Ammar isah hassan

Ammar isah hassan

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Ammar isah hassan, Health/Beauty, Darki, Abuja.

08/10/2025

Mujallar Bloomberg ta ce ɗan wasan na Portugal da Al-Nassr yana da hannun jari da kwantiragin da darajarsu ta kai dala biliyan $1.4.

Cristiano Ronaldo ya samu albashi na sama da dala miliyan 550m tsakanin 2002 zuwa 2023, inda ya buga wa ƙungiyoyi kamar Real Madrid da Man Utd.

16/09/2025

Baba Buhari Allah Ya Haskaka Makwanci🙏
Yasa aljannace makomah🤲🏾

Ammar isah hassan

16/09/2025

😳⚡ Fermín López ya karya dokokin kimiyya da lissafi!
Bugun sa mai ƙarfi kamar walƙiya ya shiga raga, har ya bar kowa a shiru — kwallo mai ban mamaki wanda har masana kimiyya ba za su iya bayanin yadda ta shiga ba. 🤯🔥

Dukkan filin wasa ya tashi tsaye suna tafa masa hannu, har Hansi Flick kansa ya tsaya a wuri, shiru saboda ƙwarewar wannan matashin tauraron Barça. 👏💙❤️

Wannan shi ne ainihin ruhin La Masia: ƙwarewa, sadaukarwa, da ƙaunar ƙungiya! 💪
Ammar isah hassan

28/08/2025

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya faɗi hakan ga magoya bayan jamʼiyyar ADC ya ce dawowarsa harkar siyasa kwanan nan "ba don neman muƙami ba ne".

Ƙarin bayani - https://bbc.in/4lNv7M0

Gwamnatin Tinubu: "Mun ba Arewa fiye da rabin kasafin ayyuka na 2024 da 2025" 07/08/2025

Gwamnatin Tinubu: "Mun ba Arewa fiye da rabin kasafin ayyuka na 2024 da 2025" A labarin nan, za a ji yadda gwamnatin tarayya ta tsaya kai da fata wajen cewa tana zuba ayyuka a Arewa kamar yadda ta ke yi a sauran sassan kasa.

Photos from Ammar isah hassan's post 07/08/2025

Innalillahi Allah Ya Jikan Sadiq Gentle . Ya Kasance Abokina Munyi Karatu Dashi 11Yrs Back, Tare Aketa Gwagwarmayar Siyasa. Muna Kwankwssiyya Tare Aka Raba tafiya Mukayi Gandujiyya Ya Tsaya A Kwankwssiyya. Gashi Yan Kwacen Waya Sun Hallakashi. Kuma Wallahi Sadiq Mutumin Kirki ne Sosai 😭😭😭LabaraiLegit.ngBBC NewsKwankwasiyya Reporters

07/08/2025

'Ba za mu lamunci ɗabi'ar da za ta taɓa ƙimar gwamnatinmu ba'BBC HausaLegit.ng HausaKwankwasiyya Reporters

18/07/2025

Peter Obi ya ce tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari ya h**e shi da riƙe amanar talakawan ƙasar.

Ƙarin bayani - https://bbc.in/4kMUWeG

18/07/2025

Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya fara samar da magungunan ƙwaya a kamfanin sarrafa magunguna na jihar JIPHARMA wanda yake mallakin jihar.

Babban Manajan Kamfanin, Nasiru Alhassan ne ya bayyana haka a ranar Alhamis a garin Dutse, babban birnin jihar, yayin da yake bitar ayyukan kamfanin na tsawon shekara biyu na gwamnatin Gwamna Umar Namadi.

Alhassan ya ce “kamfanin ya shirya fara samar da muhimman magunguna kamar su Vitamin C, paracetamol, da kuma magungunan ruwa (syrups), wanda hakan zai zama babban ci gaba a fannin kiwon lafiya na jihar.”

Photos from Ammar isah hassan's post 18/07/2025

Tinubu Zai Je Kano Domin Ta'aziyyar Ɗantata Wannan Juma'a

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai ziyarci Kano a wannan Juma'ar domin gudanar da ta'aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, ɗaya daga cikin dattawan Arewa da ake girmamawa a faɗin Nijeriya.

Kakakin Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, wato Sunusi Bature Dawakin Tofa, shi ne ya bada sanarwar.

Idan kun tuna, Ɗantata ya rasu ne mako biyu da s**a wuce yana da shekaru 93.

Kafin rasuwar sa, Ɗantata mutum ne da ya taka muhimmiyar rawa a tarihin ƙasar nan inda ya kasance mai zuba jari a harkoki daban-daban, kuma mai taimakon al'umma.

Ana sa ran cewa a lokacin ziyarar tasa, Shugaban Ƙasa zai gana da iyalan mamacin, sannan zai kai ziyarar ta'aziyya ga shugabannin jama'a da na addini.

A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya bayyana jin daɗi matuƙa da wannan mataki da Shugaban Ƙasa ya ɗauka.

Ya bayyana ziyarar da cewa "wata ƙwaƙƙwarar alama ce da ke nuna haɗin kan ƙasa da yin jimami ciki tare,” musamman a wannan lokaci da jihar da kuma ƙasar duka suke neman tsare mutunci, ɗa'a, da kyautatawa.

Ya ce: “Wannan wani lokaci ne na yin zurfin tunani tare da girmama ƙasar nan.

“Ina kira ga dukkan mazauna Kano da su yi wa Shugaban Ƙasa kyakkyawar tarba kuma a tsanake a lokacin da muke jimamin rashin ɗaya daga cikin dattawan ƙasar nan da ake girmamawa."

Gwamna Yusuf ya ce rasuwar Alhaji Ɗantata ba kawai babban rashi ga Kano ko Arewa ba ne, har ma ga dukkan ƙasar nan domin ayyukan da ya yi za su ci gaba da yin tasiri a rayuwar jama'a ta hanyar taimakon al'umma, taimaka wa kasuwanci, da ɗimbin sadaukarwa ga cigaban ƙasa.

Gwamnan ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar ta ɗauki dukkan matakan da s**a kamata don tabbatar da an yi ziyarar Shugaban Ƙasar ta hanyar lumana da kwanciyar hankali.

“Mun yi aiki tare da hukumomin tsaro das**a dace da kuma masu ruwa da tsaki a al'umma don tabbatar da cewa an aiki tare a duk tsawon lokacin da Shugaban Ƙasa zai zauna,” inji sanarwar.

Ana sa ran ɗimbin jama'a za su fito domin yi wa Shugaban Ƙasa kyakkyawar tarba.

22/12/2024

Putin ya sha alwashin ƙara ruguza Ukraine

Karin bayani - https://bbc.in/405N9By

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Darki
Abuja