Khadija Abdulmumeen
Without struggle no freedom
18/04/2024
SAƘON SOJIN AMURKA GA SHUGABA JOE BIDEN....
"Ina so nai amfani da wannan damar wurin kiran mai girma Shugaban ƙasar Amurka, ka fita daga sabgar I$ra'ila.
Mai girma shugaban ƙasa, ina sake amfani da wannan dama wurin kiran ka, kar ka bari Isra'ila ta jaka cikin yaƙin da ba namu ba, kar ka bari I$ra'ila ta sanya Amurka cikin wani yaƙi.
Amurka muna zaune cikin aminci, muna zaune cikin soyayya, mu Amurkawa muna zaune cikin farinciki, amma a yau duk mun rasa wannan saboda tsayawa I$ra'ila, mun rasa duk wani mutumcin mu, Amurka babbar ƙasa ce amma ta rasa ƙima saboda Isra'ila.
Mai girma shugaban ƙasa, karka sadaukar da mutanen Amurka zuwa wani yaƙin, karka sadaukar mana da Amurkawan mu zuwa wani yaƙi, I$ra'ila ita ta fara yaƙin, amma zan ja hankalin ka kar ka sadaukar da Sojojin mu zuwa yaƙi akan wata ƙauye I$ra'ila, ita ƙauye ce a idon Amurka da biranen ta, saboda haka karka sadaukar mana da Amurka akan watan ƴar buro uba I$ra'ila zuwa wani yaƙi.
A matsayina na wadda ya damu da AMURKA, bari na faɗa muku wani abu, Iran bata tsoron Amurka ko I$ra'ila, zan sake maimaita wannan kalmar, Iran bata tsoron Amurka ko I$ra'ila, Amurka ku faɗawa I$ra'ila ta dakatar da wannan shirman da take, duk wannan abubuwan da I$ra'ila keyi tana yine saboda tsayuwar Amurka (a bayanta), yanzu lokaci yayi da za'a san kuskure fa kuskure ne, shine abinda I$ra'ila take yi.
Mutane na, in I$ra'ila ta farmaki Iran, bari na faɗa muku wani abu, Iran zata shafe I$ra'ila ne daga doron ƙasa, a rana guda (Asabat ɗin da aka kai hare-hare Isra'ila), kun san makamai nawa ne s**a sauka a I$ra'ila?, Wannan ajiyayyen tarihi ne, Iran bata tsoron I$ra'ila, in kuma watarana ta kuskure ta kaima Iran hari, sai sunyi nadamar meyasa s**a kai wannan harin.
Cikakken bidiyon yana shafina na Telegram, zaku iya kallo ta hanyar shiga ciki ta wannan links ɗin
https://t.me/taskarMuhdBalaAfuwa
Fassara; Muhd Bala Afuwa
Ƙungiyar Biafra a shirye take ta Taimakawa Isra'ila da Sojoji 15000 da s**a samu horon da ƙwarewa wajan yaƙi.
-Inji IPOB
BIDIYO | MUZAHARAR FREE PALESTINE NA GARIN KADUNA A YAU ALHAMIS 16/11/2023
Muzaharar nuna goyon bayan ga Falasdinawa kenan da akayi yau a Garin Kaduna kafin Jami'an Tsaron Najeriya suzo su bude wuta
- DMA-PRESS
https://www.facebook.com/100092405530071/posts/246609158429267/?app=fbl
04/11/2023
🛑 DA ƊUMI-ƊUMI |
Hizbollah ta sanar da kai hari a wani sansanin sojan isra'ila, dake kan iyaka da kudancin Lebanon.
17/10/2023
SUN YI IYAKAN KOKARINSU SU BAKANTA SIFFARMU A IDON DUNIYA, AMMA SUN MAKARA.
_DR. Sheikh Ibraheem Zakzaky (H)
"..Sun yi iyakan kokarinsu su bakanta Siffarmu a idon duniya Amma sun makara, saboda muna tare da mutane ne. Mun fi su kusa da mutane. Su mahukunta da yawa nesa suke da mutane, mu kuwa kusa muke da su. Kuma kar a manta, abin da yake zukatan su (Suke Hankoro) shi muke fada, ba wani bako muka zo musu da shi ba.
An yi iyakan kokari a shafa mana mummunan fenti amma ya faskara. To amma dai basu fidda rai ba. Shiyasa kuma wannan karon s**a yi hankoron wanda za su yi na karshe. wato za a yi ta manya manya ta kare, a yi a gama. kamar yadda s**a kira shi "Once and for All". A yi ta manya manya ta qare, daga yanzu baza a sake kiran komawa addini ba, aji tsit. Sai dai kuma ma in za a yi addini sai irin yadda suke buqata. irin kungiyoyin da s**a kirkiro, suke kafirta musulmi, suke sabbaba fada tsakanin musulmi da musulmi, kuma suke ingiza musulmi su yi fada da kirista. kabila suyi fada da kabila, da bangare suyi fada da bangare. Duk su suke ingiza Wannan.
SHEIKH ZAKZAKY (H) YAYIN ZIYARAR 'YAN UWA NA KANO. 20/11/2021
17/10/2023
YAU ZA A YI JANA'IZAR SHAHIDAN ABUJA STRUGGLE!
Tun kimanin shekaru 4 ke nan da gwamnatin Allah tsine ta Janar Buhari ta yi wa Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky(h), kisan kan mai uwa da wabi a Federal secretariat a birnin Abuja, sai jiya Litinin Allah ya kwato wasu daga jikkunan Shahidai daga mahukunta
An sami karbo jikkunan Shahidan ne bayan wasu kotuna sun zartar da hukuncin a baiwa ahalin Shahidan jikkunan su, tare da biyan wasu miliyoyin kudi akan diyya, amma gwamnatin tsohon shugaban kasar Buhari ta ki mutunta hukuncin kotunan
Insha Allah za a yi jana'izar Shahidan su 5 a yau Talata a Darurrahama a garin Zaria
Da misalim 10:00am
Ana gayyatar daukacin yan'uwa gun jana'izar.
16/10/2023
-DANGANE DA YIN SUJUDA AKAN TURBA (ƘASA).
-Manzon Allah (S) Yana Cewa: ''An Sanya Min Ƙasa ta Zamanto Abin Samun Kwanciyar Hankali da Kuma Yin Sujada Akanta, Duk Inda Sallah ta Samu Mutum, Yayi Sallah A Wajen.
(Sahih Al-Nisa'i, 2/37)
-Manzon Allah (S) Ya Faɗawa Abu-Zar (RTA) Cewa: "Ƙasa Abin Sujuda Ce Gareka, Don Haka A Duk Inda Sallah ta Same Ka Kayi ta''
(Mustadraq Al-Hakim 3/473).
-Ibn Abbas Ya Ruwaito Cewa, Manzon Allah (S) Ya Kasance Yana Sujuda Akan Dutse.
(Sahih Bukhari 2/163).
-An Ruwaito Daga Anas Bn Malik Yana Cewa: ''Wata Rana Muna Sallah da Manzon Allah (S), A Lokacin Ana Tsananin Zafi, Sai Wani Daga Cikinmu Ya Ɗauki Ƴar Tsakuwa Ya Riƙe ta, Don idan Tayi Sanyi Yayi Sujuda A kanta''.
(Sunan-Abu-Dawud 1/143).
-Jabir Bn Abdullah (RTA) Yana Cewa: "Wata Rana Mun Kasance Muna Sallar Azahar da Manzon Allah (S), Sai Na Ɗauki Wasu Ƴan Tsakuwa Na Riƙe ta A Hannuna, Don Idan Tayi Sanyi Nayi Sujuda Akanta, Saboda Tsananin Zafi''
(Sunan-Alkubrah 2/104).
-Abu Sa'idul Ƙudri Yana Cewa: ''Idona Ya ga Manzon Allah (S) da Alamar Ruwa da Laka Akan Hancinsa da Goshinsa''
(Musnad Amad, 1/327).
-Ina Kuke Masu Yi Mana Surutu Akan Muna Yin Sujuda Akan Turba?, To Sai Ku Koma Makaranta, Zagin Ƴan Shi'a Ba Naku Bane.
-Ku je Kuyi Karatu Banda Sharholiya da Shaci-faɗi.
-Muhammad Jiddah Nguru
07037009525
"Ku yi yaƙi da Isra'ila da hakoranku da ƙusar ku, ku yi yaƙi da ita komai ƙanƙantar makamin ku."
-- Imam Sayed Musa al-Sadr
ƙirjin mai hankali akwatin sirrinsa,shi ko sakin fuska tarkon soyayya ne.
Zancen Hikima ne 👌
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Telephone
Website
Address
Kawo
Kaduna
234