Na'allah Sheka

Na'allah Sheka

Share

Shadda Atampah Night ware

23/12/2024

Nightfam, a tree that looks like it's taking a giant stride is New Zealand's Tree of the Year!

This 32-metre tall rātā doesn't just stand there - it has an incredible survival strategy. It starts life growing ON other trees, then sends its roots down to create its own massive trunk, making it look like it's mid-walk across the landscape.

Looking exactly like something from Lord of the Rings, this ancient giant crushed the competition with 42% of votes, even beating New Zealand's famous Instagram-star tree!

The best part? These trees can live for 1,000 years. Imagine the stories it could tell...

Nightfam, what's the most incredible tree you've ever seen? 🌳

📷 Gareth Andrews

23/12/2024

Me ya sa yarona ya kasa riƙe wuya, zama da tsaiwa a watannin da ya kamata?

Daga cikin larurorin da ke shafar jarirai ko yara yayin da suke cimma matakan girmansu akwai larurar 'shanyewar ƙwaƙwalwa' ko kuma 'dakushewar ƙwaƙwalwa' da a ke cewa "Cerebral Palsy" a turancin likita, wannan larura ce da kimanin mutum miliyan 17 ke fama da ita a faɗin duniya. Kuma ita ce larura mafi nakasa yara yayin girmansu. Wannan matsala ce da ta fi shafar motsin gangan jiki, magana/furuci, gani, da sauransu sakamakon 'shanyewar ƙwaƙwalwa'.

Yawancin yaran da matakan girmansu ke tafiyar hawainiya suna fama da 'shanyewar ƙwaƙwalwa' ne saboda lahanin da ke samun ƙwaƙwalwarsu kafin ta gama girma kamar:

1. Yayin rainon ciki: misali,

i - jirkicewar jigidar halitta, wato 'genetic mutation' a turance.

ii - haihuwar bakwaini, da sauransu.

2. Yayin haihuwa: misali,

i - doguwar naƙuda,

ii - shaƙewar jijiyar jini ta cibiya yayin naƙuda,

iii - shawara, wato rikiɗewar fatar jiki da farin ƙwayar ido zuwa rawaya/zabibi.

iv - matsanancin zazzaɓi bayan an haifi jariri ko kuma a watannin farko na rayuwa da dai sauransu.

v - Haka ma jariran da s**a gaza yin kuka nan-take bayan haihuwarsu na da haɗarin samun wannan matsala.

3. Bayan haihuwa: misali,

i - cutar sanƙarau, wato 'meningitis' a turance.

ii - zazzaɓin cizon sauro mai ratsa ƙwaƙwalwa, wato 'cerebral malaria' a turance kenan.

Alamomin 'shanyewar ƙwaƙwalwa' sun haɗa da:

1. Kasa iya motsa sassan jiki; saboda waɗansu yaran jikinsu na da rauni, waɗansu kuma jikinsu ko gaɓɓansu kan rirriƙe ne. Misali, waɗannan yara kan gaza iya riƙe wuya a wata 3, zama a wata 7 – 8, rarrafe da riƙe abu a miƙe a wata 9, tafiya a wata 12 da sauransu. Saboda haka, wuce lokacin da ya kamata yaro ya cimma ɗaya daga cikin matakan girma da aka sani a al'ada na nuni da cewa akwai matsala.



2. Kasa iya magana/furuci.

3. Dalalar da yawu/miyau.

4. Matsalar gani, juyewar ido ko hararagarke.

5. Matsalar/wahalar cin abinci da sauransu.

Abubuwan da ya kamata ka sani game da yara masu larurar 'shanyewar ƙwaƙwalwa' sune:

1) Duk yaro ɗaya cikin yara huɗu ba ya iya furuci/ magana.

2) Duk ɗaya cikin uku ba ya iya tafiya da kansa.



3) Ɗaya cikin yara biyu na da dakushewar kaifin basira yayin koyo.

4) Ɗaya cikin huɗu na da farfadiya.

Sai dai, abin takaicin shi ne 'shanyewar ƙwaƙwalwa' ba larura ce da ake shan magani a warkewa nan take ba. Amma ƙwararru na yin duk mai yiwuwa don tabbatar da cewa yaran sun cimma matakan girman da za su iya kula da kansu cikin ayyukan yau da kullum ba tare da sun zama nauyi ga iyaye ba.

Mafi ban takaici daga wannan ma shi ne yadda sau da yawa al'umma da iyaye ke tunanin wai irin waɗannan yaran aljanu ne s**a taɓa su, ko s**a shanye musu gaɓoɓinsu, ko kuma wai suna da taɓin hankali ne. Wannan sam ba haka ba ne! Wannan ya kan sa a bar yaro a gida ba tare da kai shi asibiti ba, hakan zai sa yaro ya nakasa har ya tsuguna ɗungurungum.

Muna ƙara jinjinawa iyayen yaran da s**a fahimci wannan larurar kuma suke ƙoƙari ba gajiyawa wajen zuwa asibiti akai-akai. Muna sake kira da kada a gajiya ganin cewa ba a samun ci gaba cikin gaggawa. Ya kamata a sani cewa wannan matsalar ba a shan magani a warke nan-take, saboda haka haƙurin ziyartar asibiti akai-akai ita ce mafita kawai.

Likitocin fisiyo na gaba-gaba wajen tallafa wa rayuwar waɗannan yara domin su sami mafi ingancin rayuwa gwargwadon tsananin 'shanyewar ƙwaƙwalwar' da s**a samu.

Yaran da s**a sami kulawar likitocin fisiyo tun da wuri na cimma matakan girmansu kaɗan da kaɗan, gaɓɓan jikinsu su yi ƙwari har su kamo sa'anninsu. Ta wannan hanya ce kawai irin waɗannan yara ake temaka musu har su iya kula da kansu, su je makaranta ko su koyi sana'a bayan sun girma, maimakon barinsu su nakasa kuma su zama nauyi ga iyaye ko kuma mabarata a titinanmu.

Garzaya da yaro asibiti da zarar an lura da matakan girmansa na tafiyar hawainiya, ko kuma bayyanar wasu daga cikin alamomin da muka ambata a sama domin ba shi kulawa ta musamman tun da wuri don ceto shi daga nakasa.

© Physiotherapy Hausa

Photos from PressExpress Nigeria's post 23/12/2024
23/12/2024

Gwamnatin Nijeriya ta ƙuduri aniyar gurfanar da aminan ɗan bindiga Bello Turji su takwas, da ma shi kansa da yanzu haka ake nema ruwa a jallo.

TALLAH: KSBDATA Kamfanin Da Ya Yi Fice Wajen Kasuwancin Data Da Katin Waya

Domin fara sána'ár DATA ko kuma ku dinga saka wa kanku, ku sáuké Mánhájar KSBDATA a PláyStore.
👇👇👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.ksbdata.app

Website
👇👇👇
https://app.ksbdata.com

WhatsApp
👇👇👇
https://wa.me/2349018986971

23/12/2024

Tattalin arziƙin Najeriya ya haɓaka da kashi 3.46 a rubu'i na uku na shekarar 2024, daga kashi 3.19 a rubu'i na biyu na shekarar.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/3VSLeh8

23/12/2024

Ilimin halittar tayi da Annabi ya zo da shi ya tabbatar mana Manzon Allah ne — Farfesa Keith More.

Farfesa Keith L. Moore PhD, DSc, FIAC, FRSM, FAAA, bijimin malami ne kan ilimin surar ɗan Adam da kuma ilmin halittar tayi a jami'ar Toronto, Canada. Farfesa Keith L. Moore, ya yi rubuce-rubuce da gabatar da muƙaloli masu ɗimbun yawa a waɗannan fannoni.

Kuma zuzzurfan binciken da farfesan ya gudanar tsawon lokaci ya haifar da wallafa shahararren littafinsa kan ilmin hallittar tayi, wato 'The Developing Human: Clinically Oriented Embryology'. Har zuwa yau, wannan littafi ya fi kowane littafi a wannan fanni karɓuwa a ƙwalejojin koyar da likitanci a faɗin duniya.

A ƙoƙarin neman madogara da dalilai kan halittar tayi, farfesan ya kafa hujjoji da ayoyin ƙur'ani da hadisai wanda s**a yi bayani kan halittar ɗan Adam a cikin uwa.

Bayan wallafa wannan littafi kuma, ya gabatar da muƙalolin a tarukan kimiyya daban-daban inda yai ta bayyana yadda bayanan halittar ɗan Adam a cikin ƙur'ani da hadisai s**a yi cif da cif da binciken zamani.

A wani taron ƙasa da ƙasa kan iliman kimiyya da ke cikin ƙur'ani da sunnah, wanda aka gudanar a ƙasar Masar a shehara ta 1989, Farfesa Keith L. Moore, ya gabatar da muƙala mai taken: "Abinda ƙur'ani ya ce kan halittar tayi", inda kuma ya ƙarƙare muƙalar da cewa "ya kamata a riƙa amfani zangunan halittar ɗan Adam da ƙur'ani ya ambata wajen koyar da ɗalibai musulmi, saboda ya yi dai-dai da binciken zamani kan halittar ɗan Adam kafin haihuwa, kuma zai bai wa likitoci da malam jinya musulmi damar yi wa marasa lafiya bayani kan halittar ɗan Adam dogaro da ƙur'ani. Abu ne mawuyaci Annabi Muhammad (SAW) ya san ilimin halittar tayi tun a ƙarni na bakwai im ba hawayi aka yi masa ba, saboda mafi yawancin iliman har sai a ƙarni na 20 binciken kimiyya ya kai ga gano su. Wannan ya tabbatar min ce wa, tabbas annabi Muhammad (SAW) jakadan Allah ne".

Bugu da ƙari, farfesa Keith L. Moore ya yi ta maimaita wannan magana a laccoci da sauran tarukan kimiyya, wanda hakan ya janyo raɗe-raɗi kan musuluntarsa. Bayan yawaitar wannan raɗe-raɗi, an tambaye shi a bayyanar jama'a cewa ko ya musulunta, inda ya ce ya yi imani da Allah, kuma yana girmama sauran addinai, sai dai yana bauta wa Allah ne daban da yadda musulmi ke yi kawai, kuma babu buƙatar dole sai ya musulunta kafin ya bauta masa.

Sai dai, duk da haka, mutane sun ci gaba da cece-kuce kan tabbacin musuluncinsa, inda wasu ke ganin ya ɓoye musuluncinsa ne kawai duk da bayanin da ya yi a bayyanar jama'a.

Farfesa Keith L. Moore ya mutu ranar 5 ga watan Disamban 2019 yana da shekara 94 a duniya.

© Physiotherapy Hausa

23/12/2024

Tatsuniyoyi Biyar Game Da Ciwon Gwiwa

Nau'in ciwon gwiwa wanda ake cewa amosanin gwiwa, wato "knee osteoarthritis" a turance, nau'in ciwon gwiwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa. Gurunguntsin gaɓa wani matashi ne da ke samar da taushi a gaɓa domin taimaka wa ƙashi da ƙashi yin gogayya da juna ba tare da wata tirjiya ba.

Sai dai, wannan ciwo na amosanin gwiwa na fama da gurguwar fahimta da kuma ɗumbun tatsuniyoyi da ke kewaye da shi, wanda hakan ne kan kawo tsaiko wajen ɗaukan matakan da s**a kamata wajen neman hanyoyin da za a shawo kan ciwon daga tushe.

Daga cikin tatsuniyoyin da s**a shafi ciwon amosanin gwiwa akwai:

1. Cewa wai ciwon amosanin gwiwa ciwon sanyi ne.

Ciwon amosanin gwiwa ba shi da wata alaƙa da sanyi ko ciwon sanyi, saboda haka, ba sanyi ne ke sababinsa ba face zaizayewar gurunguntsin gaɓa. Sai dai, akwai ɓuƙatar bambancewa tsakanin ciwon amosanin gaɓa wato "osteoarthritis" da kuma ciwon sanyin ƙashi wato "rheumatoid arthritis", wanda ciwon kumburin gaɓɓai ne da ya fi shafar ƙananun gaɓɓai kamar gaɓoɓin yatsun hannu da ƙafa.

Bugu da ƙari, kamar yadda aka ambata cewa ba sanyi ne sababin ciwon amosanin gwiwa ba, amma yanayin sanyi ko hunturu, danshi ko laima ko kuma kaɗawar iska mai sanyi na iya ta'azzara ciwon amosanin gwiwa.

2. Cewa kowane tsoho sai ya samu ciwon amosanin gwiwa.

Cewa kowanne tsoho ko duk wanda shekarunsa s**a miƙa tilas ne zai gamu da ciwon gwiwa tatsuniya ce kawai. Kawai dai shekaru na miƙawa haɗarin kamuwa da ciwon na ƙaruwa ne. Saboda haka sau da dama tsofi kan ƙare rayuwarsu ba tare da sun gamu da ciwon ba.

Haka nan, kowa, a kuma kowace shekara na iya samun wannnan ciwo musamman idan yana da matsalolin da ke da haɗarin janyo shi.

3. Cewa shan magungunan rage ciwo shi ne kaɗai zai magance ciwon gwiwar.

Magungunan rage raɗaɗin ciwo jinsin 'NSAIDs' ana amfani da sune kaɗai domin rage matsanancin ciwo na wani ɗan lokaci.

Amma irin waɗannan magunguna ko kaɗan ba su da tasirin warkar da zaizayewar gurunguntsin gaɓa, sai dai rage raɗaɗin ciwon na ɗan lokaci. Kuma a yayin da aikinsu ya ƙare a jiki ciwon zai sake dawowa sabo ne.

4. Cewa ciwon gwiwar ana warkewa gaba ɗaya.

Ciwon amosanin gwiwa kamar yadda muka ambata cewa yana faruwa ne sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa. Saboda haka, zuwa yanzu babu wani magani da aka sani yana toho da gurunguntsin da ya riga ya zaizaye.

Sai dai akwai magungunan da ka iya taimakawa wajen ƙara lafiyar gurunguntsin da ya ragu, da kuma hana ci gaban zaizayewarsa.

5. Cewa guje wa ayyukan da ke kawo motsa gaɓar gwiwa zai rage ta'azzarar ciwon.

Kamar yadda aka sani a yayin da ciwon ya ta'azzara masu ciwon kan guje wa ayyukan da ke da alaƙa da motsin gwiwar tsawon lokaci, kamar tafiya. Sai dai guje wa motsa gaɓar gwiwar yadda ya kamata tsawon lokaci na da gagarumar illa ga lafiyar gwiwar.

Daga ƙarshe, masu ciwon amosanin gwiwa na buƙatar ganin likitan fisiyo da zarar sun fara jin alamun ciwon domin shawo kan ciwon ta hanyar amfani da na'urorin rage ciwo da kuma keɓaɓɓen atisaye da zai taimaka wajen ƙarfafa tsokokin da ke riƙe da gwiwa — wanda hakan zai rage saurin zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa.

KA GAJI DA SHAN MAGANIN CIWON GWIWA KULLUM? TO GA MAFITA.

Duba cikakken bayani a nan https://www.facebook.com/share/p/18QCYgBcTv/

© Physiotherapy Hausa

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Sheka Gidan Kaji Kano
Abuja