Hausa Light

Hausa Light

Share

Peace

Photos from Hausa Light's post 19/01/2024

Zabi Amsa Cikin Tambayoyin

Tambaya Akan Maza ? Zabi 1 Cikin 2

1= Za'a Janye Kayan Lefe Amma Kayan Daki (Furniture)Da Abincin Gara Baza'a Kawo Maku Ba Saidai Kuyi da Kanku

2 = Zaku Kawo Kayan Lefe Amma Za'a Kawo Maku Kayan Daki (Furniture) Da Abincin Gara

Tambaya Akan Mata ?Zabi 1 Cikin 2

1 = Baza'a kawo Maki Kayan Lefe ba ko Kudin Nagani Ina So Saidai Akawo Maki Kudin Sadaki Kadai Amma Za'ayi Amfani Da Kudin Kayan Lefe da Nagani Inaso Don a Cika Ayi Gidan Da Zaku Zauna Naku na Kanku

2 = Za'a Kawo Maki Kayan Lefe Amma Gidan Haya Za'a Zauna Saboda Kudin Sun Shige a Wurin Sayan Kayan Lefe

Tambaya Akan Maza Da Mata ? Zabi 1 Cikin 2

1 = Ko Wanne Bangare Zayyi Daidai Karfinsa Batareda Korafin Gazawar Bangare 1 ba

2 = Ko Wanne Bangare Zai Tsauwala Koda Kuwa Daga Wani Bangaran Baida Karfi ?

31/12/2023

Ya Allah ka kara mana Soyayyar Annabi Muhammad S A W ka kyautata karshenmu👏

21/12/2023

Akwai Gyara
A Arewarmu ta Nigeria Aure Ya Zama Wajibi Amma Kula da Matar da Tarbiyantar Da 'Ya'ya ya Zama Makaruhi,
Zaka Samu Al'ummarmu Sunfi Ganin Illar Mara Mata (Gwauro ko Tazuru)Ko Macce Mara Aure Acikin Al'umma Koda Kuwa Suna Kare Mutuncinsu Amma Za'aga Amfi Ganin Mutuncin mai Mata da 'ya'ya da Yawa Koda Kuwa Haihuwarsu yake Baya Basu Tarbiya Saidai ya Watsa ma Duniyasu Su Zama Annoba .
Mafi Akasarinmu a Arewacin Nigeria Munfi Maida Hankali Wurin Cin Abinci da Jima'i Shiyasa Kullum Masu Magani S**afi Karkata a Maganin Maza kona Mata ,Bamu Cika Damuwa da Lissafin Mai Zamu zama ba ko Idan Muka Haifi Yaya Wanne Mataki Mukeso yayanmu su kai Domin su Taimaki Al'umma .
Abun Takaici Arewacin Nigeria ne Zakaga An Fiye Gori na Aure ,Zaka Samu Mutum Wanda yakeda Mata da Yaya baya Kulawa dasu Yanda ya dace Amma Sai ya Koma Gefe 1 yana Yima Abokinsa Gorin Aure ko Gorin Yaya Alhalin shi mai yin Gorin Ko Tarbiyantar da yayan Nashi Baya yi .

Ana Son Al'umma ta kasance Mai Lissafi .
Dabbobi ne Aka Sani Masu Maida Hankali da Abu 2 Wato Cin Abinci da Jima'i ,Mutane kuwa Bacin Abu 2 Nan Ana Son ta Kasanci Mai Nazari na Daban da Wasu Kokarin Cika Muradanta na Gaba wanda Zasu Amfani Yayanta da Jikokinta.

Allah yasa Mudace .

Photos from Hausa Light's post 05/12/2023

JIBWIS tayi Allah wadai ta kisan gungun musulmai a kaduna

Kungiyar wa’azin musulunci ta Izala tayi Allah wadai da kisan kiyashi na harin wani jirgin sama da aka yiwa al’ummar musulmai a jahar kaduna yayin da suke gudanar da wani taro.

Shugaban kungiyar Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, yayi kira ga gwamnantin tarayya da tayi bincike na gaskiya Akan hakikanin abun da ya faru, kuma ta hukunta masu hannu a cikin wannan lamari.

Lamarin de ya faru ne a kauyen Tudun Biri da ke gundumar Afaka a lardin Rigasa a karamar hukumar Igabi, inda aka yi kuskuren kashe musulman da suke gudanar da wani taro tare da jikkata wasu da dama biyo bayan wani hari da jirgin yaki mara matuki na soja ya kai don farautan ‘yan ta’ada.

Sheikh Bala Lau yayi jimami kwarai, ganin yadda daruruwan mutane s**a rasa ransu a wannan lamari. A karshe yayi addu’ar Allah ya Jikan musulmai muminai, ya baiwa wadanda s**a ji rauni lafiya, ya kuma kiyaye faruwar haka a gaba.

JIBWIS NIGERIA

02/12/2023

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un ,Wani Bawon Allah Mai Sana'ar Driver , Sulaiman Muhammad Funtua Gangaran Tasaulawa Yana Neman Taimako a Dalilin Accident , Har Yayi Mummunan Karaya a Kafa da Hannu Wanda ya Kaiga Anyi Mashi Aiki a Kano Amma Rashin Kudin da Za'aci Gabada Kulawa Da Lafiyarsa Har Karfen dake Jikinsa Ya Fito Waje Kuma Wurin Yanata Ruwa .
Ga Yara Kananu 3 Maza ,Ga Macce 1 Wadda An Sanya Mata Rana Amma Babu Halin Abunda Za'a Aurar da Ita .

Ga Numbershi Nan Ga Mutanan da Allah ya Basu Damar Taimakonsa.

Account=2318512019 UBA,Fiddausi Sulaiman .
Phone Number=09060184609.

Pls Share

Salees Ridwan Baballo 📝

Photos from Hausa Light's post 29/11/2023

Ana zargin mazauna Unguwar Kurna sun rufe titin Kurna Rijiyar Lemo ba shiga ba fita, bisa zargin wani Dan sanda da harbin wani matashi, da wasu mutane biyu, ƙarin bayani na nan tafe.

Freedom Radio Nigeria

Photos from Hausa Light's post 29/11/2023

BABBAN LABARI

Masarautar Katsina ta Sallami Magajin garin Funtua Alh Rabiu Aliyu Nuhu, Sanarwar na zuwa ne a wata takarda da masarautar ta fitar ranar litinin 27-11-2023 Mai dauke da Sanya hannun Sarkin yakin katsina Alh Bello M. IFO.

Funtua Online Tv.

28/11/2023

Ku daina alfahari da ni'ima a gaban wanda ya rasa ta.
Ku daina nuna alfahari da ƴaƴanku a gaban wanda Allah Ya jarabta da rashin haihuwa.
Ku daina alfahari da dukiya a gaban wanda Allah Ya jarabta da talauci.
Ku daina alfahari da lafiya a gaban wanda Allah Ya jarabta da ciwo.
Ku daina alfahari da aure a gaban wanda ya rasa halin yi.
Ku daina alfahari da ni'ima a gaban wanda ya rasa ta, saboda kuna sosa masa zuciya, kuna fama masa ciwon damuwar rashi da yake ciki, idan damuwar ta bayyana a fuska ko a harshensa ku zarge shi da hassada.
Kana da ƴancin bayyana farin cikinka, amma ka kiyaye kada ya yi sababin damuwar wani.

Isa Sadi

25/11/2023

Jami'ar Kimiyya ta Birnin Funtua Wadda Aka Samar .

Alhamdulillah,

An karbi General Hospital Funtua a matsayin sabuwar Asibitin Koyarwa ta Jami'ar Lafiya Funtua wanda za'ai Upgrading.

Alhaji Abubakar Ibrahim Nabature Fta.

23/11/2023

Kome ke Kawo Tangardar Shigar Katin Waya Musamman Wanda Ya Shafi MTN ?
Mutane da Dama Suna Korafin Shigarsa a Safiyar yau .

21/11/2023

Akwai hikima ta ubangiji anan

A daidai gadar Ƙofar Ruwa, wani mutum da ya goyi wasu ƴan makaranta na tafiya a kan mashin, kuɗin sa ya faɗo daga aljihunsa. Bai san kuɗin sa ya zube ba, ya cigaba da tafiyarsa.

Wani mutum da ke biye da shi a baya shi ma akan mashin, ya ga sanda kuɗin su ka faɗo ƴan dubu-dubu. Bai yiwa mutumin magana ba don ya tsaya ya kwashe kuɗin sa.

Cikin sauri, ya yi fakin, ya fara bi ya na tsintar kuɗin. Ana haka sai wani matashi ya ƙaraso wajen. Da ya ga kuɗi a ƙasa, sai shi ma ya fara bi ya na tsinta.

Mutum na farko da ya kammala tsinta, sai ya yi sauri ya hau mashin ɗin sa ya tafi cikin hanzari. A daidai lokacin da ya miƙe, wayar sa ta faɗo bai sani ba.

Matashin da ya zo a bayan sa ya ga sanda wayar ta faɗo. Ya yiwa mutumin magana amma mutumin ya ƙi kula shi. A zaton sa ko kuɗin hannun sa matashin zai nema. Haka ya fisgi mashin ɗin sa a guje ya yi gaba.

Matashi ya ƙarasa ya ɗauki wayar. Ya goge ta. Ya sa a aljihunsa. Ya koma wajen mashin ɗin sa. Ya tashe shi. Ya hau. Ya sa giya. Zai fara tafiya kenan, sai ya ga wani mutum ya biyo one-way ya na dube-dube.

Mutumin ya kalli matashin. Ya ce don Allah ba ka tsinci kuɗi ba? Matashin ya ce ya tsinta. Ya ɗauko kuɗi kusan dubu tara ya ba mutumin. Sannan ya ciro wayar da wancan mutumin ya yar, ya danƙawa wanda ya yar da kuɗin.

Matashi ya ce masa wannan wayar ka riƙe ta. Wanda ya yar da ita shi ne ya tsinci ragowar kuɗin ka. Na tarar da shi ya na tsinta. In ya kira wayar, sai ka faɗa masa kai ne ka yar da kuɗin da ya tsinta. Ya dawo ma ka da kuɗin ka, ya karɓi wayar sa. In ya ƙi, sai ka san yadda za yi da wayar.

Mutumin ya yiwa matashi godiya sosai. S**a yi sallama.

Allah ka sa mana tsoron ka a ko wane hali.


Badamasi Aliyu

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Abuja