Salafiyya Methodology

Salafiyya Methodology

Share

IYAKA NA ABUDU WA IYAKA NASTA'IN�

17/09/2026

MU NAN DUK LAWAN TRIUMPH NE

13/09/2026

INFAKUL MAISURI(Part 4)

BABI NA 4: HASADAR SARAKUNA ZUWA GA SHEHU

Muhammad Bello yace: Shehu bai daina aikin da yake yiba. Yanaci gaba da tabbatar da farillolin aini ga jahilai, yana kuma watsa ilmi ga malamai.

Shehu yana fita kowane daren Juma'a yana yiwa mutane wa'azi. Mutane suna taruwa da yawa har ba a iya kidayasu. Haka kuma yana fita wasu darare bayan Isha'i domin yada ilmi, sannan bayan Sallar La'asar yana koyarwa.

Yana koyar da:

Tafsirin Alqur'ani,
Hadisi,
Fikihu,
Sufanci (gudun duniya).

Haka kuma yana da wasu littattafan daya rubuta da kansa, wadanda yake karantawa a wasu lokuta. Yana fita zuwa wasu garuruwa domin wa'azi, sannan ya koma Degel.

Yadda jama'a s**a fara taruwa

Marubucin yace mutane da yawa daga gabas da yamma suna zuwa wurin Shehu, kuma mafi yawan malaman zamaninsa suna neman albarkarsa.

A cewarsa, addini ya fara bayyana sosai a wadannan kasashe, mutane suna aiki da gaskiya. Wannanne yasa wasu daga cikin sarakuna masu son duniya s**a fara kiyayya da Shehu, alhali kuwa tun farko suna girmama shi kuma suna neman albarkarsa da addu'arsa.

Bello yace: Shehu bai hana sarakunan abin da suke soba, kuma baiyi musu katsalandan ba. Amma abin daya fusatasu shine ganin addini yana bayyana da kuma gaskiya tana samun karfi, alhali tsarin sarautarsu, a cewar marubucin, ya ginu ne bisa wasu ka'idojin da s**a saba wa Shari'a.

ABIN DAYA KARA TSANANTA AL'AMARIN:

Bello yace: wasu malaman banza da sarakuna s**a fara cutar da jama'a, suna karbar dukiyoyinsu, suna amfani da wasu mutane wajen cutar da jama'ar Shehu, har suna tare hanyoyin da jama'ar Shehu suke bi.

Musamman kuma, Bello ya danganta wannan makirci da sarakunan Gobir.

Yace sun fara shirya yadda zasu hana masu kira zuwa ga addinin Allaah yin wa'azi, kuma su tilasta mutane su koma ga abin da s**a gada daga iyaye da kakanninsu (maguzanci).

Gargadin Sarkin Gobir Nafata:

A nan Bello yakawo wani muhimmin bayani kai tsaye.

Yace Sarkin Gobir Nafata yayi gargadi a kan abubuwa uku:

1. Bai yarda kowa ya yi wa mutane wa'azi ba, sai Shehu shi kadai.

2. Bai yarda mutum ya shiga Musulunci ba sai idan ya gada Musuluncin daga iyaye da kakanni. Wanda bai gada ba, saiya koma ga addinin daya tarar iyayensa da kakanninsa suna yi.

3. Ya hana maza sake nada rawani, sannan ya hana mata sake lullubi zane su yafashi a bisa kirji (hijabi).

Bello yace an yada wannan gargadi a kasuwanni.
Bayan Nafataya rasu: sai Yunfa yahau gadon sarauta,

Bello yace lokacin da Yunfa dan Nafata ya hau gadon sarauta, yaci gaba da wannan hanya.

Sai lamarin yakai ga kai hari wata babbar alkarya ta Musulmi a lokacin da mutanen garin basuyi tsammanin yaki ba. An kashe Musulmi da yawa, musamman malamai da masu haddar Alqur'ani, kuma abin yafaru da rana a watan Ramadan, mutane suna azumi.

Zamuci gaba insha Allaah!

KUCI GABA DA BIBIYARMU KUYI FALLOW, LIKE, SHARE, NAGODE.

11/09/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN

Yanzunnan muke samun LABARIN Wani Dan iska ya lallabo da adda yasari sheikh malam musa lukuwa sokoto Amma alhamdulillah da sauki malam Yana asibiti, shikuma Dan ta'addar ANSAMU nasarar kasheshi

Allaah yqbawa malam lafiya

04/09/2026

Seda aka shekara 500 ana musulunci ba'asanma menene maulidi ba

02/09/2026

Ko a cikin littafinku na jawahirul ma'ani babu maganan maulidi ballantana littattafan Musulunci!
MAULIDI ISKANCINE

01/09/2026

BABU WANI DAN SHEIKH JAFAR DA YAZAMA KAFIRI!
Wannan Sharrin Yan Bidi'ah ne

31/08/2026

BAREWA BAZATA TABAYIN GUDUBA DANTA YAYI RARRAFE

Bazaka tabajin Nuru Khalid yafito Yana goyan bayan MURADUN musulunciba saina kiristoci duk Mai bibiyarsa yasan haka
Duk inda laifin musulmi yake shiyake zakulowa yayi S**A Akai Amma baya s**ar kiristoci

Saima yabonsu da kare muradunsu da yake

Nuru Khalid shiya Maida dansa Kirista da kansa ta hanyar irin kazamar da'awarsa ta inter Faith

Nuru Khalid Muna addu'ar Allaah yashiryaka katuba kafin mutuwa ta riskeka akan mummunan akidarka ta inter Faith

27/08/2026

SAMI'INA WA'ADA ANA (MUNJI KUMA MUNBI)

Maganar nan taka tanuna jahilcinka da rashin hankalinsa Kai baban gawuna.

Hadisin matar data shayar da kare ruwa ta shiga Aljanna, baya nufin duk wanda ya shayar da wani zai shiga Aljanna ba. Aikin alheri baya soke hukuncin Aqida da Tauhidi.

Amma batun iyayen Manzon Allaah saw. akwai Sahihan hadisi daga bakin manzon Allaah saw.Muslim, inda aka tambayi Annabi saw. game da mahaifinsa, sai yace: “Mahaifinka yana cikin wuta.” (Sahih Muslim, 203)

Sannan Annabi saw. yace: “Na nemi wa mahaifiyata gafara, amma ba a bani izini ba.” (Sahih Muslim, 976)

Saboda haka, ka daina auna hukuncin Allaah da tunaninka. Shayar da kare ruwa falala ce; amma ba ita ce ma'aunin tsira ba.

Kafin ka kira wani “mahaukaci”, ka fara zuwa makarantar ilimi, domin jahilci ba hujja bane, hayaniya kuma bata zama dalili ba.

INKA KARYATA MAGANAR MANZON ALLAAH SAW. KAZAMA KAFIRI

Photos from Salafiyya Methodology's post 25/08/2026

INFAQUL MAISURI (Part 3)

BABI NA 3: HALAYEN SHEHU MADAUKAKA

Shehu yatashi yanada kamun kai da kyawawan halaye, kuma Bello ya bayyana cewa baisan wani mutum a zamaninsa da yake da halaye irin nasa ba.

Yace mutane suna zuwa wurinsa daga gabas da yamma, kuma ya kasance malamin malamai, mai daga tutar addini.

Shehu:ya raya Sunna;
ya kashe bidi'a;
ya yada ilmi;
ya warware rikice-rikicen addini;
ya yada ilmin Tauhidi da Shari'a;
yayi tafsirin Alkur'ani shekaru masu yawa;

Yasan ilmin kira'a da fannoni daban-daban na Alkur'ani;
yayi zurfi a ilmin Hadisi da Usuludini;
yayi aiki da hukuncin Alkur'ani da Hadisi.

Bello ya takaita sifar Shehu da kalmomi masu karfi:

Shehu ma'abucin haske guda biyu ne: ilmi da aiki.

Hoton farko da littafin ya kawo. Littafin ya sanya shi a matsayin “Gidan Shehu a Degel Hoto na 1”, kuma hoton yana nuna wuraren da aka danganta da Shehu, kaburbura, gidan Shehu da makarantar Shehu.

Hoton dake sama na bincike ne domin karin gani; hoton da yake cikin littafin da muka dogara dashi shine hoton da aka nuna a shafin littafin,

Shehu a wajen mutane:

Bello yakuma bada wani labari da yace shi kansa ya saba gani.

Yace idan Shehu zai fita yaje wajen mutane, wani lokaci yakan tsaya a kusurwar gida na dan lokaci kafin ya fita. Da ya tambaye shi dalilin haka, Shehu yace yana sabunta niyyarsa, yana yiwa Allaah alkawarin tsarkake niyyarsa, sannan yana rokon Allaah Ya sanar da wadanda zasu halarta abin da zai fada musu.

Idan ya isa wurin mutane, yana gaishe su cikin sakin fuska da kyakkyawan hali, sannan yace:

“A saurara.”
Bello yaci gaba da bayyana cewa Shehu baya gajiya da bayani, kuma baya yin fushi saboda rashin fahimtar mai sauraro. Yana magana da karfi domin kowa yaji, kuma baya jin nauyin fadin gaskiya koda akwai manya ko malamai masu hassada a wurin.

KUCI GABA DA BIBIYARMU KUYI FALLOW, LIKE, SHARE, NAGODE

Photos from Salafiyya Methodology's post 23/08/2026

INFAQUL MAISURI (Part 2)

BABI NA 2: TARJAMAR MAHAIFIN MAI LITTAFIN:

marubucin ya fara shiga cikin tarihin mahaifinsa, Shehu Usman bin Fodie.

Ya fara da cewa akwai wani babban malami daga cikin malaman kasar, malami mai girman daraja da tsoron Allaah, wanda ya kasance uban Muhammadu, wato:

Usumanu dan Muhammad dan Usumanu, wanda aka fi sani da “dan Fodie”.
Kuma ya kirashi da cewa: “mahaifinsa.”
Labaran da aka riga aka bayar game da zuwan Shehu

A cewar marubucin, wasu daga cikin waliyyan Allaah sun riga sun bayar da labarin bayyanar wannan malami tun kafin lokacin dazai bayyana.

Ya ambaci Mallam Walididi da Mallam Dahiru cikin wadanda akace sunyi wannan ishara. Haka kuma ya kawo wata ruwaya daga Umma Hani'i, wadda ya siffanta da saliha kuma waliyiya daga zuriyar Fulani.

A cikin wannan ruwaya, an bayyana cewa wani waliyyin Allaah zai bayyana a yankin Sudan, yayi aikin sabunta addini, raya Sunna da tsayar da addini, kuma mutane zasu bishi. An kuma ce sunansa zai shahara a kasashen yankin, har sarakuna da talakawa suyi koyi da al'amuransa.

Bello yace Shehu ya fara kiran mutane zuwa ga addinin Allaah tun yana karami, yana shiryar da mutane zuwa ga addini.

Ya fuskanci abubuwa da dama daga mutane, ciki harda jayayya, kin yarda da shi da izgili, amma yaci gaba dayi musu bayanin al'amuran addini gwargwadon fahimtarsu, tare da tausasa musu.

Daga baya, Allaah Ya shiryar da wadanda akayi wa rabon shiriya, s**a nufi wurinsa, kuma jama'ar muminai s**a saurari wa'azinsa.
Bello yace Shehu ya kasance yana bayyana wa mutane gaskiya da hanya madaidaiciya.

Halin addini a kasar Hausa:

Bello yakawo wani muhimmin bayani.

Yace Shehu ya sami al'umma da mummunan yanayi na addini, inda yace akwai kafirci, fasikanci da sabo da s**a mamaye kasar. Ya bayyana cewa mutane kadanne suke da ingantaccen imani da ibada yadda ya kamata.

Akwai wasu da s**a san tauhidi kuma suke yin sallah, azumi da zakka, amma basa cika sharuddan ibadunsu, kuma suna hada wasu ayyukan ibada da al'adun kafirci da s**a gada daga iyaye da kakanninsu.
A irin wannan rukuni akwai wasu daga cikin sarakuna, mayaka, bokaye da malamai.

Amma akwai wasu muminai kadan wadanda s**a san tauhidi kuma suke kyautata ibadunsu.

Abin da Shehu ya mayar da hankali a kai:
Aokacin da Shehu ya fara wannan kira,
yana kiran mutane zuwa ga addinin Allaah;
yana yi musu nasiha;
yana rushe munanan al'adu;
yana yaki da bidi'ah;
yana raya Sunnar Annabi ﷺ;
yana sanar da mutane farillolin addini;
yana shiryar dasu zuwa ga da'a ga Allaah;
yana kawar da jahilci daga cikinsu.

Saboda wannan kira, mutane s**a rika shiga cikin addinin Allaah jama'a-jama'a, kuma Shehu yaci gaba da bayyana musu gaskiya da hanya madaidaiciya.

Shehu ya fuskanci jafa'i da wahala daga wasu malaman zamaninsa, amma Allaah Ya taimake shi, Ya kuma bashi wasu malamai nagari wadanda s**a gaskata shi s**a taimake shi.

WAKAR WAZIRI ABDULLAHIN GWANDU:

Bayan wannan bayani, Bello yakawo Wakar Waziri Abdullahin gwandu (balaraben kasashen yamma),game da kiran da Shehu yake yi wa mutane zuwa ga addini.

Fassarar ma'anar baitocin da littafin ya bayar : Shehu yayi kira zuwa ga addinin Allaah, baya tsoron masu zarginsa ko masu tsegumi saboda wannan aikin. Mutane da yawa s**a saurare shi, kuma darajarsa ta karu.

KUCI GABA DA BIBIYARMU KUYI FALLOW, LIKE, SHARE, NAGODE

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Kano?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Website

Address


Dambatta
Kano
702104