Gyaran Aure

Gyaran Aure

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gyaran Aure, Beauty, cosmetic & personal care, Abuja.

01/07/2022

YADDA AKE ZAMAN AURE DA NAMIJI ME SAURIN FUSHI


shi fushi dabi'ahce ta dan adam

kowanna mutum yana fushi akwai sanadaran fushi acikin kwakwalai da suke a tara wanda dan adam ke gadosu daga iyayen sa IDAN KANA DA SANADARAN DAYAWA SAI KAZAMA ME SAURIN FUSHI KENAN.

IDAN MACE TA AURI NAMIJI ME SAURIN FUSHI TO TANA CIKIN MATSALA IDAN BATABI A HANKALI BA WATARANA AKAN ABU KADAN ZAIMATA DUKA YA FARFASA MATA JIKI HARDA KARYA HAKORI WANI KAN IYA KARYAWA MACE QAFA MA .

yar uwa inkina da namiji me yawan fushi to ana so kizama me lura sosai da wadannan abubuwa:

* meye yake saurin sa shi fushi da tunzura?
* meye yake saurin sauko dashi in yayi fushi ?

*Wani namijin bayasan yawan surutu in yana jin yunwa, ko in yadawo daga gun aiki.

*wani namijinn yakan ji saurin fushi in bashi da kudi ko yaje sana'arsa bai samo komaiba.
Wani kuma yafi fushi da bata rai in yasami kudi ko ya dauki albashi duk dan karki dameshi da kinmatsa kuwa za abata.

* wani idan aka batamasa rai a waje koda a musune sai ya dawo gida da fushi dazarar kin tsokanoshi kadan sai ki taka sawun barawa yai tai miki masifa inba kiya sa a bama yai miki duka.

* wani baya so yanai miki magana kema kinai masa magana sai yai fushi da harzuqa zaiga kinma raina shi yana magana kina magana yafisu in yafada kiyi shuru har sai yagama.

WANI KUMA HAKAN YATSANA
YAFISO YANA FADA KINA FADA DA KINYI SHURU SAI YADAUKA KIN RAINA SHINE.

wani kuma baya son gatse ko zolaya ko yawan wasa nandanan sai ya hau fushi.

Dan haka ke zaki karanci halin mijinki kisan yadda yake dakuma hanyoyin da zakina mu amalantarsa.

*SANNAN DOLE KI ZAMA ME HAAKURI FIYE DA KOWACCE MACE AMMA INBA HAKABA GIDANKI ZAIZAMA FAGEN DAGA SAI KIGA KUN FUTA DABAN A UNGUWA YAYAN KUMA HAKA ZASUTASO.

TAYAYA ZA A CANJA DABI'AR SAURIN FUSHI?

** aiki da ilmi da tarbiyyar muslunci sune kadai zasu saita mutum me yawan fushi domin akan sami me tarin ilmi amma baya aiki da ilmin saikaga da ransa yabacci ya tabka wani rasshin da'ar.

Amma duk me aiki da ilminsa da ransa yabaci yayi fushi to zai nemi taimakon Allah sai kuga yaqi yanke hukunci cikin fushi kamar yadda Manzon rahama s.a.w ya umarta.

Domin shi fushi dabi ace ajikin rai baka da ikon hana kanka jinsa AMMA SAAI ANNABIN RAHAMA YACEMA KAZAMA ME MALLAKAR ZUCIYARKA A YAYIN FUSHI.

YAKUMA HANAKA YANKE HUKUNCI A YAYIN FUSHI.

DAFATAN MAZAJE MASU SAURIN FUSHI DA MATANSU ZASU LURA SU RAGE sugane raunin dake tattare da su na hankali tunani hali da dakuma jiki.

ALLAAH YASA MUDACE

04/06/2022

Abubuwan Da S**a Dace Uwa Ta Sanarwa 'Yarta A Lokacin Tasowarta:

SHARE 💕


Akwai abubuwa da dama da s**a dace duk uwa ta tabbatar ta sanarwa 'yata musamman a lokacin da ta soma zama mace.

Wadannan abubuwan zasu taimakawa diya mace wajen sanin yadda rayuwa yake.
Ga wasu abubuwan da s**a kamata duk uwa ta sanarwa'yata.


1: Yana da kyau duk uwa ta nunawa 'yarta tare da sanar da ita mahimmancin da illimi yake dashi a rayuwarta.

Sanarwa diya mace mahimmanci illimi na addini dana zamani zai baiwa diya mace kwarin gwaiwa da zata maida hankalin ta domin ganin ta samesu.

Dole ne uwa ta nunawa 'yarta a wannan lokacin da ake ciki babu macen da take da daraja cikin al'uma sai idan tana da illimi.

2: Uwa ta nunawa 'yarta cewa, yanada kyau idan an mata ba dai-dai ba tayi magana. Idan an mata daidai nan ma tayi magana.
Rashin nunawa 'ya mace hakan yasa ake cutarwa da 'ya'ya mata kuma su kasa magana. Ko kuma a musu abun arziki basu iya nunawa godiyarsu ba.

Nunawa diyarki duk wanda yayi mata ba daidai tanada damar ta masa magana amma cikin girmamawa. Haka nan duk kankantar abun kwarai da aka mata ta nuna farin cikinta da godiya ga wanda s**a mata. Kada ta zama mara magana kada kuma ta zama mara godiya.

3:Nunawa 'yarki a rayuwa akwai samu kuma akwai rashi. Sanar da ita hakan zai fahimtar da ita rayuwa.
Idan yarki tana cikin wadata ne, ma'ana iyayenta nada wadata. Dole ne a nuna mata cewa akwai miliyoyin mutane da yanzu haka suke kwana da yunwa. Akwai kuma masu wadatar da har zubba abinci suke. A nuna mata alherin dake cikin taimakawa marasa shi. Da kuma yiwa Allah (SWT) godiya ako wani yanayi mutum ya samu kansa.

4: Ki nunawa 'yar ki yadda zata mutunta mutane. Yadda zata daraja mutane.
Nuna mata ba wasu sun fi wasu bane saboda Allah baya son marasa shi bane. Kawai haka tsarinsa yake.
Ta kuma sani marashi a yau na iya samu a gobe. Don haka duk wani mutum data gani ta mutuntashi ta daraja shi.

5: Kada ki boyewa 'yarki sanin tarihi da kaita asalin tushenta. Duk wata uwa, dole ne ta nunawa 'yarta cewa sunada asali, koda kuwa talauci ko kaskanci ne a asalin nasu.

Uwar da zata nunawa ko ta sanarwa 'yata wadannan abubuwan ko makamantansu, dole ne diyarta ta taso cikin tarbiya da sanin ya kamata.

~ Sirrin Rike Miji

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Website

Address


Abuja