Al- muhsin foundation zaria

Al- muhsin foundation zaria

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Al- muhsin foundation zaria, Health/Beauty, .

18/06/2023
18/06/2023

Kadan daga cikin sana'oin da muke yikenan

18/06/2023

AL-muhsin foundation Zaria
Motto: skills for life
Address:anguwan taki Kwarbai Zaria
City kaduna

12/11/2022

Yadda bayanin yake ga 'yan uwa wadanda basu samu damar sanin bayanin da CBN tayi ba.
__________________________________
Za'a fara amfani da sababbin kudaden Naira 200, 500 da Naira 1,000 ranar Al-Hamis 15 ga watan December 2022 din nan in sha Allah.
~ Daga wannan ranar sababbin kudaden da tsofaffin duk za suyi ta aiki a matsayin Legal Tender, wato kudi na zahiri na gaskiya.
~ Amma daga ranar 31 ga watan January na shekara me zuwa, 2023 Kuma tsofaffin 200, 500 da 1,000 zasu daina aiki a hukumance.

~ Abin nufi idan kaje ka Kai kudin ranar 31 ga watan January Banki, zasu karba ranar karshe kenan, washegari ranar 1 ga watan February (Watan Biyu) na 2023 idan kaje da kudin Banki ba zasu karba ba.
~ Kuma kaima kada ka karbi tsofaffin kudaden a Shagon ka ko wajen kasuwancin ka daga ranar 1 ga watan February, domin ko kaje Banki ba zasu karba ba.

~ Domin ka saukakawa kanka a wajen Sana'ar ka toh ka daina karban tsofaffin kudi daga ranar 25 ko 27 ga watan January kawai.
~ Duk Wanda zai baka ya baka daga cikin sababbi, domin akwai su a lokacin, suna nan suna zagayawa tare da tsofaffin.
Kada kaje kayi ta Tara kudi da nufin zaka Kai Banki wani Dalili ya taso ya hana kaiwa, har a wuce 31 January, idan kaje musu da kudin on 1 February ba zasu ko saurare ka ba ma.

~ Hatta masu POS suyi hankali, su lura wajen karban kudade a yanzu da kuma lokacin da ake Daf da 31 January, domin "Fake Notes" zasu iya shigowa cikin mutane, idan baka Saba ta'ammuli da kudi ba ba zaka taba iya gane su ba, sai kaje Banki kaga ana ta ware maka su, ana cewa ba kudi bane.
~ Takarda ce kawai ko plain sheet ne kawai yasha ado da Fenti kamar kudin gaske, alhali Kai Kuma an baka ka tura wa mutum ta Account, Transfer, kaga an barka da asara.

~ Allah ya tsare ya kiyaye, Amma gaskiya a lura da kudade sosai a 'yan wadannan watannin da s**a rage.
Allah yasa mu dace...
✍️

Website