dr_fayyuza_ibrahim_idris

dr_fayyuza_ibrahim_idris

Share

My product is oriflame product
and many knows that their product is very nice to people

Because if you use it you will feel good��
#Testy Money���

10/04/2024

*Taqabbal Allāhu minnā wa minkum!*

Alhamdullillah Rabbal Alameen for His rahama to witness the end of this *Ramadan 1445AH.*

May Allah accept our siyam, our qiyam, our duʿa’, our charity and all our ʿIbadah, and May He make us witness many more of it. And may Allah help us restore peace in Nigeria. Aameen🙏🏼!

*EID - MUBARAK TO YOU AND YOUR FAMILY*
اللهم إنك عفو تحب العفو فاعفو عن

08/04/2024

ZAZZABIN RANA (SUN ECLIPSE) ZAI SHAFI GANIN WATAN SHAWWAL

Hukumar nazari da binciken sararin samaniya na Kasar Amurka "National Aeronautics and Space Administration" (NASA) tace ranar Litinin 8-4-2020 ( nan da kwanaki biyu) duniyarmu na Earth zata fuskanci mafi tsananin zazzabin Rana (Sun Eclipse)

Kamar yadda sakamakon binciken NASA ya nuna, duk bayan shekaru 364 duniyar mu tana samun irin wannan zazzabi mafi girma da tasiri da yake jikkata Rana

Mutanen duniya da s**a rayu shekaru 364 da ya wuce sunga irin zazzabin, to bayan anyi wannan na ranar Litinin idan Allah Ya kaimu ba za'a sake fuskantar zazzabin Rana mai girma da yake shafan duk duniya ba sai bayan wasu shekaru 364 (Idan Allah bai tashi Alqiyama ba kenan)

Hukumar NASA sunce Rana zata rasa haskenta da kaso 90 cikin 100 na tsawon awanni 5 zuwa 7, ba zamu ga hasken Rana ba, duniyarmu zatayi duhu (SubhanalLah)

Zazzabin ranar zai shafi batun ganin watan Shawwal ranar Litinin idan mun kai azumi 29 kenan, saboda a cewar Geographers wai Wata yana zukar hasken rana ne, to idan ya kasance Rana tayi zazzabi a ranar to ganin sabon jinjirin watan Shawwal zai zama da wuya

A matsayin mu na Musulmi munyi imani da Allah cewa dukkan juyawan Lamari a Hannun Allah su ke, binciken NASA na iya zama gaskiya ko akasin haka

Idan hakan ta faru akwai yadda Musulunci ya karantar zamuyi, kuma zazzabin Rana da Wata fadakarwa ne Allah Ya ke yiwa mutanen duniya akan cewa mu hankalta, domin akwai wata rana da Allah zai jingine Wata da Rana, Qiyamah ta tsaya kenan

Yaa Allah Ka sa mu wanye da duniya lafiya 🙏

16/03/2024

Karkaji ana cewa mace Mai rauni ce yazama baka Neman shawarar ta a gida
Da wuya ka nemi shawarar matarka a wata harkar tabaka shawara kaga bakayi nasara ba

NANAH KHADIJA MATAR MANZON ALLAH (S.A.W)
Ta isheka misali.
Allah yakara muku Albarka Mata iyeyenmu

Photos from dr_fayyuza_ibrahim_idris's post 10/03/2024

Yau kwana 40 kenan ba tare dake ba ummina😭😭😭, karin farko zanyi azumi ba tare da jinki ko ganinki ba hajiya ummah na 😭😭😭, Ubangiji Allah yayi miki rahama hajiya ummah na 😭💔😭, Allah Yasa kina cikin aljannarsa madaukakiya ummina 😭😭😭 🤲🤲🤲!!!.

10/03/2024

Anga Wata A Najeriya....

Mai alfarma Sarkin Musulmai ya bada sanarwar fara Azumin watan Ramadan 1445 daga gobe Litinin 11/3/2024 insha Allah.

The Sultanate Council Sokoto has declared Monday 11/3/2024 as the first day of Ramadan 1445 AH.

Yahaya Muhammad Boyi
Sarkin Malaman Sokoto .

10/03/2024

LADUBBAN DA AKA SO MAI AZUMI YA KIYAYE SU….

Lallai akwai ladubba masu yawa da ake son mai azumi ya kiyaye su, ga Kaɗan daga cikinsu.
1- Yin sahur saboda hadisin Anas inda ya ce, Manzon Allah (S A W) ya ce, Ku yi sahur a cikin sahur akwai albarka, sannan mutum zai iya yin sahur ko da da dabino ne, ko ya sha ruwa.

2- Gaggauta buɗabaki, Manzon Allah (S A W) ya ce, Mutane ba za su gushe ba, suna cikin alkhairi da riskar alkhairi, matuƙar suna gaggauta buɗa baki. Manzon Allah (S A W) ya kasance yana fara yin buɗabaki ne, sannan sai ya zo ya yi Sallah, kuma yakan ci ɗanyen dabino ko bushasshe in kuma babu sai ya sha ruwa.

3- Yin addu’a lokacin buɗabaki, Manzon Allah (S A W) ya kasance idan ya yi buɗa baki yakan ce,

‎(ذَهَبَ الظَّمَأُ وَابْتَلَّتِ الْعُرُوقُ وَثَبَتَ الْأَجْرُ إِنْ شَاءَ اللهُ)
Ma’ana: Qishirwa ta tafi, jijiyoyi sun jiƙa, lada kuma ya tabbata da yardar Allah.

4- Mutum ya kiyaye gaɓɓansa ga barin abin da zai ɓata darajar azuminsa, wato ya nisanci gulma, da qarya, da cin amana, da ha’inci, da kage, da shaidar zur, da annamimanci, da duk wasu ayyukan da zasu iya jawo masa zubewar mutuncinsa a wajen Allah.

5- Yawan kyauta a watan azumi, da yawan karatun Alqur’ani da yawan koyar da shi, Manzon Allah (S A W) ya kasance mafi alkhairin mutane, kuma ya kasance mafi alkhairin lokacin da ya fi kowane lokaci kyauta shi ne a watan Ramadan a yayin da Mala’ika Jibrilu yake haɗuwa da shi, s**an haɗu a kowane dare na watan Ramadan har watan ya wuce, ya kasance Jibrilu yana bujuro masa da Alqur’ani suna yin bitar sa tare.

6- Ana so mai azumi ya yawaita ibada a dare da rana a watan Ramadan, Manzon Allah (S A W) ya kasance idan goman ƙarshe ya shigo yakan raya dare da ibada, kuma yakan tashi iyalansa suma su raya darensu, sannan ya kasance yakan qara daura ɗamara, ma’ana yakan qara dagewa sosai wajen ibada.

Ubangiji ka azurtamu da rabauta da falalar wanan wata na ramadan, daya ke gaf da zuwa gare mu.

06/03/2024

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN

Allah yayiwa tawfiq rasuwa d'an gidan yaya babangida, dazu bayan isha'i za'ayi jana'izan shi da safe In Allah Ya kaimu à Adamawa mubi

30/01/2024

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!!!
Allah ya yiwa mahaifiyata rasuwa yau bayan sallar magriba a garin Kano, za'ayi Jana'izarta gobe da safe in Allah ya kaimu, lallai idanuwanmu suna hawaye zukatanmu kuma suna bakin ciki amma ba za mu fadi wata kalma ba sai wanda Allah ya yarda da shi, Allah ya jikanki da rahama yasa kin huta yasa Aljannatul Firdausi ce masaukinki ya ummee amin Ya Hayyu Ya Qayyum...

30/01/2024

Innalillahi wa inna ilaihirraji'un
Innalillahi wannan inna ilaihirraji'un
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un

Allah yayiwa mahaifiyata rasuwa

22/01/2024

Shekara Dubu hamsin (50.000) zamuyi muna tsaye muna jiran hisabi a Filin kiyama ko kallonmu bazaayi ba . baci basha ba bacci 😢😢 ga wuta an masto da ita muna kallonta gamu cikin tsananin zafin rana.
Innalillahi wainna ilaihiraju'un. 😭😭😭😭
Shin Muna tuna wannan ranar kuwa
Allah kasa mu cika da Imani.

02/10/2023

Ya ubangiji Allah ka bawa kasarmu Nigeria zama lafiya da ci gaba da arziki me dorewa.
Allah ka shiryar da shuwagabannin mu izuwa yi mana adalci.
Allah kada ka basu ikon zaluntantan mu,
Ya Allah koda sunyi niyya su cutar damu Allah ka karkatar da zuciyoyinsu ga tausayimmu izuwa suyi mana adalci akan tsare dukiyoyimmu, rayukammu, da lafiyanmu.
Muma Allah kasa mu zamo masu tausayin junan mu da kuma yiwa junanmu adalci domin mu sauki daga gareka ya Allah!!! 🤲🤲🤲

13/09/2023

Allah ya jikanka da rahama baba Allah yasa ka huta,Allah yasa aljannah ce makomarka, Allah yasa mutuwa hutu ne a gareka mu kuma Allah ya kyauta namu zuwan baba am!😭😭😭.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Jeddah?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Jeddah
KN/020/KWR/ONLN/MARKET/0061