So da kauna
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from So da kauna, Health/Beauty, Abuja.
23/05/2026
Zaid ibn Harithah (Radiyallahu Anhu) shi ne sahabi guda daya tilo da aka ambaci sunansa sarai a cikin Alkur'ani.
Shi ne wanda Annabi Muhammad ﷺ ya nuna wa tsananin soyayya har ta kai ana yi masa lakabi da:
“Hibbu Rasoolillah ﷺ” – wato wanda Manzon Allah ﷺ yake so da kauna.
Mahaifiyarsa sunanta Su’da bint Tha’labah.
Wata rana, ta yanki shawarar tafiya ziyara zuwa gidan iyayenta, sai ta tafi da danta Zaid yana karami.
A kan hanyarsu ta tafiya, sai wasu 'yan fashi s**a far wa ayarin ababen tafiyarsu.
S**a kwashe dukiyoyinsu, sannan s**a kwashe yaran da ke tare da su s**a sayar da su a matsayin bayi.
A lokacin, Zaid ibn Harithah yana da kimanin shekaru takwas kacal a duniya.
SubhanAllah.
Haka aka raba wannan yaro karami da iyalinsa, aka rika sayar da shi a kasuwannin bayi.
Wanda ya saye shi shi ne Hakim ibn Hizam, kani ga Khadijah bint Khuwaylid (Radiyallahu Anha).
Hakim ya kawo wasu bayi da ma'aikata gaban gwannonsa Khadijah ya ce mata:
“Gwannona, ki zabi wanda k**e so a cikinsu a matsayin kyauta.”
Sai ta zabi Zaid ibn Harithah.
Ya kasance yaro mai duhun fata, gajere, mai kuzarin jiki, kuma mai dabi'ar kunya.
Daga baya, lokacin da Sayyidatuna Khadijah (R.A) ta auri Muhammad ﷺ, sai ta ba shi Zaid a matsayin kyautar bawan da zai rika taya shi aiki.
Kuma tun daga ranar, ba su sake rabuwa ba.
HADUWAR ZAID DA MAHAIFINSA
A gefe guda kuma, mahaifin Zaid, wato Harithah, ya shafe shekaru yana ta fadi-tashi da neman dansa cikin tsananin damuwa. Shekaru s**a shude.
Wata rana, wasu mutane daga cikin kabilarsu sun zo Makka domin yin aikin hajji (al'adar dãuri).
Suna cikin yin dawafi a kewayen Ka’aba, sai s**a yi tozali da Zaid ibn Harithah.
Ya gane su, su ma s**a gane shi.
S**a tambaye shi:
“Me ya faru da kai?”
Sai Zaid ya kwashe daukacin labarin ya gaya musu.
Mutanen nan s**a koma gida, s**a sanar da mahaifinsa.
Nan take Harithah ya kwashe duk abin da yake da shi na dukiya, ya dauki wani dan nasa guda daya, s**a garzaya zuwa Makka.
A karshe, s**a isa gidan Muhammad ibn Abdullah ﷺ – kuma wannan ya faru ne kafin a ba shi annabta.
S**a ce masa:
“Ya Muhammad, mun zo ne domin neman danmu.
Muna shirye mu biya dukkan kudaden da kake bukata.
Don Allah ka mayar mana da shi.”
SubhanAllah.
Kalli amsar da Muhammad ﷺ ya ba su ko da yake kafin saukar wahayi ne:
“Zan mayar muku da shi ba tare da na karbi ko kwandala ba.
Amma da farko bari mu tambaye shi me yake so.
Idan ya zabi ya tafi da ku, to ya tafi.
Amma idan ya zabi ya zauna da ni, to dole ku bar shi ya zauna.”
S**a kira Zaid ibn Harithah.
Ya cika da farin ciki lokacin da ya ga mahaifinsa da dan uwansa.
Sai s**a ce masa:
“Ya Zaid, mun zo ne domin mu mayar da kai gida.”
Amma sai Zaid ya ba kowa mamaki.
Ya amsa da cewa:
“Ba zan tafi da ku ba.”
Mahaifinsa ya kasa daurewa cikin bacin rai ya ce:
“Ya Zaid, zaka zabi bauta akan 'yanci?
Mun zo ne fa domin mu cece ka!”
Sai Zaid ibn Harithah ya amsa:
“Wallahi, da kun san wannan mutumin da kuma irin soyayyar da ke tsakaninmu, da kun fahimci zabina.
Akwai daukaka da alheri a wurina idan ina tare da shi fiye da ko'ina.”
SAUYIN SUNA DA HUKUMCIN MUSULUNCI
SubhanAllah.
Wadannan kalmomi sun ratsa zuciyar Muhammad ﷺ sosai.
Nan take ya k**a hannun Zaid, ya fitar da shi zuwa gaban Ka’aba, ya sanar a bayyane a gaban Quraishawa:
“Ku shaida cewa Zaid dana ne.
Shi 'yantacce ne, kuma zai gade ni, ni ma in gade shi.”
Tun daga ranar, mutane s**a fara kiran shi da sunan:
“Zaid ibn Muhammad.”
Amma daga baya, Allah (Subhanahu wa Ta’ala) Ya saukar da ayoyin Alkur'ani wadanda s**a bayyana hukuncin rikon uba (adoption).
Allah Ya yi umarni da cewa:
“Ku kira su da sunayen ubanninsu; hakan shi ne mafi adalci a wurin Allah.” [33:5]
Bayan haka, sai sunansa ya koma yadda yake da can, wato: Zaid ibn Harithah (Radiyallahu Anhu).
A wani lokaci, Allah Ya umarci Muhammad ﷺ da ya shawarci Zaid ibn Harithah ya auri Zaynab bint Jahsh (R.A).
Zaid ya aure ta, amma daga baya auren bai dore ba, sai s**a rabu (s**a yi saki).
Bayan haka, Allah Ya umarci Annabi ﷺ da kansa da ya auri Zaynab bint Jahsh (R.A).
Wannan auren yana dauke da wata babbar hikima ta shari'a:
Ya bayyana karara cewa 'ya'yan riko ba duba daya suke da 'ya'yan jini ba a cikin hukunce-hukuncen Musulunci (k**ar haramcin auren matar da da ya bãta).
JARUNTAKARSA DA SHAHADA
Annabi ﷺ ya kasance yana matukar kaunar Zaid.
Duk lokacin da ya hango shi yana nufo shi daga nesa, yakan tashi tsaye, ya ruga da gudu zuwa gare shi, ya rungume shi sosai, sannan ya yi masa fuskarsa sumbata.
Lokacin da Annabi ﷺ ya tafi garin Ta'if domin yin da'awa, Zaid ibn Harithah ne kadai mutumin da ya raka shi.
Sa'ar da mutanen Ta'if s**a rika jifan Annabi ﷺ da duwatsu, Zaid ya rika amfani da jikinsa a matsayin garkuwa domin kare Manzon Allah ﷺ, inda duwatsun s**a rika samun sa shi maimakon Annabi ﷺ.
Daga baya ya zama daya daga cikin manyan kwamandojin yaki na Musulunci.
A Yakin Mu’tah, Annabi ﷺ ya nada Zaid ibn Harithah a matsayin babban kwamandan rundunar yaki ta Musulmai.
A can ne, a shekara ta 8 bayan Hijira, Zaid ibn Harithah (Radiyallahu Anhu) ya yi shahada yana kare addinin Allah.
A yau, kabarinsa yana kasar Jordan.
Wannan shi ne Zaid ibn Harithah (R.A) – wanda Manzon Allah ﷺ ya fi kauna.
23/05/2026
ƘISSAR HARUTA DA MARUTA
Asalin tsafi.
Daga Shafin Bashir Halilu.
Acikin Alkur'ani mai girma, Allah Maɗaukakin Sarki Ya ambaci sunayen Haruta da Maruta sau ɗaya, acikin Suratul Baƙarah.
Ruwayoyi da dama sun zo akan Ƙissar waɗannan sunaye na Mala'iku ko kuma Sarakuna amma dai za mu ɗauki jigon ruwayar da Imamu Ahmad ya fitar acikin Musnad, da kuma ibnu Hibban acikin Sahihinsa daga ibn Umar رضي الله عنهما
sai mu shigar da bayanin sauran ruwayoyin a ciki.
GA CIKAKKIYAR ƘISSAR
Lokacin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya saukar da Annabi Adam ﻋﻠﻴﻪ السلام
daga Aljanna zuwa kasan duniya, sai Mala'iku s**a dinga cewa "Ya Ubangiji, yanzu ka sanya wadanda za su yi ɓarna, su dinga zubar da jinin junansu a duniya?!, alhali mu muna girmamaKa tare da gode maKa kuma muna kaskantar da kai gareKa?".
Sai Allah Madaukakin Sarki Ya ce "Ni Na san abinda baku sani ba".
Sai su ka ce "Ya Ubangiji, mu fa mun fi yi ma Ka biyayya sama da 'yan Adam, inda mu ne ka saukar da mu duniya to ba za mu saɓa ma Ka ba".
Sai Allah Mai girma Ya ce musu "To ku kawo Mala'iku guda biyu a cikinku, sai Mu saukar da su kasan duniya, don Mu ga yadda za su yi. (za suy biyayya ko ba za suy ba?!)".
Sai su ka ce "Ya Ubangiji, Ga Haruta da Maruta mun za6e su a kaisu"
Sai aka saukar da wadannan Mala'iku biyu zuwa duniya, aka sauke su a garin Babiyla.
Lokacin da aka sauke su sai aka ce musu ga Tsafi nan ku dinga koyawa mutane amma duk wanda ya zo zai koya ku gaya masa in ya aikata ya zama kafuri.
A wata ruwayar kuma an ba su Sihiri ne domin su dinga yiwa mutane gargadi akan su guje shi kada su aikata shi.
To bayan an saukar da su, sai Allah Ya mayar da Zahr', wato wannan babbar tauraruwar da muke gani a kusa da wata, sai aka mayar da ita siffar mace.
Sai ta zo wajensu a sura kyakkyawa.
Da su ka ganta sai su ka nemeta. Sai ta qi amincewa, ta ce musu "Saidai in za ku kafurta to zan yarda da ku".
Da su ka ji haka sai su ka ce basu yarda ba.
Sai ta fi, ta sake dawowa da wani jariri a hannunta.
Sai su ka kuma nemarta. Sai ta qi amincewa, ta ce "Saidai in za ku kashe wanan yaron, to zan ba ku hadin kai".
Sai su ka ce basu yarda ba. Sai ta tafi, ta sake dawowa da tukunyar giya a hannunta.
S**a nemeta. Sai ta ce bata yarda ba sedai in za su sha giya tukuna. Sai su ka yarda su ka sha giyar.
Bayan sun sha sai maye ya k**a su, su kay zina da wannan matar sannan kuma s**a kashe wannan jaririn.
Lokacin da s**a farka sai Allah Ya tambayesu alqawarin da s**ay akan ba za su sa6a masa ba.
Daga nan sai aka ba su za6i akan su za6i irin azabar da za ay musu. Shin a duniya suke so ay musu azaba ko kuma a bari sai an je Lahira?!.
Sai s**a ce ai azabar Lahira bata karewa, mun za6i ta duniya.
Shikenan sai aka kai daya inda rana take 6ullowa. Kullum idan rana ta 6ullo sai ta tafasa masa kansa dayan kuma sai aka kai shi inda rana take faduwa, kullum in rana zata fadi sai ta kona shi.
Ita kuma Zahra' sai aka mayar da ita tauraruwa ta koma sama.
To a lokacin ne aka ba su sihiri, (bisa sa6anin ruwaya).
Sai aka ce duk wanda ya zo yana so su koya, to su koya masa.
Sai s**a dinga koyawa mutane da Aljanu yadda ake raba tsakanin miji da mata amma basa koyawa kowa sai sun ce masa "Tabbas mu fitina ne!, don haka kada ka kafurta".
Ma'ana duk wanda ya koyi sihiri a wajensu to ya zama Kafiri.
In Mutum ko Aljan ya yarda zai kafurta sai su koya masa.
Daga nan sai harkar Sihiri da Tsafi su ka yadu a tsakanin mutane da Aljanu.
Malamai sun yi raddi sosai akan wannan qissa musamman kasancewar Mala'iku basa sa6o da kuma maganar cewa su ne s**a koyar da tsafi sannan ruwayoyin yawanci Isra'iyliyyat ne, ma'ana daga wajen Yahudawa aka samo su, sedai abinda aka samu na ɓangarorin ƙissar daga Alqur'ani da kuma ruwayar ibnu Umar daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
k**ar yadda muka ambata.
Harkar Bokanci, Sihiri, Tsafi, Surkulle, Rufa-ido, Tsibbace-tsibbace da mak**antansu, sun samu shahara sosai da karɓuwa a wajejen aiko Annabi Sulaiman عليه السلام
shi yasa ya zamto yana daga cikin manyan abubuwan da Annabi Sulaiman عليه السلام yay fada da su kuma ya yaqi masu aikata shi.
Sannan wannan harka ta samu kar6uwa ne da matsayi da shiga zukatan al'umma a wajejen zamanin Annabi Musa عليه السلام،
inda a lokacin ake ganin wanda ya iya sihiri tamkar wani shugaba kuma wani abin ay wa biyayya sannan abin tsoro.
A baya, mun kawo cikakkiyar ƙissar yadda Annabi Sulaiman عليه السلام ya yaƙi masihirtan zamaninsa da kuma dalilin da yasa bayan ya yi wafati Shaidanu s**a ce ya mulki duniya ne ta hanyar tsafi.
Sannan mun sake duba ƙissar Haruta da Maruta tare da bayanin yadda Annabi Musa ya fuskanci matsafan zamaninsa.
Duk wannan ya zo a cikin posting din mu mai taken "ƘISSAR ANNABI SULAIMAN (A.S)",
Domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada acikin Suratuz Zariyati cewa:
* ﻛَﺬَﻟِﻚَ ﻣَﺎ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻣِﻦْ ﺭَﺳُﻮﻝٍ ﺇِﻻَّ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺳَﺎﺣِﺮٌ ﺃَﻭْ ﻣَﺠْﻨُﻮﻥٌ [ ﺍﻟﺬﺭﻳﺎﺕ :50 - 52] .
Ma'ana: "Kamar haka ne (Su wadannan mutanen) babu wani Annabi da ya zo wajen wadanda s**a gabace su face sai sun ce masa mai Sihiri ko kuma mai hauka".
Wannan ayah tana nuna cewa tun zamanin Annabi Nuhu ﻋﻠيﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
duk da cewa shi ne farkon Manzanni, duk Annabin da Allah Ya aiko sai Kafurai sun ce masa mai sihiri ne. Kenan tun a lokacin ana yin sihiri.
Wasu Malaman kuma suna ganin sihiri ya samo asali ne daga hannun Aljanu kuma dalilansu sun fi karfi gaskiya.
Duk mun kawo cikakken bayani a cikin " ƘISSAR ANNABI SULAIMAN (AS)", Mai son karantawa zai iya dubawa cikin wannan shafin na mu.
Daga shafin Bashir Halilu mai Ruƙ'yah da bayar da magunguna na Musulunci da na gargajiya. Lambar waya 08134434846.
23/05/2026
LOKACIN DA NANA FAƊIMATU YAR MANZON ALLAH ﷺ TA RASU.. SAYYADINA ALIYU YACE KU TAIMAKAMIN KUƊAUKETA😭😭😭...
Ya Kasance Zaki A Fagen Daga… Mutum Mai Ƙarfin Hali Da Jarumtaka Marar Misaltuwa. Aliyu Ibn Abi Ɗalib رضي الله عنه Wanda Yana Iya Ɗaga Manya Manyan Ƙofofi Alokacin Dayake Azumi Wanda Nauyinsu Yakai 900kg, Yakuma Kayar Da Maƙiya, Kuma Ya Tsaya Tsayin Daka Domin Addinin Musulunci.🥹
Amma Lokacin Da Matarsa Abar Ƙaunar, Fatimah Bint Muhammad رضي الله عنها, Ta Rasu… Sai Yace... “Ku Taimaka Mini Ɗaukar Ku Ɗauketa.”😭
Domin Ƙarfin Gaskiya Ba Kawai A Cikin Hannuwanka Ko Ƙwanji Yake Ba… Yana Cikin Zuciyarka Ne. Musulunci Bai Koya Mana Mu Zama Marasa Tausayi Ba. Yana Koya Mana Mu Kasance Masu Ƙarfi, Amma Masu Taushin Zuciya. Jarumai, Amma Masu Nuna Soyayya. Masu Iko, Amma Masu Tawali’u.🥲
Hatta Mafiya Ƙarfi Daga Cikin Sahabban Annabi Muhammad ﷺ Sunji Baƙin Ciki, Soyayya, Da Raɗaɗi. Saboda Haka Kada Ka Ɗauki Shiru A Matsayin Ƙarfi… Kuma Kada Ka Ɗauki Hawaye A Matsayin Rauni.😭
Muna Roƙon Allah Yabamu Zukata Irin Tasu Masu Ƙarfi Cikin Imani, Masu Taushi Cikin Soyayya, Kuma Masu Haƙuri A Cikin Jarabawa. Ameen 🤍😥😢
YARON KIRKI
22/05/2026
YA MANZON ALLAH ﷺ YUNWA NAKEJI, SANNAN KUMA BANI DA LAFIYA😭😭😭...
An Ruwaito Nana Fāɗimah (رضي الله عنها) Tana Rashin Lafiya.
Kamar Yanda Kuka Sani, Itace Shugabar Matan Aljanna. Kuma Ƴaƴanta, Hasan Ibn Ali Da Husayn Ibn Ali (رضي الله عنهما), Sune Shugabannin Samarin Aljanna.
Lokacin Da Annabi ﷺ Ya Samu Labarin Rashin Lafiyarta, Sai Yaje Domin Ya Duba Ta. Tare Da Shi Akwai Sahabi Imran Ibn Husayn (رضي الله عنه). Sai Annabi ﷺ Ya Ƙwanƙwasa Ƙofa Yace.. Yata, Zan Iya Shiga? Imran Yana Tare Dani.
Sai Ta Amsa... Ya Manzon Allah ﷺ… Bani Da Babban Mayafi A Gidana Wanda Zan Iya Yin Cikakken Hijabi Dashi.
Wacece Ita? 😭 Shugabar Matan Aljanna. 😭 Ƴa Ɗaya Tilo Mafi Soyuwa Ga Annabi Muhammad ﷺ. 💔
Sai Annabi ﷺ Yabada Mayafinsa Aka Shiga Dashi Ciki. Ta Rufe Jikinta Dashi. Sannan Ya Shiga ﷺ Ya Tambaye Ta Halin Da Take Ciki, Cikin Yanayin Raunin Jinya… Ta Fara Kuka.
Ta Ɗora Kantā A Kan Ƙirjin Annabi ﷺ Mai Albarka Sannan Tace.. Ya Manzon Allah… Ina Jin Yunwa… Kuma Ga Rashin Lafiya.😭😭
Sai Annabi ﷺ Ya Fashe Da Kuka... Domin Ciwon Ƴaƴa… Iyaye Ne Kaɗai Suke Fahimtarsa Da Gaske. Yana Rungume Da Ita, Sai Yace ﷺ..
“Yake Abar Ƙaunata… Kada Kiyi Baƙin Ciki. Na Rantse Da Wanda Raina Yake A Hannunsa… Kwana Uku Sun Wuce, Ni Ma Banci Ko Dabino Ba.😭😭💔
💔 Wannan Ce Rayuwarsu… Ba Jin Daɗin Duniya Ba… Ba Wadatar Duniya Ba… Sai Haƙuri. Sai Soyayya. Sai Alaƙa Da Allah Fiye Da Yadda Zamu Iya Tunani.
YARON KIRKI
22/05/2026
💭 WASU ZUNUBAN… SUJUDAR DARE CE MAGANINSU.
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum (Hafizahullah) yace:
In mutum na qiyamul laili…
Ko appointment s**a hada da karuwa…
Yana da wahala ya iya zuwa.
Saboda me?
Domin qiyamul laili tana raya zuciya.
Idan mutum yana tashi da dare yana tsayawa a gaban Allah…
yana rokon gafara…
yana sujada cikin dare…
to zuciyarsa zata fara jin tsoron Allah.
Idan zai aikata laifi…
ko a office ne…
ko a gida ne…
ko shi kadai ne…
Sai hankalinsa ya tashi.
Sai ya shiga firgici da damuwa.
Sai zuciyarsa ta kasa nutsuwa da sabon.
Karshe… sai ya fara kaucewa laifin saboda Allah.
Annabi ﷺ yace:
Qiyamul laili tana taka birki wa mutane daga saba ma Allah.
Idan kanaso kayiwa kanka turke daga zunubi…
to ka rike sallah.
Domin Allah Yace:
Lallai sallah tana hana alfasha da munkari.
Amma qiyamul laili…
Tana da wani sirri na musamman.
Tana hana mutum sabawa Allah
Shi yasa Annabi ﷺ yace:
Ku rike qiyamul laili…
Sannan Annabi ﷺ ya bayyana falalarta:
Abu na farko: Qiyamul laili al’adar salihai ce.
Abu na biyu: Tana samarwa mutum kusanci da Allah.
Abu na uku: Tana kankare zunubai.
Abu na hudu: Tana hana saba ma Allah.
Allahu Akbar…
💭 Dan uwa…
Ka taba gwada tashi cikin dare…
ka yi raka’a biyu saboda Allah kadai?
Wallahi akwai wani haske da nutsuwa da Allah ke
sanyawa a zuciyar mai qiyamul laili da ba
kowanne mutum ke fahimta ba.
Wasu matsalolin rayuwa…
ba yawan magana ke magancesu ba.
Sujudar dare ce maganinsu.
Wasu zunuban…
ba karfin mutum ke hanasu ba.
Qiyamul laili ce ke kashe sha’awarsu daga zuciya.
🤲 Ka fara ko da raka’a biyu ne.
🤲 Ka tashi ko minti goma ne kafin asuba.
🤲 Ka sabawa kanka saboda Allah.
Wata kila…
wannan sallar dare ce zata zama sanadin tsirarka a Lahira.
🤲 Ya Allah…
Ka sanya mu cikin masu qiyamul laili.
Ka raya zukatanmu da ibada.
Ka nisantar damu daga alfasha da munkari.
Ameen Ya Rabbal Alameen.
Addinu Annasiha
22/05/2026
Wannan shi ne wajen gonar Manzon Allah ﷺ inda aka ce ya shuka dabino da hannunsa mai albarka. Ana cewa wannan ruwa ne ke ban ruwa ga dabinon tun daga wancan lokaci har zuwa yau.
Abin mamaki shi ne, ruwan na fitowa ne daga cikin dutse cikin tsabta da kyau, ba tare da datti ko canjin launi ba.
Hakika al’amuran Manzon Allah ﷺ suna cike da darussa da albarka. Shekaru masu yawa bayan wafatinsa, har yanzu ana ganin alamomin ni’imar Allah a wuraren da s**a shafi rayuwarsa.
Duk wanda ya san darajar Annabi ﷺ zuciyarsa ba za ta gushe daga ƙaunarsa ba.
Allah Ya arzuta mu da ziyartar irin waɗannan wurare masu albarka, Ya kuma sa mu mutu a kan soyayya da bin tafarkin Muhammadu Rasulullah ﷺ.
Subscribe my account https://www.facebook.com/hlpgausicreatives/subscribenow
Idan ka/kinji dadi kayi sharing group 5 sabo da annabi s.a.w
22/05/2026
sanda yakwana a kogon Sauru.
kwanansa Huɗu a ciki fa, ba hutu ga zafin Rana, ga wahala ga kafirai suna nemansu.
sayyadina Abubakar ya gigice idon sa na zubar da hawaye, yana ce sun k**amu ya Rasulullah.
manzon Allah ya buɗe idon sa yace Abubakar me ya faru,yace ai an k**amu, Shugaba yace mai ya faru, Abubakar yace ka gansu nan da sun zuro hannunsu ma ƙeyata zasu k**a su jani mu tafi shikenan.
Anan shugaba yabudewa Sayyadina Abubakar wane shafi da yake nuna masa ashe ma baka san ina muka dosa ba.
sai shugaba yake cewa Haba Abubakar wa dannan ai angama Dasu, mune biyun nan fa da Allah ne na ukun mu.
Sayyiduna Abubakar sai yaga wabi abu da yabashi Mamaki, sai yaga kawai Shugaba ya koma ya kwanta, hawaye na zuba a idon Abubakar, Shikuwa Shugaba yana vewa dashi karka Damu ba komai.
Ga sufa suna kallansu amma saboda muradin....!
Daga nan Sayyiduna Abubakar ya gane bafa Ɓuya s**ayi ba, ba ɓuya bane, kawai sirrin Bauta ne ya shigar dasu nan.
salawatullahi wa Salamuhu Alaihi.
Malam Ibrahim Mai Ashapa
22/05/2026
HAJARUL ASWAD : Dutse ne daga cikin duwatsun gidan aljannah. Manzon Allah ﷺ yace lokacin da Mala'iku s**a kawoshi (dutse) fari ne sosai k**ar madara. Amma zunuban 'yan Adam ne ya mayar dashi ya zama baqi wuluk.
Kuma aranar Alqiyamah Allah zai sanya masa harshe yayi magana k**ar kowa, kuma zai bada shaida ne ga duk wadanda s**a ta'ba sumbartarsa, ko ta'bashi yayin dawafi ko nunashi.
Duk wanda ya ta'ba zuwa wannan waje, Ya Allah ka maimaita mana cikin Lutufinka da karamcinka da baiwarka.. wadanda kuma basu je ba, Ya Allah ka kawo musu hanyar zuwa cikin sauki...
22/05/2026
KOFAR MASALLACIN ANNABI S.A.W: Shin ka san cewa Masallacin Annabi ﷺ lokacin da aka fara gininsa a zamanin Annabi ﷺ yana da ƙofofi uku ne kawai?
1. Ƙofar kudu (ɓangaren tsohuwar alƙibla)
Wannan ƙofa tana buɗewa ne zuwa wajen Baitul muƙaddas amma bayan an sauya alƙibla zuwa Ka’abah mai girma, sai aka rufe ta.
2. Ƙofar Atikah (Ƙofar Rahama)
Tana a ɓangaren yamma, kuma an kira ta da sunan “Atikah” ne saboda wata mata daga Makkah da gidanta yake kusa da ƙofar. Haka kuma ana kiranta “Ƙofar Kasuwa” domin tana kaiwa zuwa kasuwa. Daga baya aka fi saninta da “Ƙofar Rahama” bayan wani lokaci da aka roƙi Annabi ﷺ ya yi addu’ar neman ruwa, sai ALLAH Ya saukar da rahama mai yawa.
3. Ƙofar Usman… (wacce yanzu ake kira Ƙofar Jibrilu)
An kira ta “Ƙofar Jibrilu” ne saboda wani babban lamari da ya faru a wajen, inda Annabi ﷺ ya haɗu da Mala’ika Jibrilu alaihis salamu
Bayan kammala Yaƙin Khandaq wato yaƙin (Ahzab), mala'ika Jibrilu ya zo wajen Annabi ﷺ a kan doki, yana umartarsa da ya fita zuwa Banu Qurayzah.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Abuja