Hasken musulunc
Hasken musulunci bayani akan adduoi dakuma wa azi
11/04/2026
15/08/2023
FATAN ALKAIRI KAWAI
KO KUN SAN CEWA
A'uzu, bikalimatullahit tammat, Min sharri makhalaq. Manzon Allah (S.a.w) yace; Duk wanda ya fadi wannan tasbihin sau uku (3) da safe Allah xai kareshi daga dukkan abin cutarwa mutum ne ko aljan dabba ce da dukkanin wata halitta Haka kuma idan ya karanta sau uku da Yamma Allah zaisanya mala'ikun da xasu rinqa gadinsa har gari ya waye. Allah kasa mudace, don Allah idan kun samu iko ku sanar da 'Yan uwa musulmai ko Allah xai bamu ladan gaba daya.
04/08/2023
JAN HANKALI
IDAN KANA AIKATA ABUBUWA UKU IMANINKA ZAI KARU:
1- Tilawal Al-Qur'ani.
2- Kiyamul-laili.
3- Azkhar.
ZAKA FUSKANCI MATSALA A KABARINKA IDAN KA MUTU DA ABU UKU:
1- Hakkin Wani
2- Dabi'ar Annamimanci
3- Hassada
ABUBUWA UKU SUNA KAUDA FUSHIN ALLAH AKAN BAWANSA:
1- Istigfari.
2- Tausayawa waninka
3- Sadaka
IDAN ALLAH YA BAKA ABU UKU TO KA GODEWA ALLAH:
1- Lafiya
2- Wadata
3- Basira
KADA KA YARDA KA AURI MACE MAI DABI'O'I GUDA UKU:
1- Mai yawan fushi.
2- Maras sirri
3- Marar tsafta (Kazamiya)
KA YI KOKARI KA GINA RAYUWARKA AKAN ABU UKU:
1- Son Allah da Manzonsa.
2- Gaskiya da Rikon Amana.
3- Hakuri da Jarrabawa a Rayuwa
ABUBUWA UKU KA ROKI ALLAH (S.W.T) YA TSARE KA DA AIKATA SU:
1- Yanke Zumunta.
2- Zagin Sahabbai.
3- Mutuwa da hakkin wani
MUTANE UKU KADA KA SAURARI MAGANARSU:
1- Makaryaci
2- Magulmaci
3- Malami mai kwadayi da son zuciya
MUTUM UKU KADA KA YARDA SU DINGA KUSANTARKA:
1- Munafiki
2- Mazinaci
3- Maras kunya
ABUBUWA UKU BA A SON JINKIRTA SU IDAN LOKACIN SU YA ZO:
1- Sallah
2- Aure
3- Jana'iza
ABUBUWA UKU RIKO DA SU YANA SAMAR DA RABO A LAHIRA:
1- Kokarin ibada
2- Kula da Nafila
3- Amfani da Halal a Rayuwa
ABUBUWA UKU SUNA HANA MUTUM TANADIN LAHIRA:
1- Dogon Buri.
2- Rashin karanta Alkur'ani
3- Nisantar sauraron Wa'azi.
MUTANE UKU SUNA SAMUN TAIMAKON ALLAH:
1- Mutumin da yake Neman aure Don ya kare mutuncin kansa
2- Mutumin da ya tafi jihadi, Domin daukaka kalmar Allah.
3- Bawa wanda aka dora masa fansar kansa.
ABUBUWA UKU NASA ZUCIYA TA GURBACE:
1- Rashin yarda da kaddara.
2- Aibata bayin Allah na kwarai
3- Wulakanta Iyaye
Ya Allah ka tsare mu daga sharrin Shaidan, ka shiryar da mu kan hanya madaidaiciya, amin.
MATA 10 WAINDA ALLAH YA
TSINE MUSU: -
ﺍﻟﻮﺍﺷﻤﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺷﻤﺎﺕ
1. Mata masu
tsaga
fuskokinsu. -
ﺍﻟﻨﺎﻣﺼﺎﺕ
ﻭﺍﻟﻤﺘﻨﺼﻤﺎﺕ
2. Mata masu
aske gashin
gira. -
ﺍﻟﻤﺘﻔﻠﺠﺎﺕ
3. Mata masu
kankare hakori
(wushirya). -
ﺍﻟﻮﺍﺻﻠﺔ
ﻭﺍﻟﻤﺴﺘﻮﺻﻠﺔ
4. Mai 'karin
gashi da wadda
ake karamata
gashin. -
ﺍﻟﺘﻲ ﺳﺨﻂ ﻋﻠﻴﻬﺎ
ﺯﻭﺟﻬﺎ
5.Matar da
mijinta ya
01/08/2023
Kadan daga cikin dabi'un fiyayyen halitta annabi muhammadu (S@W) 🙇🙇🙇: (1)Zumunci (2) uzuri(3)mutunci(4) kyautatawa(5) karbar uzuri ga wanda yafadeta(6)jinkai(7)tausayi(8)adalci(9)karamci(10)tausasawa(11)taimakon wanda bashida shi(12) kunya(13)daraja allah yabamu ikon koyi da fiyayyen halitta (S@W) 🙏🙏🙏
28/07/2023
𝐌𝐀𝐙𝐀𝐍 𝐉𝐈𝐘𝐀: Marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, Lokacin Da Yike Jawabi a Kasar Saudiya, Shekarar 1976.
Dafatan Allah Yai Masa Rahama
27/07/2023
Allahu Akbar!
Ya Allah Ka Jiɓanci lamarin Al'ummar Kasar Nijar
Ya Allah Ka tsare musu Addinin su, Imanin su, Jinin su, Lafiyar su, Dukiyar su da Mutuncin su.
Ya Allah Ka Zamo musu Majiɓanci kuma Mataimaki.
Allah Ka wanzar musu da alkhairin Ka ta sama da kasa, dama da hagu, ciki da wajen su.
Ya Rabbal Aalameen, Ya Waliyyus Saliheen. Ameen.
27/07/2023
YA ALLAH DUK TSANANIN RAYUWA KARKA BAMU IKON TSINKE IGIYAR DA KE TSAKANINMU DA ANNABI MUHAMMAD
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Numan
LB8A