki da ya wuce kilomita murabba’i 2,600, wanda a baya yake ƙarƙashin ikon tsagerun ƙasar masu samun goyon bayan Saudiyya.
Mafi girman nasarorin da aka samu, a cewar rahoton, sun haɗa da kwace Hays, da kuma yankin bakin teku guda biyu, Al-Khawkhah da Al-Mokha.
Rahoton ya ƙara da cewa wannan nasarar ta bai wa Houthi damar samun kusan cikakken iko a kan mashigar Bab el-Mandeb, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen zirga-zirgar jiragen ruwa tsakanin Bahar Maliya da Tekun Aden.
10/09/2026
NASARAR IRAN A DAREN JIYA WAYEWAR YAU.
A lokacin hare-haren mak**ai masu linzami da Iran ta kai a daren jiya kan sansanin sojin sama na Muwaffaq Salti da ke Jordan, wani jirgin yaƙin Amurka kirar A-10 'Warthog' ya samu mummunar barna, har ya rasa ɗaya daga cikin fukafukinsa.
Haka kuma, kimanin jiragen yaƙi 8 kirar F-15 an raunata su sak**akon hare haren. Ya Hayyu ya Qayyumu, taimaki Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
10/09/2026
🇺🇸🇬🇧🇸🇦 Amurka da Birtaniya na cigaba da kwashe sauran jiragen sama masu aikin shayar da jirage mai a cikin iska daga sansanoninsu daban-daban da ke Gabas ta Tsakiya, tare da mayar da su zuwa filin jirgin saman King Abdul Aziz da ke Riyadh
Kome hakan yake nufi?
09/09/2026
WATA KATUWAR NASARA......
Jami’an Rundunar Sojin Iran (IRGC) sun sanar da cewa sun kai hari kan jiragen yaƙin ruwa na Amurka guda biyu, wato USS Delbert D. Black (DDG-119) da USS John Paul Jones (DDG-53), waɗanda ke cikin Carrier Strike Group 11 (CSG-11), ta hanyar amfani da mak**ai masu linzami na ballistic da aka ƙera na musamman domin kai hari kan jiragen ruwa (ASBM).
Rahotannin sun tabbatar da cewa jiragen biyun sun samu mummunar illa. Ya Hayyu ya Qayyumu, taimaki Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
09/09/2026
Rundunar Sojin Ruwa ta Iran ta k**a wani jirgin ruwa na ƙarƙashin teku mara matuƙi na sojojin ruwan Amurka, shine jirgi mafi hatsari da Amurka ke ji da shi na ƙarƙashin Teku, an k**a shi ne a kusa da Mashigar Hormuz. Ga masu siyan Gwangwan, muna bada farashin Sari.
06/09/2026
Mun tsinci kan mu a wani irin yanayi da muke yiwa junan mu Taqiyyah. Ka nemi sanin abinda kake yi na Addini da Hujja, don kai zaka kare kanka a ranar lahira. Kuma mafificiyar Ibada, itace wacce BAWA ke aikata ta da sanin ma'anonin ta ba don ya gada ko ya ga Al'uma suna yi ba.
Imam Ali (As), wadda shine muke komawa gare shi don kaiwa ga Annabin Rahma (S), ya sha bayyanawa Almajiran sa da wadda suke tare da shi cewa, kuyi tambaya, haka Imam Sadiq (As) ya sha horar ƴan Shi'ar su da yawan tambaya, tambaya mai ma'ana ta neman sanin Allah da dacewar sa, tana ƙara ƙarfin Imami da tsayuwa ƙyam a turba. Kuma da irin haka zukata ke samun nutsuwa, k**ar dai yadda Annabi Musa ya tambaya yana son ya ga Allah, ba don shakka ko inkari ba, yayi tambayar ne don yana son ƙarfin Imanin sa ya ƙaru.
Ya kai mai karatu, ina mai ƙara tunatar da kai cewa ALLAH yayi ka ƴantacce, saboda haka yana buƙatar ka bauta masa cikin ƴanci, ba irin Bautar Bawa da Ubangidan sa ba, wato irin bautar da ake don tsoron uquba ko kwaɗayin duniya. Wannan gidan (duniya), gida ne na gwaji, daga mu har Annabawan Allah mun zo nan ne don a gwada mu, ba kawai Allah ya tashi Annabawa bane don su shiga Aljanna bayan shiryatar da mu, A'a, suma an gwada su ne k**ar yadda ake gwada mu, har ma zance gwajin su ya fi namu tsanani, gwargwadon girman ka a wurin Allah gwargwadon jarrabawar ka.
Duk abinda baka gane ba, kayi tambaya, duk aikin da ka Jahilta baka san hukuncin Allah a cikin sa ba, ƙin aikata shi shi shine Alheri. Kar ka yadda a razana ka akan lahirar ka, ya zama ka fahimci gaskiya amma kana shakka akai, kowa yana aiki ne don lahirar sa. Wasu kwaɗayi, wasu tsoro, ya sa fuskar su ta ainihi na bayyana ne a lokacin da s**a keɓe, amma ta zahirin ta saɓa da abinda muka ce a farko. Allah ka tabbatar da mu akan hanyar ka madaidaiciya.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Website
Address
Kontagora
SHI'AIMAMIYYA