Zauren Sunnah

Zauren Sunnah

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Zauren Sunnah, Health/Beauty, Bauchi.

17/12/2025

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Bello Umar Dan Awo, Mohammad Garba Ahmad MG

23/11/2024

Masha Allah ❤❤

26/05/2023

ZUWA JUMA'A DA WURI
•═════❀🏮❀═════•

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Wanda yayi wanka ranar Juma'a sannan ya tafi Masallaci a cikin sa'a ta farko, to kamar ya soke taguwa ne saboda Allah, wanda ya tafi a sa'a ta biyu, kamar ya ba da saniya ne, wanda ya tafi a sa'a ta uku kamar ya ba da rago ne, wanda ya tafi a sa'a ta hudu kamar ya ba da kaza ne, wanda ya tafi a sa'a ta biyar kamar ya ba da 'Kwai ne. Idan Liman ya fito, sai Mala'iku su zo suna sauraron zikiri(khudba). Bukhary da Muslim.

Telegram: Contact @Zaurensunnah 22/05/2023

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•✿.¸¸.•°˚˚°✿
⇣♥️⇣
┊┊⇣
┊⇣IDAN ALLAH YA SO BAWA




An ruwaito daga Abu Hurairah ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Lallai Allah idan ya so bawa sai ya kira Jibrilu ya ce masa: Lallai Ni ina son wane, kai ma ka so shi, ya ce: Sai Jibrilu ya so shi, Sai ya yi kira a sama ya ce: Lallai Allah yana son wane ku ma ku so shi, sai ma'abota sama su so shi, Ya ce: Sai a sanya mishi kar6uwa a kasa...." Muslim

Zaurensunnah

https://t.me/Zaurensunnah



‎ ♥️࿐❥ ✍🏻
•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

Telegram: Contact @Zaurensunnah

20/05/2023

FALALAR YIN MUSAFAHA YAYIN HADUWA

An ruwaito daga Baraa bn Aazib(RA) ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce: "Babu wasu musulmai da za su gamu, sai su yi musafaha face an gafarta musu tun kafin su rabu".

السلسلة الصحيحة 525

04/05/2023

TAFKIN MANZON ALLAH ﷺ.
✿❁࿐❁✿ 💦‏​✿❁࿐❁✿

DAN BIDIA BA ZAI SHA DAGA GARESHI BA!

Manzon Allah ﷺ ya ce: Alkauthar wani kogi ne wanda Ubangijina Madaukaki ya yi min alkawarinsa a Aljannah, yana da wani tafki da duka Al'umata za su gangara mata su sha ruwan da ke cikinta ranar Alkiyama, adadin abin sha/madebin da ke wajen adadin taurarin da ke sama, sai a dakatar da wasu mutane daga shan wannan ruwan, sai in ce: Yaa Ubangiji wannan ai suna cikin Al'umata, sai Allah ya ce: Ai ba ka san abin da al'umarka s**a kirkiro ba a bayanka". Muslim.

27/04/2023

Shaykh Ibn Al-Uthaimeen (Rh) ya ce: "Duk wanda ya ji tsoran Allah ya ke aikata abin da Allah ya umarce shi, kuma yake hanuwa daga abin da Allah ya haneshi, to Allah zai sanya masa mafita a cikin kowane qunci da yake ciki, kuma duk lokacin da wani abu ya quntatu a gareshi alhalin yana mai tsoran Allah(yana bin dokokin Allah) Allah zai sanya masa mafita, ko da kuwa quncin a cikin rayuwarsa ne, ko a cikin 'ya'yansa ne, ko a cikin dukiyarsa ne, idan dai ka zamto mai tsoran Allah, To babu shakka ka tabbata cewa: Allah zai sanya maka mafita a cikin kowane qunci.
شرح رياض الصالحين٥١٧/١

13/04/2023

SHIN KA SAN IRIN SOYAYYAR DA YAKE MAKA?

Shine zai zo a ranar Alkiyama, ranar da dan uwa yake gudun dan uwansa, ranar da daa yake gudun iyayensa, ranar da kowa yake ta kansa, bayan mutane sun gigita, sun dimauce, sun firgita sun fita hayyacinsu saboda tsananin tashin hankalin da ke a wannan rana, A na tsaka da wannan hali an rasa yanda za a yi, zai je ga Allah ya yi ceto mafi girma, bayan ya fadi yayi sujada da godiya a gaban Ubangijinmu, za a ce masa: Ya Muhammad d**o kanka, ka fada za a saurara, ka roka za a ba ka, ka yi ceto za a ba ka ceton, Sai ya ce: Yaa Ubangiji Al'umata, Al'umata...

Iyayena da kaina fansa gareKa Yaa Manzon Allah(SAW).

Ku yawaita Salati a gareshi, duk wanda yayi salati daya a gareshi Allah zai yi salati goma a gareshi🌹

13/04/2023

🌃LAILATUL QADRI🌃

"Manzon Allah ﷺ ya ce: "ku lalubi daren Lailatul qadri a kwanakin mara (Witri: 21,23,25,27,29) na goman karshen Ramadhan". Al-Bukhariy

"Manzon Allah ﷺ ya ce: "Wnda yayi tsayuwar daren Lailatul qadri yana mai imani kuma yana mai neman lada, to za a gafarta masa zunubansa na daga abin da ya gabata" Al-Bukhary

Allah Ka datar damu wannan dare mai albarka ka bamu ikon ribatarsa kuma ka karba mana.

13/04/2023

GOMAN K'ARSHE

Shin wane tanadi kake yi ma kanka a wadannan kwanaki??

Daga Ummuna Aisha Allah ya ƙara yarda a gare ta, ta ce: "Manzon Allah ﷺ ya kasance idan waɗannan goman s**a shigo, ya kan zage damtse (dagewa gurin ibada), ya raya darensa, kuma ya tayar da iyalensa" Bukhary da Muslim

Ku dage ku ribaci wadannan kwanaki ta hanyar:

●I'tikafi
●Yawaita Sadaka
●Raya dare/Qiyamullaili
●Karatun Alkur'ani
●Yawaita Addu'oi

Da sauran ayyukan da'a da Allah ya ke so...

Allah ya datar damu.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Bauchi?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address


Bauchi