Umaimah Ado Gaya's Palace
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Umaimah Ado Gaya's Palace, Health/Beauty, Sharada Kwanar Ganduje, .
13/04/2026
Jama'a kuna Nan ana cin uwar sabada a Auren sati daya. Aure ya Kare Amma Asaad ya fara zagaye wa yana yaudarar Rahina yana sharbar Roman damakwaradiyyar qauna shi da Zahra. Maza idan ba ku biya kudi ba ku biya a yi da ku, ko kuma ku yi following din wannan link ku karanta a Arewapen
https://www.arewapen.com/chapter?id=69d37fa2ca365deaf1c630c2
13/04/2026
Wato Jama'a ina mai tabbatar muku ba za ku yi nadamar karanta labarin Ummata ba, domin dai kunsan alƙalamin Fatima Umar Kas Hilfat.
10/04/2026
Hmm jama'a ina ta son ba ku labari sai na sha'afa. Gaskiya idan mutum bai yi abu dan Allah ba yana ruwa. Nice aka zo aka sanar da ni ƙawata ta gaban layinmu ta haihu. Jama'a cikin azumi ba na fita sai da dalili ko cefane ban je ba har aka sallace na manta. To ina ba ku labari, sai ranar muka haɗu a hanya muka gaisa na ganta da goyo, na ɗage gira tare da riƙe haɓa nace "au wai haihuwa kika yi?" Irin fa ban sani ba jama'a. Tayi murmushi tace "Wlh na haihu baki sani ba? Kin san da yake ba kai zaka fita ka sanar ba, ba ka san suwa s**a ji ba." Nace "!haka ne insha Allah zan zo" Ai in faɗa muku ƴar halak ban je ba na sake mantawa. Ranar ina fitowa naji ƙamshin suyar ƙashi, nace wa maƙociyata "wai ni nake jin ƙamhin suyar nama?" Ɗayar tace "wlh nima naji." Sai na sake cewa "kuma wlh na suna ma nake ji kamar ma irin ana kan suyar ƙashi ma." ai kuwa sai maƙociyata tace mini gidan ƙawar nan tawa aka yi wa hakika da yake ba a nan ƴan'uwanta suke ba ba'a yi mata ba sai yanzu da s**a zo. Jama'a kar ku ce mini kwaɗayayyiya,kun san dai yadda naman suna yake da farin jini. washegari na shirya naje barka yaro har yayi wayo. Da na kammala barka na riƙa cewa "to zan tafi" Yo ƙawata da ƴan'uwanta ba su fahimta ba har na fito. Nayi biyu babu, ni ba da nama ba ba kuma da lada ba. Allah ya sa mu riƙa abu dominSa. Jama'a mini ciniki na fara sayar da Data.
05/03/2026
Wai da gaske sai ka bayyana sirrinka a social media kuma wasu ba su gane ka ba? Aradu wasu bibiyar mutane suke haka kurum ma b***e kuma ka faɗi sirrinka.
Kun san fa'idar haɗin gwiwa ga al'umma irinmu kuwa? Kun san mai ake nufi da sadaukar wa kuwa?
02/03/2026
Shin idan aka tambaye ki/ka mene ne babbar matsala ko kuma musabbabin halin da muke ciki a yanzu mai za ka/ki ce? Ni dai a nawa mahangar ba mu da ƙarfin zuciya sannan ba ma iya tsaya wa kanmu. Sannan ba mu mayar da junanmu ƴan'uwa ba.
Jama'a ku zo mu sha labari. Jiya ƙawata ta tashi da son cin kifi. Da rana mai kifi yazo wucewa ta tare shi tace ya saka mata kifi guda biyu. Bayan ya saka ta tambaye shi nawa kifi? Mai kifi yace duk ɗaya 2k. Ƙawata tace "dubu biyu? Gaskiya Allah ya bada sa'a." Shi kuma mai kifi ya dage akan sai ta taya. Hajiyanka tace idan ya siyar 1k duka biyun. Mai kifinka yace taje ta ɗauko wuƙa da robar da zata saka saboda wuƙarsa ta faɗi a hanya. Hajiya saboda jin garaɓasa ta shige gida har dan gudunta ta ɗauko. Tana gaf da ƙofar gidanta ta biyu da yakeƙofofi biyu gare ta mai kifinka ya saɓi kifinsa yayi gaba yana faɗin "kifi na miya!" Da ta fita sai ya juyo yana faɗin "Au kin ɗauko? To ki cigaba da jiran asararran da zai siyar miki da wannan kifin a 1k. 😂 Allah ya yafe wa mata son banza. Ku biyo ni don jn yadda nima muka kaya da mai kifi😄.
10/04/2026