Alwassiyya Channel Nigeria

Alwassiyya Channel Nigeria

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Alwassiyya Channel Nigeria, Government House Road, Abuja.

27/08/2026

Malamin ya bayyana hakan ne a yayin karatun da yake gabatarwa a kowane mako a Shiyyar Bello Way, da ke Jihar Sakkwato.

Sheikh Murtalah Bello Sokoto (Assada)

27/08/2026

Mukiyaye Salwabta Rayukan Yan Uwa Musulmi Sheikh Abdulrrahman Sani Maitawul Sokoto

25/08/2026

Kuyi Adalci Tsakanin Matanku Sheikh Abdulrrahman Sani Maitawul

Photos from Alwassiyya Channel Nigeria's post 15/08/2026

AN KAMMALA BIKIN KARRAMA FITATTUN MASU TAIMAKAWA AL’UMMA A SAKKWATO

SOKOTO: An kammala bikin karrama fitattun mutane masu bayar da gudunmawa wajen ci gaban al’umma da taimakon jama’a a Jihar Sakkwato.

An gudanar da bikin cikin nasara a Nana Khadija Usman Bn Fodiyo Hall, Nana Asma’u, Runjin Sambo, Sokoto, inda aka karrama mutane 11 bisa irin gudunmawar da suke bayarwa ga al’umma.

Daga cikin wadanda aka karrama akwai Engr. Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato), Malam Ahmad S. Fada, Dr. Adamu Bello Kasarawa, Hon. Samaila Hamisu Kuchi, Rashidat Muhammed Esq., Alhaji Abdulkadir Muhammad, Usman Muhammad Binji (Shugaban NUJ na Jihar Sakkwato), Malam Usman Idris Abubakar Sokoto, Alhaji Bashar Abubakar MC (Sarkin Hausawa), Hon. Faruk Umar Yabo (Jarman Gagi), da Bashar Aminu Sabo.

Taron ya samu halartar manyan baki da jama’a daga sassa daban-daban, inda aka bayyana muhimmancin yabawa da karrama mutanen da ke bayar da tasu gudunmawa wajen inganta rayuwar al’umma.

Kungiyar 10Youths Forum, wadda ta shirya taron, ta bayyana godiyarta ga dukkan mahalarta, manyan baki, iyaye, malamai da masu ruwa da tsaki da s**a taimaka wajen ganin an gudanar da bikin cikin nasara.

Kungiyar ta kuma yi fatan wadanda aka karrama za su ci gaba da ayyukan alheri da tallafawa al’umma domin samun ci gaba mai dorewa a Jihar Sakkwato.

Allah Ya saka wa kowa da alheri, Ya kara basira da karfin gwiwa ga wadanda aka karrama wajen ci gaba da yi wa al’umma hidima.

15/08/2026

Cigaban da Gwamnatin Muslim Muslim Takawo Prof Mansur Ibrahim Sa'id

02/08/2026

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya yi wa fitaccen mawakin siyasa Muhammad Kosan Waka rasuwa bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya.

Rasuwar tasa ta girgiza masoya da abokan sana'arsa tare da al'ummar da s**a san shi, inda ake ci gaba da bayyana alhini da addu'o'i a gare shi.

Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata kabarinsa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya ba iyalansa, 'yan'uwansa da daukacin masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.

01/08/2026
31/07/2026

USTAZ SANUSI ASADUS SUNNAH AMORE YA YI ADDU'AR FATAN ALKHAIRI GA SHEIKH ISAH ALI IBRAHIM PANTAMI

Fitaccen malamin addinin Musulunci a Jihar Sakkwato, Ustaz Sanusi Asadussunnah Amore, ya yi addu'ar fatan alkhairi ga Sheikh Isah Ali Ibrahim Pamtami Isah bayan wani faifan bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta.

A cikin bidiyon da ke yawo, ana zargin mawakin siyasa Dauda Kahutu Rarara da furta kalaman da wasu ke kallon sun zubar da mutuncin Sheikh Pantami, wanda kuma dan takarar gwamnan Jihar Gombe ne a karkashin jam'iyyar PDP.

Ustaz Sanusi Asadus Sunnah Amore ya yi addu'ar Allah Ya kare martabar malamai, Ya ba su lafiya da tsayin daka, tare da rokon Allah Ya tabbatar da gaskiya, Ya kuma hada kan al'ummar Musulmi.

Lamarin dai ya jawo muhawara a kafafen sada zumunta, inda mutane ke bayyana ra'ayoyinsu mabambanta kan bidiyon da ake yadawa.

Abba Sani Pantami

31/07/2026

NEMAN TALLAFIN CETON RAYUWA 🚨

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai.
Ana roƙon al'umma, 'yan uwa, abokai da masu hannu da shuni da su taimaka wajen tara kuɗin jinyar Sheikh Abdul-Rashid B. Lawal Sokoto, wanda ke fama da matsananciyar rashin lafiya kuma yake buƙatar kulawar gaggawa.
Adadin kuɗin da ake buƙata domin gudanar da jinyarsa ya kai Naira Miliyan 100 (₦100,000,000). Kowane irin gudummawa, babba ko ƙarama, na iya zama sanadin ceton rayuwa.

Allah Maɗaukakin Sarki Ya ce:
﴿وَإِذَا مَرِضْتُ فَهُوَ يَشْفِينِ﴾
"Kuma idan na yi rashin lafiya, Shi ne Yake warkar da ni."
(Suratush Shu'ara'i: Aya ta 80).

Bayanan Asusu:
Badamasi AbdurRasheed Lawal
Banki: First Bank
Lambar Asusu: 3052574497

Allah Ya saka da alheri ga duk wanda ya bayar da gudummawa, ya yaɗa wannan saƙo, ko ya yi addu'ar samun sauƙi. Allah Ya ba Sheikh Abdul-Rashid B. Lawal Sokoto cikakkiyar lafiya da waraka. Amin.

30/07/2026

🕊️ INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Ya yi wa Sir Abubakar Alhajin Alhaji Sardauna Sokoto rasuwa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Allah Ya karɓi ran Sir Abubakar Alhajin Alhaji Sardauna Sokoto a yau, 30/07/2026.

Muna miƙa ta'aziyya ga iyalansa, masoyansa, da al'ummar Jihar Sokoto baki ɗaya bisa wannan babban rashi. Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya jiƙansa da rahama, Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sa Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, Ya kuma bai wa iyalansa da al'umma haƙurin jure wannan rashi.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Government House Road
Abuja