Komai da lokaci mutuwa da rayiwa

Komai da lokaci mutuwa da rayiwa

Share

Dan kasuwa

05/05/2026
27/12/2025

KAI MATASA KU MOTSA!
Ko Rana da tsaye take cak waje ɗaya da ta cutar da duk abinda take Haskawa, haka da farin wata bai fitowa ya koma da bazai zama sha kallo ba.
Shi Ruwa idan yana tsaye baya gudana sai kaga ya gurɓace, amma wanda ke gudana sai ai shekaru amfaninsa bai ƙarewa ba.
Daƙin dake kulle iskar cikinsa bata daɗi, amma wanda iska ke kai-komo nan yake zama Dausayin hutawa.

Magana nake akanka mai karatu, kana neman ɗaukaka amma kana zaune waje guda? Ɗa nah ka motsa
تَغَرَّبْ عَن الأَوْطَانِ في طَلَبِ الْعُلَى
وَسَافِرْ فَفِي الأَسْفَارِ خَمْسُ فَوَائِدِ

تَفَرُّجُ هَمٍّ، وَاكْتِسابُ مَعِيشَةٍ
وَعِلْمٌ، وَآدَابٌ، وَصُحْبَةُ مَاجِد
Imam Shafi'i ne nan ke baka shawara..
Yace Ka motsa! idan kana son ɗaukaka, matakin farko kabar garin da kake kayi balaguro, Ɗa nah acikin Tafiye tafiye akwai wasu fa'idoji 5 da ake Samu,
Zaka samu yayewar damuwa, da Abin da zai rike rayuwarka, zaka ƙara ilimi da koyon ladubban Rayuwa da mu'amala, Sannnan zakai abota da mutunan kirki masu daraja watarana.

Dan haka ka motsa!

16/11/2025

Bro to Bro:

Ɗan’uwa Ka yi duk abin da ya kamata, ka yi amfani da dukan ikonka, don ka kuɓuta daga talauci amma ta hanyar Halal.

Allah yayi mana tsari da Talauci.

15/11/2025

DARI BISA DARI (100%):
MATSALOLINKA 90% ZASU KARE IDAN KA YI WADANNAN ABUN 7

Namijin da ya mallaki:

1. Sha'awar Jikinsa: wato Kare farj*nsa daga z!na da alf@sha.

2. Kwadayin Cikinsa: wato Cin abinci don rayuwa, ba rayuwa don cin abinci ba.

3.Kama kansa lokacin fushi da bacin rai.

4. Harshensa: wato Sanin lokacin magana da lokacin yin shiru.

5. Idanuwansa: Wato Kare kallo daga abubuwan da ba su dace ba.

6. Barcinsa: Rage kasala da tashi da wuri don neman na kai.

7. Son Zuciyarsa: wato Yin abin da ya dace, ba wai abin da ransa yake so ba.

Ya warware kashi 90% na matsalolinsa.

Ka mallaki kanka.

KAKARE MUTUNCINKA.

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Address


Kano
700101