Umar Musa Usman

Umar Musa Usman

Share

Animal scientist

03/11/2023
Photos from Umar Musa Usman's post 01/11/2022

Kungiyar IZALA tana da Masallatai da makaranti sama da dubu dari a Naijeriya

✍️Musa H. Musa

Shugaban Kungiyar Izala, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau,ya karbi rahoton aikin da ya saka mambobin kwamitin Jibwis Social Media na tattara adadin masallatai na juma'a, khamsu Salawat da makaranti mallakar kungiyar a jihohi 37 harda Abuja a Naijeria

Kungiyar ta karbi yawan adadin masallatan juma'a guda dubu 9,225. Khamsu salawat dubu 63,409. Makaranti 39,727.
Wanda adadin ya kai yawan dubu 112,361.
A halin yanzu kungiyar tana da bayanan duk wani limami,Na'ibi, ladani shugaban kwamitin masallaci, da shugaban makaranta, a duk fadin kasar.

Wannan lissafi ya shafi iya masallatai da makaranti mallakar kungiyar Izala ne a duk fadin kasar.

Sheikh Bala Lau, ya yabawa mambobin kwamitin a wannan namijin kokari da s**ayi wajen bada hadin kai har aikin ya kammala cikin nasara. "Muna yaba muku,kwarai da gaske, kuma zamu dora aikin da kuka kawo mana a kan manhajar 'google map' ta yadda duk inda mutum ya shiga a kasar nan zaka samu masallatai da makarantun izala cikin sauki akan wayar hannun ka" inji shi

Tun farko a bayanansa, shugaban kwamitin Jibwis Social Media, Alh. Ibrahim Baba Suleiman ya karanto irin yadda mambobin s**a sha fama wajen tattara bayanan, tare da jinjina na musamman gare su, duk da 'yan matsaloli da aka samu a yayin gudanar da aikin,amma duk da haka anyi nasara.

Allah ya sakawa kowa da alheri. Amin

JIBWIS NIGERIA 🇳🇬

01/11/2022

ABUL-HAJJAJ AL-MIZZIY: MALAMI MAI K**A DA COMPUTER
An haifi Al-Hafiz Yusuf Ɗan Abdurrahman Ɗan Yusuf Jamaluddin Al-Mizziy ne a shekarar hijira ta 654 a wani ƙauye kusa da birnin Aleppo. Allah cikin ikonsa, Al-Hafiz Al-Mizziy bai fara koyon ilimin hadisi ba sai da ya kai kimanin shekaru 21 da haihuwa.

Daga cikin malamansa akwai Ibnu Abil Khair da Ibnul Bukhariy da Al-Imamul Nawawiy da wasunsu waɗanda ya gamu da su a garuruwa mabanbanta. Ya karanci ɗaukacin manyan littafin hadisi da dubban ƙananan littafai waɗanda ya kwafe su da rubutun hannunsa wanda aka ce yana da kyau kwarai.

Abul-Hajjaj Al-Mizziy ya kasance ƙwararren masani a ilimin hadisi da sanin mazajensa da ilimin Nahwu da Sarfu. Ya kuma kasance mutum mai kawaici da tawali'u da haƙuri da ƙarancin surutu da iya zama da mutane. An ce daga cikin ɗabi'arsa ba ya haddasa ko gulmar mutane.

Wani abu da aka sani a tarihin Al-Hafiz Al-Mizziy shine talauci da ya yi masa katutu. Ba shakka wannan malami ya yi fama da talauci, ta yadda har ya kasance ba shi da abin hawan da zai hau in zai zo cikin birnin Damascus don karantar da hadisi daga ƙauyensu watau Mizza (k**ar tafiyar 10km) sai dai ya taka sayyada, in ya iso bakin gari sai ya nemi ruwa ya yi kwaskwarima kafin ya shiga garin, a lokacin kuma shine malami mafi shahara wajen sanin ilimin hadisi.
Haka nan kuma ya tursasu izuwa ga ya sayar da asalin kwafin littafin sa na (Tahzibul Kamal) saboda tsananin rashin abin hannu.

Littafan sa guda biyu sune suke bayyana irin nau'in basirar da Allah ya yi masa wacce aikin ta ya yi k**a da na na'ura mai ƙwaƙwalwa ta fuskar amfani da lissafi da ƙalailaicewa wajen bayar da bayani mai gamsarwa da kuma tsari na logic.

Na farko shine littafin (Tahzibul Kamal) sai kuma (Tuhfatul Ashraf). Baya ga haka, Al-Mizziy ya yaye ɗalibai manya irin su Zahabi da Ibnu Katheer da sa'anninsu.

Zahabi yana cewa: "Mutum huɗu cikin malaman da na gamu da su sune ƙololuwa a sanin hadisi a zamanin mu; Ibnu Daqiqil Eid da Dimyātiy da Ibnu Taimiyah da

27/10/2022

Assalamu Alaikum,

Sanarwa!

Insha Allah daga gobe Juma'a Mallam ( Dr Muhammad Alhaji Abubakar ) zai bude Sabon Karatu a masallacin Marigayi Sheikh Muhammad Abba Aji na Mairi.

Lokaci: Bayan Sallar Magariba a kowani Sati.

Littafi: sai anje za'aji kowani Littafi ne

Allah yasa Mudace. AMIN

Sanarwa daga Dr. Muhammad Alhaji Abubakar( HAFIZAHULLAH)

26/10/2022

DUNIYA BATA DA TABBAS

Ina tausayin wanda Allah ya ba shi dama ta muqami ko iko ko kudi ko karatu ko kyau kuma yayi amfani da wannan damar wajen wulakanta mutane ko kaskantar da su ko danniya da muna-muna.

Yawancin masu irin wannan wulakancin tun a duniya suke fara danasani, kuma kaito yana nan yana biye da su

عسى سائل ذي حاجة إن منعته
من السؤل يوما أن يكون له غد

25/10/2022

DAGA TASKAR KARATUKAN MAL ALBANIY (ZARIA RAHMATUL LAH ALAIHI): BA DA MUHIMMANCI WAJEN KARANTAR DA SAHEEHUL BUKHARIY (April, 2008)

Littafin Saheehul Bukhariy ba ya buƙatar gabatarwa. Malamai da ɗaliban ilimi da ma sauran mutane gama-gari irina mun san matsayinsa a addinin Musulunci.

Tun a mid-80s Mal. Albaniy Zaria (Rahimahul-Lah) ya fara karantar da Bukhari. Haka nan kuma an yi wa ɗalibai darussa mabanbanta da ke da alaƙa da littafin da tsarin sa da sharhohin sa da marubucin sa da sauran su.

Daga baya, a shekarar 2008 Mal. ya sake dawo da karatun Saheehul Bukhariy daga farko. A ka ci gaba da yin wannan karatu a Markazul Salafiyyah dake Tudun Wada Zaria-Nigeria kowace Asabar da Lahadi har zuwa rana ta ƙarshe a rayuwar Mal. Albaniy. (Kaset na 308)

Ga masu son karatukan, za su iya samun audios ɗin su a tuƙullumar mu ta Telegram via the following link

https://t.me/sheikh_auwal_albani_zaria_audios

10/10/2022

ان تنصروالله ينصر كم ويثت اقدا مكم

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Maiduguri?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Address

Zannari
Maiduguri
NIL